← Book details Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 63

Sashe 30

Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

17&18

Yatsun hannunta take ja ahankali duk ta rasa sukunin ta,tanemi surutu, da zaqin baki da tsiwar ta tarasa,gaba daya yayi mata wani irin kwarjini,ahankali tace"yana...yana...um birthday gift din yana wajan manager"

Ahankali yasaki wani irin murmushi wanda yasa Inaas takusa sumewa a tsaye,cikin sigar rada yace"no,ni naki nakeso"

Ahankali tagyada kanta alamun amsawa,amma takasa yarda tad'aga ido ta kalleshi, cikin nutsuwa ya sunkuya ya yanko cake din dake gabansu yanufi bakinta dashi sannan yace"open your mouth"

Inaas sai taji maganar tasa kamar saukar aradu,cikin sauri tadago kanta ta kalleshi gabanta ya tsananta fad'uwa,idanunsu yahadu dana juna,cikin rawar murya tace"yalla6ai a a kabar...."

Kafin tagama cewa ka barshi,yadora yatsan hannunsa guda daya akan lips dinsa yace" shiiii...." alamun tayi shiru,sannan yanufi bakinta da cake din,ahankali tabude d'an qaramin bakinta yasaka mata cake din,cikin darura tafara tauna cake din me mutuqar dadi,yadauki tissue yagoge hannunsa,sannan yazura hannunsa acikin aljihun wandonsa yazaro wata sarqar gold me masifar kyau,yanufeta da'ita,a wannan lokacin kam kusancin nasu yayi kusanci hakan yasa har jikinsa yafara gogar nata,jikin Inaas yafara rawa, shi kansa yaga yanda take karkarwa amma saiya maze kamar baigani ba,yasaka hannunsa na dama ya janye laffayar dake kanta,kyakykywan gashinta ya bayyana saide an nad'eshi abaya anyi mata ribon dashi, idonsa akan gashin nata yanaji kamar ya d'ora hannunsa akai, amma yahana kansa aikata hakan saboda yanzu ma jikinta yana irin wannan rawar idan yadora hannunsa ajikinta sai yaya kenan?
Sarqar yadaga yasako mata ita a wuyanta,sannan ya daura mata sarqar tanajin yanda hucin numfashin sa yake sauka akan wuyanta saboda ya sunkuyo yake kallon kyakykywan wuyan nata,saida yagama kallonta sannan yaja laffayar tata idonsa akan gashinta yamaida mata ya rufe mata kanta yace"tunda kin hanani birthday gift,ni ga nawa nan"

Cikin sauri ta gyada masa kanta sannan tace"nagode Yalla6ai,zan iya tafiya?"

Kai tsaye yace" a a,haka zaki tafi baki bani kyauta ba baki bani cake ba?"

Gabanta yasake fad'uwa,tadago kanta ta kalleshi,da idonsa yayi mata nuni da cake din dake gabansu,sannan yace"idan kika bani saiki tafi"

Inaas tarasa yaya zatayi, tarasa meyake mata dadi,tana so tabar wajan, bata so wannan ke6ewar tasu tasa yayi mata wani abu,ahankali tajuya ta kalli ko'ina taga babu kowa awajan,cikin sauri ta sunkuya ta yanki cake din dan qarami sannan ta nufi bakinsa dashi,babu musu ya rissina ya daidaita tsawon su sannan yabude bakinsa tasaka masa cake din ya lumshe idonsa yana taunawa,Inaas ta kalleshi tarasa menene abun lumshe ido acin cake...

Adede lokacin p.a ya qaraso wajan, cikin sauri Inaas ta janye idonta daga kallon Jawad, ta sunkuya ta dauki tissue din wajan ta goge hannunta kamar yanda taga yayi,p.a ya kalli Jawad cikin ladabi yace"yalla6ai ga saqon"

Jawad ya kar6i ledar,sannan yayi magana da p.a qasa-qasa, Inaas batasan me yace masa ba, tagade p.a din yajuya yabar wajan yanufi hanyar da mutane suka tafi wajan cin abinci.

Saida yaga 6acewar p.a sannan yasake matsowa kusa da ita yasaka hannunsa ya ruqo nata hannun,lokacin d'aya sukaji wani irin shocking, Inaas tafara qoqarin qwace hannunta amma saiya sake riqe ta sakamakon wani irin laushi dayaji hannun nata yanayi,yaso ace su tabbata ahaka har zuwa wayewar gari,amma babu yanda ya iya,dole zaibarta tunda lokacin tashin su yakusa,ledar da p.a yakawo masa yadauka yasaka mata acikin hannun nata, sannan yazaro wani kati mai daukeda numbers dinsa ajiki yabata, yace"please ki gaida Mama,kifada mata nayi KEWAR TA "

yana fada mata haka ya juya yabar wajan da sauri hannunsa zube cikin aljihun wandonsa yana tafiyar sa irinta qaqqarfan namiji ingarma.

Inaas tabishi da kallo harya 6acewa ganinta sannan ta lumshe idonta tasaki wata irin ajiyar zuciya,taji kanta yasara,gumi ya wanke mata goshi kasancewar bata ta6a yin kusanci dawani namiji kamar haka ba,sannan wani namiji bai ta6a riqe mata hannu ba,kafin tagama tunanin taji muryar Hajiya Halima wadda p.a yaje yaturo ta wajan, tana cewa"Inaas mekikeyi anan ke kadai? zomuje mutafi kici abinci kowa yana can banda ke"

Inaas ta kalleta sannan taja ta tsaya ta ajiye ledar hannunta aqasa, sannan tafara qoqarin cire sarqar da Jawad yasaka mata tana cewa"wannan sarqar cire ta zanyi, babu ruwana wallahi Abbana dukana zaiyi idan yaji waye yabani"

Hajiya Halima data riga tasan komai saita nunawa Inaas kamar bata ganeba tace"sarqar mecece wannan din, waye yabaki?"

