Sashe 31
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Manu ya kalli Farouq yatashi ya futo daga gidan yana goge hawayen idonsa, yarasa Ina Farouq yanufa,da alama yana goyon bayan yayarsa,shida ya nemi taimakon sa maimakon yabata haquri wato shine yake cewa yatashi yaje idan tahuce saiya dawo suci gaba,bashida niyar bata haquri kenan saide yadawo suci gaba daga inda suka tsaya.
Tunda Manu yafice yabar gidan, Bilkisu bata sake futowa tsakar gida ba, tana daki tana uzurin ta,saide in an kira sallah zata futo tayi alwala saita juya takoma daki, Farouq yanaso yayi mata magana amma kuma yana shakkarta,saboda yasan halin yayar tasa zata jima tana haquri dakai amma inde kakai haqurin ta qarshe to tana daukan zafi sosai, hakan yasa baice da'ita uffan ba,har saida aka kira sallar magrib yaje yayi sallah yadawo, anan yaganta ta shimfida babbar tabarma tana zaune a tsakar gida da 'yar qaramar wayarta a hannunta tana danna wa,zama yayi shima a gefenta sannan yace"yaya yanzu mekike ganin za'a yi?"
Bilkisu ta kalleshi tace" game dame kenan?"
Farouq ya daure duk da yana shakkarta ya cije,ya dake kamar baya tsoron yimata magana sannan yace"dangane da Manu,agidan Alhaji Auwal nahadu dashi,ban bashi fuskar dazai min doguwar magana ba,ashe ya biyo bayana bansaniba,tun acan gidan Alhaji Auwal din naga nadama acikin idanuwan Manu,ni aganina Yaya da kinyi haquri kin saurare shi tunda bakisan dame yazo ba,bakisan dalilin da yasa ya gudu yabar kiba,Yaya ubangijin daya haliccemu mafa muna aikata masa laifi wani da saninmu, wani babu saninmu, amma kuma idan muka roqeshi gafara yana gafarta mana,kiyi haquri Yaya kibashi dama kamar yanda yafada din domin ya wanke laifin sa a wajanki, tsawon shekarun nan dakika rabu dashi har yanzu babu wani namiji dakika bawa dama ya aure ki,aganina ki koma gidan uban danki,kuci gaba da Addu'ah har Allah yasa idan da rabo kuga d'anku".
Bilkisu ta kalleshi tace"kagama?"
Duk da yana shakkarta haka yadago ya nuna mata shi cikakken namiji ne ya kalleta babu alamun tsoro yace"nagama saura naki"
Bilkisu tace"to tunda sauran nawane,saika barni inyi abinda nayi niyya, Farouq da alama bakada hankali,mutumin daya gudu yabarni da tsohon ciki,na mutu kona rayu duk daya awajansa,shine kake cewa in koma gidansa? dana dauki shekaru naqi yin auren cemaka akayi Manu nake jira? ta dalilin safa nataho nan, har na rasa Muhammad dina,yanzu shi Manu in banda tsaurin ido irinna maza har yanada qwarin gwiwar dazai iya kallon idona yace in koma gidansa? yanda yasa nayi asarar d'ana shima yayi asara ta wallahi"
Ta qarasa maganar tana karkad'a qafa.
Adede lokacin Inaas tayi sallama tashigo gidan, manager ilyasu yana bayanta.
Cikin murna ta qarasa ta rungume Ammiy,Bilkisu tabita da kallo ganin kayan data fita dashi ranar dazasu tafi, ba shine ajikinta ba,Inaas ta kalleta dakyau tace"Ammiy meya sameki naga kamar kina cikin damuwa?"
Bilkisu tayi shiru kamar bataji tambayar da Inaas din take mata ba, tajuya suna gaisawa da Ilyasu manager, Abba ma yabashi hannu suka sake gaisawa, yayinda Ammiy tatashi takawo masa ruwa.
Ilyasu yasha ruwan sannan ya kallesu yace" to Malam Farouq kamar yanda nayi alqawari gashi nacika,nadawo da Inaas gida lafiya,kuma Yalla6ai Jawad yace yana sake yimuku godia Allah yabar zumunci"
Farouq yayi murmushi yace"qwarai kacika alqawari,sannunku da zuwa,Yaya hanya to?"
Ilyasu yace"Alhamdulillah hanya lafiya,mungode sosai, bari in wuce"
Ammiy tace"har tafiya zakayi?"
Ilyasu yace"eh wallahi naga dare yayi"
Inaas tatashi ta rakashi qofar gida sannan tadawo gidan ta zauna ta kalli Ammiy tace"Ammiy meyake damunki?,waye yata6a min ke?"
Kai tsaye Bilkisu tace"Sulaimanu ne yazo"
Cikin rashin sani Inaas tace"waye Sulaimanu?"
Bilkisu tace"tsohon mijina,Baban Muhammad"
Cikin sauri Inaas tace"kaiiii Alhamdulillah,wallahi naji dadi Ammiy inama ace ina nan yazo dana ganshi, dama ban ta6a ganinsa ba"
Bilkisu ta kalleta da tsananin taqaici sannan tace"toke da miye hadinki dashi dakike wani washe baki kina cewa baki ta6a ganinsa ba? d'ansa na cikinsa ma bai taba ganinsa ba tunda guduwa yayi yabarshi tun kafin yazo duniya"(🤭😂)
Inaas tanajin wannan amsa da Ammiy tabata saita nutsu tayi shiru,da alama akusa take,saida ta dauki minti biyu sannan ta sassauta murya alamar lallashi tace"Ammiy,koba komai shifa Baban danki ne,kin riga kin hada alaqa dashi tunda duk runtsi idan an ganshi za'a ce shine Baban danki,Ammiy bansan ki da fishi ba,kiyi haquri ki yafe masa Allah yanason ba yinsa masu haquri Ammiy"
Hawaye yacika idon Bilkisu,tanaso ta tsaida su amma saida sukai nasarar zubowa ta kalli Inaas tace"Inaas ta dalilin sa fa narasa Muhammad dina,kema kin goyi bayan mutumin daya gujeni saboda talauci?"
