← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 63

Sashe 20

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ya qarewa abincin kallo sannan ya za6i guda daya,mummy ta matso tafara bashi abincin da spoon,yanaci yanajin dadin girkin har wani lumshe ido yake, hakan da Hajiya Zaliha tagani shine yasake tabbatar mata yanajin dadin abincin,dan haka tasake tura masa abincin yaci yanda ransa yakeso.

P.a ne ya qaraso wajansu ya rissina cikin girmamawa yabawa Jawad wasu takardu yace"yalla6ai ana buqatar saka hannunka anan"

Babu musu Jawad ya kar6a yaduba sannan yasaka masa hannun, shikuma yafita.

Man Sulaiman ne yashigo falon,cikin girmamawa ya gaida Hajiya Zaliha,ta amsa masa.

Jawad ya kalleshi yace"Uncle Ina wuni"

Man Sulaiman ya kalli Jawad da tsantsar soyaiya yace"lafiya kalau Jawad,sannu da hutawa"

Jawad baice masa komai ba yadai dauki tissue yafara goge bakinsa.

Hajiya Zaliha ta kalli Man Sulaiman tace"Man Sulaiman dan Allah gidan gona zakaje, fruits din gidan nan yaqare, kaje kadebo wasu"

Cikin murmushi yace"to Hajiya insha Allah, za'a debo yanzu"
Yajuya yafice daga falon cikin sauri.

Lokaci d'aya Jawad yaji ransa yayi wani irin baqi,inda yanada iko dayace ya sallami malam Sulaiman saboda tun yana yaro yake ganinsa agidan har kawo yanzu, zuwa wannan lokacin ya kamata ace anbarshi haka da ire-iren wannan aiken.
Hakan yasa ya kalli Mummy wadda hankalin ta yakoma kan waya fuskarsa cikeda damuwa yace"Mummy please kudena aiken wannan mutumin dan Allah,banajin dad'i kokad'an wallahi,idan yana aiki inaji ajikina kamar nine nake aikin, yanda yake faman driving kullum jinake kamar da ga66an jikina yake amfani ba nasa ba,banajin dad'i kokad'an, shekarun sa sunja yakamata kubarshi haka Mummy"

Cikin sauri Hajiya Zaliha ta kalleshi.

ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

Amnah El Yaqoub✍🏻
[1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne.

300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034

Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034.

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

41&42

Cikin sauri Hajiya Zaliha dake zaune agefensa ta kalleshi sannan ta ajiye wayar hannun ta tadawo kusa dashi ta zauna, tadora hannunta akan kafadarsa tace"duk menene yayi zafi haka Jawad? shine abinda kakeso kawai?"

"yes Mummy"

"toya isa,kada kasa damuwa aranka saboda hakan ok?"

Kansa yagyada mata cikin nutsuwa,sai yanzu ne yaji wata irin nutsuwa acikin ransa.

Da yamma yasan Daddy baya nan,hakan yasa yayi shigar qananun kaya farar fatar qafarsa tana sanye cikin wani takalmi me mutuqar laushi irinna zaman falo,computer sace akan cinyarsa yana aiki cikin nutsuwa,sosai yake jin dadin aikin nasa musanman idan yatuna da Mummy ta masa alqawari Man Sulaiman yadena ayyukan dayake.

Wata matashiyar budurwa ce tashigo falon bakinta daukeda sallama,hankalinsa yana kan computer ya amsa mata sallamar da muryarsa qasa-qasa, sannan yadago kansa yazuba mata ido jin muryar yarinyar tanada zaqi sosai kamar ta yarinyar dayaje yasha shayi a gidansu a qasar Niger (🙆🏻‍♀️🤭😳)

Har yarinyar taqaraso cikin falon, bai janye idonsa daga kanta ba,so yake yaga yanda muryarta take kama data yarinyar nan ta Niger shin a fuska ma suna kama?

Mummy data futo daga dakinta ta kalli Jawad tana murmushi ganin yanda yazubawa yarinyar mutane ido yana kallo,har zata masa magana saita rabu dashi tana so taga gudun ruwansa.

Jawad kuwa bakin yarinyar ya kalla sannan yatuna da d'an qaramin bakin Inaas,yaga ba irinsa bane, ahankali ya girgiza kansa, yasake kallon daurin dankwalin yarinyar irin wanda ake fitarda gashi ne, ya kalli gashin nata, yatuna irin yawan gashin Inaas yaga wannan kamar na qari tasaka saboda wanda ya futo daga bayan yafi gashin gaban goshin ta baqi,cikin sauri ya girgiza kansa sannan yamaida idonsa kan computer sa yaci gaba da aiki.

Hajiya Zaliha tayi murmushi tadaga murya tace"Jiddah kin qaraso?"

Yarinyar tayi murmushi tace"eh wallahi Hajiya Ina wuni?"

Mummy ta amsa mata, sannan tajuya ta kalli Jawad wanda hankalinsa yake kan computer kamar ba shine yagama qare mata kallo ba tace"ina wuni?"

Idonsa akan computer sa batare da ya kalleta ba yace"lafiya"

Hajiya Zaliha tajata suka shige daki,basufi minti biyar da shiga ba suka futo hannun yarinyar daukeda leda, dazata wuce tasake kallon Jawad tace masa"sai anjima"

Amma Jawad yayi gim kamar badashi take ba, Hajiya Zaliha tayi murmushi Sannan ta zauna agefensa tace"yakaga wannan yarinyar? tayima ne insa Alhaji yayi magana da babanta sai afasa waccen maganar ta aurenka da Amal?"