Inaas ta kalleta kamar zata fashe da kuka cikin rawar murya tace" shine yabani,Yalla6ai Jawad ne"

Hajiya Halima tayi murmushi tace"to meyasa zaki cire? kinsan darajar wannan sarqar kuwa? to kudinta albashin kine na duka tsawon rayuwarki,ai kyauta ce, babu kyau maida hannun kyauta baya,shima Abban ki ai yasan kyauta ce bazai miki komai ba,karki yi kuka kinji,zomuje kici abinci naji manager yana cewa munkusa tashi"

Inaas ta gyada kanta sannan tayi sauri ta maida qwallar idonta, ta dauki ledar daya baya suka tafi,kafin su qarasa Hajiya Halima tace"menene acikin ledar?"

Inaas tabata ledar tace" nima bansani ba"

Hajiya Halima ta bude ledar taga kwalin waya ne sabuwa dal,wayar sak irinta Jawad ce,tayi murmushi tace"ai waya ce,ungo jakata ki riqe saiki saka wayar taki aciki karma mutane su ganki da leda suce waye ya baki"

Cikin sauri Inaas ta kar6i hand back din tata, tajefa kwalin wayar aciki, sannan ta rataya jakar a kafadarta suka tafi wajan cin abincin,suna zuwa kuwa taga kowa sabgar gabansa yake anata ciye-ciye,Yalla6ai Jawad yana can qarshan table din yana cin abinci cikin nutsuwa ko dago ido baiyi ya kalli inda Inaas take ba,bazaka ta6a cewa akwai wani abu a tsakanin suba,kokadan bai bada wannan damar ba,inka dauke manager,Hajiya Halima,p.a dakuma guards dinsa, babu wanda yayi zargin wani abu.

Abincin ma dan kad'an taci, ko yaya tayi motsi sai yanayin su na dazu itada Yalla6ai Jawad yafado mata,ko minti ashirin batayi da zama ba,sukai shirin tafiya,har wajan motocin dazasu shiga Jawad da tawagar sa suka musu rakiya,p.a yabi kowa a cikinsu yabasu envelop wadda kana gani kasan kudi ne aciki,saide envelope din Inaas daban take.

Jawad yana tsaye daga can gefe shida guard,hannunsa guda daya yana cikin aljihun wandonsa,fuskarsa babu fara'ah haka idonsa yana sanye da glass jan duhu, yana ganin yanda p.a yake sallamar su,gaba daya ya tattara nutsuwar sa akanta,haka idonsa akanta harta shige cikin mota sannan yayi ajiyar zuciya yajuya ciki, suma aka dauke su aka nufi Airport dasu,acan Airport dinma basu wani dade ba jirgin su yatashi suka nufo jamhuriyar Niger.

*** *** ***

Niger Republic

tana gama shanya kayanta tawuce zata shige daki,cikin sauri Man Sulaiman yatashi yabi bayanta ya tsugunna yariqe qafafunta yana kuka,tanajin yanda hawayen sa yake d'iga akan qafarta.

Farouq yana zaune agefe saiya gyara zamansa ya kishingid'a yana daga kwance yana kallonsu uffan baice musu ba.

Bilkisu taja qafarta taja takasa qwace wa daga ruqon dayayi mata,cikin kuka yace"Bilkisu dan Allah ki yafemin, Bilkisu nasan cewa nime laifi ne a wajanki,kiyi haquri ki yafemin,Bilkisu idan baki yafemin ba haqqin ki bazai daina bina ba,dan darajar Annabi Muhammad s.a.w Bilkisu kiyi haquri kidawo mugina sabuwar rayuwa domin ingoge kuskuren dana aikata miki Abaya,naje gida neman ki,anfada min cewa kintaho nijar,Bilkisu nazo nan qasar nayi kwana biyu ina neman ki, bansameki ba,sannan acan gida sun fad'a min cewa kin haihu,kin haifi da namiji,Bilkisu ina gudan jinina yake nima in ganshi ko zanji dadi?"

Kallonsa tayi fuska babu alamun karaya tace"Manu,saboda ka hadani da darajar Allah da ma'aiki ne yasa nayima magana,amma banda haka, banida wata alaqa dakai dazata sa magana ta hadamu,yaro dakake tambaya ka dade da salwantar da danka,ta dalilin ka na rasa dana,Manu bazan ta6a yafema ba, tun kafin in dauko wuqa Manu ka sakarmun qafata inwuce"(😳🙆🏻‍♀️)

Manu yajuya ya kalli Farouq dayake kwance yana jinsu kamar baya wajan,cikin hawaye yace"Farouq kasa baki dan Allah, katayani neman yafiyar Bilkisu,inaso tabani dama nagyara kuskure na,tun bayan barin Bilkisu daga cikin rayuwata har yanzu bana bacci cikin nutsuwa,katayani bata haquri Farouq"

Kafin Farouq yayi magana Bilkisu ta waiga gefenta tazaro wata wuqa tanufo Manu da wannan wuqa gadan-gadan.(🙆🏻‍♀️)

Cikin sauri yasaki qafarta yayi baya,cikin 6acin rai tasa gefen zaninta ta goge inda yasa hannu yariqe mata qafar sannan tayi wani irin tsaki tashige ciki tareda rufo qofar.

Wani irin kukan baqin ciki da nadama yakama Man Sulaiman, duk irin soyaiyar da Bilkisu take masa yau shine take goge inda hannunsa ya ta6a jikinta, rayuwa kenan.

Farouq yatashi zaune yace"katashi kaje,idan tahuce saika dawo kuci gaba"(😂🤭)
Chapter 30 · 0% Book details