← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 63

Sashe 38

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fu'ad yace"Ina da wani sabon sim card bari in kawo miki saiki yi amfani dashi"
Bai jira amsar taba yanufi dakinsa da sauri yadauko mata sim din yakawo mata,shine yasaka mata, sannan yayi kira yadauki number shima yayi saving a wayar sa,ya kalli dogayen gashin idon Inaas yace"yanzu shikkenan kema kinyi waya saiki dinga waya da samarin ki,ko babu?"

Yayi mata tambayar yanason jin ko akwai samarin,idan babu yasako kansa yafara kafa tasa gwamnatin.

Inaas tayi murmushi shima yana kallonta yasaki wani irin murmushi.

adede lokacin Jawad yasauko daga sama,kasancewar jiya baiyi bacci dawuri ba yana faman juye-juye da tsammanin kiran Inaas,hakan yasa bai tashi dawuri ba sai yanzu ya futo, yana sanye cikin wando three quarter, da riga marar hannu,da murmushin Inaas da Fu'ad yaci karo,hakan yasa nan da nan yaji wani irin zafi agefen zuciyar sa,ya d'aure fuska yaqaraso cikin falon,saide ganin Ammiy yasa nan da nan yaji 6acin ran nasa yana raguwa.
Ammiy ta daga kai ta kalli Jawad dayake saukowa,lokaci daya gabanta yayi wata irin fad'uwa,shima Jawad a nasa 6angaren hakan ce ta kasance,yarasa meyasa duk lokacin dayaga wannan matar yake tsintar kansa cikin fad'uwar gaba,haka yazuba mata ido yana kallonta har yaqara so cikin falon.
Mummy tayi murmushi ta kalleshi tace"Jawad katashi?"

Saida ya tsugunna sannan yadan kalli Bilkisu kad'an yace"MAMA barka da safiya"

Cikin jin dadi Bilkisu tace"sannu Jawad"

Jawad ya amsa mata yana qoqarin komawa wajan Mummy,Bilkisu tasake kallonsa, taga yanda dantsan hannunsa yake a mummurd'e tace"Baba nah wannan hannu a dinga rufeshi mana"

Jawad yayi d'an qaramin murmushi baice komai ba.

Inaas tasaci kallon dantsan hannun Jawaad taga yanda yawani murde,ta d'an jinjina kanta ta tuna ranar da suka fara haduwa take cewa yazo ya daketa mana meyake jira?

Tayi sauri ta kawar da wannan tunanin sannan ta dan kalli idonsa tace"ina kwana?"

Jawad yayi kamar bai gantaba,yadauke kansa sannan ya amsa mata da qyar yace"lafiya"

Yatashi yakoma can gefen Mummy ya zauna,Fu'ad ma yatashi yakoma wajansa.

Ko minti biyar Jawad baiyi da zama ba,aka kira wayarsa,fuska babu walwala yadauka yafara magana akan zakkar dazasu fitar,yadan jima yana magana fuskarsa babu walwala, ransa baqiqqirin musanman idan yatuna irin murmushin datake wa Fu'ad sai yaji ransa yana zafi,saida yagama wayar sannan yakashe.
Me aiki takawo masa abinci ta ajiye sannan tajuya tabar wajan cikin sauri, wayarsa yaci gaba da dannawa kamar baiga abincin da'aka kawo masa ba,d'ayar wayarsa dake ajiye agefe ta dauki qara, yadauka tareda dora qafar sa daya kan daya yafara magana"idan kunje kusamu Hakimin garin kuyi magana dashi,iya yara marayu kawai zaku dauka,wanda basu wuce shekara biyar ba,za'a dauki photonsu ahada da bayanan su, sannan kowanne mutum daya a cikinsu insha Allah zamu bashi kudi amatsayin zakkar da zamu fitar, abawa kowanne yaro dubu tamanin amatsayin kudin islamiya,amma ku sanar dasu cewa muna so nanda wata uku wadannan yaran su haddace uzu biyu na Alqur'ani,please kuyi yanda nafada muku ok?"

Yana gama wayar yakashe ta sannan ya kalli Fu'ad yace"kaje dakina zakaga wata jaka,ka kaiwa Alhaji Isah"

Fu'ad yatashi yace"ok yaya"

Sannan yanufi dakin Jawad,yana zuwa kuwa yaga jakar,saida yabude yaga kud'ad'e ne aciki sannan ya rufe ya futo,yana zuwa falo yayi sallama dasu Mummy yafita, Hajiya Zaliha taji dadin hakan,tana so koda yaushe taga Jawad din yana qoqarin saka Fu'ad wasu abubuwan dan shima Fu'ad din yazama Busy.

Jawad ya ajiye wayar hannunsa,yayi ajiyar zuciya sannan ya saci kallon Inaas,karaf akan idon Mummy,shikuma baisan Mummy tana ganinsa ba,haka ya dinga kallon Inaas din qasa-qasa, saide har yanzu fuskarsa babu walwala.

Mummy tayi murmushi ta kalli Inaas tace" Inaas matso ki zubawa Yayanki abinci"

Cikin daure fuska Jawad yace"no Mummy,ta barshi kawai"

Bilkisu ta kalli Inaas taga itama tahade rai da alama de su sukasan abinda ya hadasu,tayi murmushi ta kalli Jawad din sannan tace"Jawad bari nazo nabaka"

Jawad ya kalli Bilkisu,yaji kokad'an bazai iya yin musu da matar ba,har tazo ta zauna akusa dashi bai iya yunqurin hanata ba,itace da kanta tazuba abincin,sannan tasaka hannunta acikin abincin ta debo ta nufi bakinsa dashi,babu musu yabude bakin tasaka masa abincin yafara ci,nan take yaji wata irin nutsuwa, hakan yasa yasauke wata irin ajiyar zuciya kamar wanda yadauki tsawon lokaci yana kuka.