Jawad yadan 6ata fuska sannan yace"Mummy already nabaki za6i"

Murmushi tayi cikin jin dadi,sannan ta wuce hanyar kitchen.

Da daddare yana zaune a falonsa dake sama, ba main falon qasa na kowa da kowa ba,coffee ne agabansa yakesha kad'an kad'an,yadauki remote zai kunna kallo ya kalli labarai lokaci daya maganarta tafad'o masa.

(kasan ne? mamana tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah,saboda nidin tadaban ce...)

Yafasa kunna kallon yakoma ya jingina da jikin kujera ya lumshe idonsa,maganarta tasake fad'o masa.

(yanzu daya koreni da wanne kudin zan sake miki kayan daki?)

Furzar da is'ka yayi daga bakinsa sannan ya runtse idonsa,ahankali ya motsa lips dinsa qasa-qasa yace"sun kyautata min"

Kwata-kwata sai yaji kallon yafita daga ransa,mutanan dasuka yimasa irin wannan karamcin basu cancanci haka daga gareshi ba,idan da albashin nata suke amfani wajan siyan abinci hakan yana nufin ya toshe musu hanyar cin abinci kenan? shikuma yazo gidansu ya zauna mahaifiyar ta tayi masa kirki, ta yi masa karamci kamar d'anta.

Ya dade yana tunani,baisan tsawon lokacin daya dauka ba har yaji bacci yafara daukan sa, da wannan tunane-tunanen yayi bacci.

Washegari abokinsa Na'im yakawo masa ziyara, suna zaune a compound din gidan cikin wata yar qaramar rumfa irinta hutawa, guard guda biyu suna tsaye daga bayansu,ga computer agabansa abude da alama wani aikin yake zuwan Na'im dinne yasa ya dakata da abunda yake,daga gefen Na'im gorar ruwan Faro ne guda biyu dakuma Apple manya-manya mai launin ja acikin wani tsarararren plate.
P.a ne ya qaraso wajansu ya rissina cikin ladabi yabashi wasu takardu sannan yace"yalla6ai wannan takardun suna buqatar saka hannun ka"

Kar6ar takardun yayi yana fadin"takardun menene p.a?"

"takardun da kukai agreement ne akan daukan sababbin ma'aikata"

Shiru yayi yana sake duba takardun sannan yayi masa sign din, yahada da wasu takardun dake gabansa yabashi yace"kahada da wannan c.v din nawasu yarane danake dubawa, idan nagama da Na'im saika dawo min dasu"

Cikin biyaiya yace"okay sir"
Sannan yajuya yabar wajan.

Jawad yagyara zamansa ya fuskanci Na'im yace"naje qasar Niger gaisuwa"

Na'im yadauki tuffa guda d'aya yakarya sannan yamaida nutsuwar sa kacokam ga Jawad yace"yeah naga tattaunawar da gidan tv sukai dakai"

Jawad ya motsa lips dinsa kamar bayason magana,har Na'im yafitar darai zai masa magana sai caan yaji Jawad d'in yace"yarinyar ta had'u,idan nacema had'uwa to ina nufin maqurar had'uwa,komai nata gwanin birgewa,har tsawon wasu lokaci surutun yarinyar ya 'DEBE MIN KEWA"(🤭)

Na'im yasake kallon Jawad da tsananin mamaki sannan yasaki murmushi yace " you're talking about lady Jawad,are you serious?"

Jawad yagyara zamansa yace"yeah,hatta ahalinta na lura sunada d'abi'u masu kyau especially mahaifiyar ta,gidan nasu babu kowa,babu hayaniya,inaji kamar naci gaba da zama da matar har abada,kamar kada nafuto daga gidan,tabani shayi,tazuba min ruwa na wanke hannu na,tasake bani shayi, kaiii tayi min kirki de wanda yasa har yanzu tunaninsu duka su biyun yakasa barin zuciyata"

Cikin mamaki Na'im yace"ikon Allah,but tayaya ka'iya shan abun hannunsu? baka tsoron su cutar dakai?"

Jawad yadaga kafadarsa alamun rashin damuwa sannan yace"no,hankali na ya kwanta da matar gaskiya"

Na'im yayi murmushi yasake gyara zamansa sannan yace"but ita kuma yarinyar fa?"

Cikin rashin sanin yana bayyana abinda yake cikin ransa, zuciyarsa d'aya yace"bana tunanin akwai ta biyun ta wajan kyau,surutun ta ya 'DEBE MIN KEWA tsawon wasu minute's din"

Na'im yasaki wata irin dariya yace"wow!!,you're in love Jawad...."

Cikin sauri Jawad yace"no"

Na'im yasake cewa "seriously you're in love Jawad"

Shima Jawad cikin comfidence yace"no,Na'im"

*** *** ***

Niger Republic

Kayan gwanjon dake kanta tasauke agaban matan gidan bayan tayi sallama,Hajara tafara kunce kayan tareda fadin "Me gwanjo yau keda kanki?"

Bilkisu tace"to yazanyi? dole ne mufuto nema"

Hajara tadaga wata riga me kyau tana jujjuya ta tareda fadin"yau ina 'yar taki? kobata nan?"

Bilkisu tace"tana can tana bacci dayake yanzu ba zuwa kamfani,banaso na tasheta daga baccin ta yau nabarta tahuta tunda kullum itace take zarya"

Hajara tace"hakane kam ai tana qoqari ma,yau dinma dakin bari tatashi ai zata zagaya da kayan naku"
Chapter 20 · 0% Book details