Inaas ta matsa ta rungume ta sannan tace" Ammiy idan da ya gujeki saboda talauci ai har yanzu mu d'in talakawa ne,yanzu ma ai gashinan yadawo gareki duka de acikin talaucin"
Bilkisu batace komai ba ta dauki ruwan da manager yasha yarage, ta matsa gefe ta wanke idonta, sannan tayi ajiyar zuciya ta kalli Inaas tace"ya hanya? Ina Jawad yake? yana lafiya?"
Cikin sauri Inaas tace" yana nan kalau Ammiy,shima muna haduwa yace ina kike? kuma wai ince miki yayi KEWAR KI"
Bilkisu tayi murmushi tace"Allah sarki Jawad yaron kirki,Allah de yayi masa albarka,Allah yakare shi aduk inda yake"
Farouq ya kalleta da tsananin mamakin yanda take zubawa Jawad Addu'ah saikace wani d'anta.
Inaas tayi murmushi tace"Amin"
Sannan ta dauko ledar gefenta tace"wannan ma shine yabani,harda sarqar wuyana"
Bilkisu da Farouq suka bude leda,tsaleliyar wayarta qirar iPhone tafuto fili,Farouq ya jujjuya wayar yagani sannan ya ajiye,yabude envelope din daya gani aciki,daloli suka bayyana sababbi fil amiqe"
Cikin sauri Bilkisu ta zaro idonta waje tace"duk wannan din na menene haka? wannan dalar amurka cefa,mezaki da wannan uban kaya? sarqar wuyan naki ma naga kamar sarqar gold ce"
Inaas tace"eh haka Hajiya Halima ma tace,waita gold ce, kuma tanada tsada"
Bilkisu ta jinjina kanta sannan tace"tab lalle Jawad yayi qoqari,wannan kashe kudin ai yayi yawa,kinga yanzu shikkenan kema kinyi waya saiki dauka kije daki idan ankawo wuta saiki saka caji"
Farouq yayi sauri yaja wayar gabansa yace"ta dauki me?, wai Yaya kina tunanin a banza zai kashe mata wannan uwar dukiyar ne? dole akwai abinda yake nema a wajanta,saboda haka ba zatayi amfani da wannan wayar ba,kudin ma a ajiye shi duk lokacin da Allah yasa suka sake had'u wa adauki kudinsa a bashi,ni tsoron masu kudin nan nake,bare kuma shi Jawad din kansa,yaron nan ranar da akai rasuwa agidan Alhaji Auwal ina ganin yanda manyan qasar nan suke zuwa har gabansa su rissina su gaidashi nasan cewa ba qaramin mutum bane,saboda haka gaskiya ina tsoron wannan al'amari Yaya"
Bilkisu ta kalleshi tace" Farouq bangane ba zatayi amfani da waya ba, Jawad nefa yabata"
Cikin sauri Farouq yace"shi Jawad din Muhammad dinki ne? ni Yaya kwata-kwata nakasa gane miki akan wannan yaron,daga ganin yaro sau d'aya shikkenan kin dauki yarda kin bashi,haka lokacin da yarinyar nan tazo da batun tafiyar nan tasu kika daure mata gindi wai ai Jawad ne babu komai kawai taje ta yaron yanada nutsuwa,Yaya kidawo hayyacinki Jawad fa ba Muhammad dinki bane bare kiyi masa shaidar kirki"
Bilkisu ta kalli Inaas tace" ai shikkenan, ke sai kiyi haquri da wayar,idan Jawad din yazo karma ki masa zancen waya,nida kaina zan fada masa cewa ubanki ya hanaki amfani da wayar saboda yana zarginsa"(😂🤭)
Inaas tatashi tawuce ciki ta dauki buta tashige bandaki, yayinda Farouq yadauke wayar da envelope din kudin yayi cikin dakinsa dasu yana mamakin yayar tasa akan wannan Jawad din,har yanzu de dayayi mata wannan dogon bayanin ita bataga laifin Jawad din ba.
Da daddare bayan ta watsa ruwa taci abinci ta kwanta tayi shiru tana tunanin sa aranta,sarqar daya daura mata takamo ta riqe da hannunta tana shafa sarqar tana tuna lokacin datake saka masa cake abaki,ta tuna d'an qaramin lips dinsa wanda yake kama da nata lips dinta,ta tuna kyakykywan sajen daya sake qawata fuskarsa,tayi murmushi tasake gyara kwanciyar ta,ahankali tayi magana can qasan maqoshinta tace"yalla6ai Jawad ya had'u sosai,maqurar had'uwa shidin had'ad'd'e ne".
(Inaas yadai🤔)
Mutara zuwa gobe🙏🏻
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.
300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.
Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME DEBE KEWA,300 ne kacal,ba dubu daya bane ba dari biyar bane 300 ne kacal idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe,ki biya ki karanta cikin salama👌🏻
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034.
Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034