Idon Jawad akan Bilkisu sai kallonta yake, yanajin wani irin sonta acikin zuciyarsa,Bilkisu kuwa batasan kallonta yake ba,fuskarta kadaran kadahan take bashi abincin,shikuwa sai faman kallonta yake yana ji kamar su tabbata ahaka,kowanne lokaci Mummy da spoon take bashi abinci,amma yau gashi wannan matar da hannunta take bashi abinci,kuma yake jin abincin yamasa dadi fiye da qima.

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta baki biyani haqqina ba banyafe ba nabarki da Allah 👌🏻
300 ne kacal ki biya ta wannan account number

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

31&32

Yayi mamakin irin Abincin dayaci,Abinci yaci wanda rabon sa dayaci abinci mai yawan haka harya manta,har zuwa wannan lokacin idonsa yanakan Bilkisu,yanajin matar sosai aransa,tana birgeshi,shide baice mata ya qoshi ba,itace da kanta taga hakan zai iya wadatar dashi,danhaka ta dauki tissue din gefensu ta goge masa bakinsa,sannan ta dauke abincin ta wuce kitchen dashi,daga can ta wanke hannunta.

Mummy ta kalli Jawad tace"masha Allah Jawad kaine kaci abinci haka?"

Bilkisu data futo daga kitchen tace"bayason cin abinci ko?"

Mummy ta jingina kanta cikeda tabbatar wa tace"ina harkokin sa ma suka barshi yaci abincin?inkinga yatsaya ya nutsu yaci abinci sosai to na matsa masa ne"

Kafin Bilkisu tayi magana wayar Inaas ta dauki qara,tana dubawa taga Fu'ad ne yake kiranta,lokaci daya fuskarta ta washe,ta miqe tsaye ta dauki wayar tana shirin ficewa daga falon sannan tace"Hello Yaya Fu'ad"

Jawad ya runtse idonsa,ransa ya sosu da wannan kiran waya,nan take gefen zuciyarsa yafara yimasa wani irin zafi,lokaci daya ransa yayi baqiqqirin.
Cikin damuwa yatashi yabar falon yawuce sama,saide babu wanda ya lura da irin yanayin daya shiga.

Da daddare suna zaune afalo shida Mummy,kallo sukeyi amma hankalin ta yana kan Jawad,tun dazu dasafe da taga irin yanda yake satar kallon Inaas taji aranta ko son yarinyar yake? tun ganin farko datayi wa Inaas taji yarinyar ta birgeta,nutsuwarta tayi mata,taji tana yiwa Jawad sha'awar ta,to Jawad din nata ne ba'a gane kansa,wani lokacin ba'a yimasa gwaninta inde akan mata ne,amma yakamata tashiga cikin lamarin.

Jawad kuwa cikin yanayin damuwa yawuce dakin karatun sa,wani littafi ya dauka zai fara dubawa, yabude littafin kenan, sai tunanin ta ya fad'o masa,meyasa shi taqi kiransa? meyasa takira Fu'ad amma shi ko sau d'aya duk tsawon lokacin nan taqi nemansa? ya runtse idonsa yasaki wata irin ajiyar zuciya, sannan yayi qoqari ya kawarda tunanin ta aransa,ya ajiye littafin hannunsa yabude computer,yadauko wasu takardu suma yabude su zai fara dubawa,yatashi yabude wani fridge dake can gefe yadauko gorar ruwa guda daya,yadawo ya zauna zai fara aiki,lokaci daya wannan kyakykywan murmushin nata datake yiwa Fu'ad dazu yafado masa arai,cikin taqaici yakawarda computer gefe har hakan yasa takardun suka zube aqasa amma bai damu ba.

Wayarsa tafara qara,yaduba yaga Na'im ne,ahankali yadauka yayi shiru baice komai ba,daga can 6angaren Na'im yace"yanzu nake gani a labarai kashigo qasar"

A taqaice Jawad yace"yes"

Na'im yace" Alright,nima gobe zan shigo qasar insha Allah"

Yanzun ma Jawad a gajarce yabashi amsa yace"ok"

Na'im yayi mamaki,danhaka yace"what happen to you?"

Batare da 6oye-6oye ba,kai tsaye Jawad yace"wata yarinya ce"

Wata irin dariya takama Na'im,saida yagama shan dariyar sa sannan yace"Jawad fa d'an kasuwa ne,babu abinda yasani sai kasuwanci,ciki harda soyaiya"

Jawad ya runtse idonsa,batare dayace komai ba qit yakashe wayarsa yatashi ya futo daga dakin karatun yadawo falo.

Mummy tadaga kai ta kalleshi,daga gani yana cikin damuwa saide idan an tambayeshi ma zaice babu komai, kokuma yace yanayin aiki ne kawai, ahankali tatashi tawuce dakinta,ta dauko wani turaren qamshi mai bala'in dadi,takawo masa turaren alokacin harya sake shigewa cikin kujera ya kwanta kamar wani maraya, ta kalleshi tace"Jawad ka kaiwa Bilkisu wannan turaren kace tayi amfani dashi yanada dad'i"

Idonsa yafara d'agowa ya kalli turaren,kamar bashida niyyar kar6a,saikuma ya kar6a yatashi yafice daga falon baice mata uffan ba.
Chapter 38 · 0% Book details