Sashe 1
Me Debe Kewa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝
('yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu's name
https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu
1&2
Da sunan Allah mai Rahma mai jin qai,ina sake yiwa Ubangiji godia daya nuna min ranar dazan fara posting wannan labarin lafiya,littafin ME 'DEBE KEWA na dad'e da fara rubutunsa,tun kafin na rubuta littafin MAWAHIB nake faman rubutu akan littafin ME 'DEBE KEWA,idan har akwai wani sharri wanda zai amfani al'umar Annabi asandin wannan labari,ina roqon Allah karya bani damar dazan kaishi qarshe,ina roqon Allah yasa na rubuta abinda zai amfani al'uma baki d'aya,Alkhairin dake cikin wannan labarin ina roqon Allah ya sadamu dashi,ina roqon ku kada kuyi amfani da qyale-qyalen dakukaci karo dashi acikin wannan labari,kuyi amfani da darasin da littafin yazo muku dashi,ina Addu'ah ga duk wasu mata iyayenmu da qannanmu,da yayunmu masu juna biyu ubangiji Allah ya saukesu lafiya,wanda suka rigamu gidan gaskiya da wanda sukai rashin iyayensu Allah yaji qansu yayi musu Rahma,Allah yasa Aljannah ce makomar mu baki d'aya,Allah yayi mana tsari da talauci,Allah ya sauqaqa mana wannan yanayi na matsin rayuwa damuke ciki.
ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,naso in kawo muku shi tun 2023 kamar yanda na saba kawo muku littafi sau biyu a shekara,amma Allah bai nufa ba sakamakon wasu uzurirrika dakuma salon bincike da labarin yazo min dashi.
Akwai wanda suke siya littafi na,saisu koma gefe su dinga siyar dashi,ban yarda ba,ban amince ba,ko kad'an daga cikin labari na ban yarda ajuyamin ba bare asiyar dashi,babu kyau shiga haqqin mutum bare kuma d'an uwanka musulmi.
Wannan labari gaba d'ayansa na sadaukar dashi ga dukannin masu Suna BILKISU,yanda sunan littafin yazo ME 'DEBE KEWA, ina Addu'ah Allah yasa ya 'DEBE muku KEWA.
Lokacin dana rubuta littafin MAWAHIB,dayawa daga cikin masoyana suna min complain littafin yayi tsada,dan Allah na rage suna so su siya,harma da wanda suke cewa dan Allah inci gaba da rubuta labari akan farashin 300 Naira,nikuma ina ganin ai dad'in labari shi kesa mutum ya siyeshi ko naira nawa aka sa,to kunfi qarfina 😣, dama saboda ku Amnah take rubuta littafi,idan babu Readers babu rubutu,kamar yanda kuka roqa gashinan littafi daidai da aljihunku,dan Allah idan kinsan zaki siya ne domin ki dinga fitar min dashi zuwa group to wallahi na haqura da 300 dinki😭
Ku riqemin amana dan Allah,duk wacce taga tayimin magana ta private ban saurareta akan lokaci ba,tayi haquri,tayi haquri,tayimin uzuri dole zan saurare ta saboda Amina ta kowa ce,ta dukkanin fan's dinta ce🥰
ME 'DEBE KEWA naira 300 ne kacal,duk wanda yakeson wannan labari zai iya yin payment ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034
masu tura kati transfer kokuma photon Kati,zaku iya turowa ta wannan number 08033300034
_____
Garin Malam...Hadejia Area,Jigawa State.
{ 1986.}
Shekaru Talatin da Bakwai baya.
Gidane d'an qarami wanda yake d'aukeda d'aki qwaya d'aya jal ginin qasa,be samu arziqin samun Katanga irinta d'akin ba,wato katangar qasa,saide yasamu arziqin samun katangar zana,ita kanta zanar da'akai katangar da'ita batakai har qarshe ba saida kara aka qarasa ta.
Gidan abushe yake qaraf bashida komai face wata madedeciyar bishiyar maina me mutuqar sanyi,kana ganin gidan kasan gidan wani mashahurin talaka ne futuk wanda bashida cin yau bare na gobe.
Kyakykywar mace me shekaru aqalla talatin da biyar tagama share gidan daqyar saboda tsohon cikin datake dauke dashi me mutuqar girma haihuwa yau ko gobe,gumin fuskarta ta share,ta nufi qasan bishiyar gidan ta zauna tana maida numfashi tareda lumshe idonta tanajin dad'in is'kar datake kad'awa,jingina tayi da jikin bishiyar hakan yasa d'an kwalin dake d'aure akanta yazame yafad'i,wani uban gashi me sheqi da bala'in tsawo ya bayyana,gashin nata baqi ne sid'ik,ita kanta idan ka kalleta karon farko zaka tabbatar matar manya ce,asalin kalar farar fatarta zaisa kagane cewa ba 'yar Nigeria bace.
Ahankali tajuya ta kalli d'akinsu da tsakar gidan wanda babu komai yaqare,babu abinda zata samu tasa acikinta,amma duk da haka cikin dauriya ta shafa qaton cikinta tace"kayi haquri kaji,Babanka zaizo yakawo mana abinci"
Kafin ta d'auke hannunta daga kan cikin,mijinta yashigo gidan bakinsa d'auke da sallama,tun kafin ya qaraso inda take yagama qare mata kallo yana sake yiwa Allah godia daya azurtashi da Samun mace kamarta, yasan cewa banda qaddara da qudurar ubangiji itadin ba sa'ar aurensa bace,amma sai gashi ubangiji bai dubi hakanba, ya mallaka masa ita amatsayin mata d'aya tilo.
Zama yayi kusa da'ita har jikinsa yana gogar nata,ya kalleta cikeda kulawa da tsantsar so sannan yace"Mai Gadon zinare yakike zaune haka kai babu dankwali?"
Murmushi tayi dimples dinta suka bayyana,wanda suka sake qawata kyawun fuskarsa na asalin buzuwar qasar Nijar,cikin shauqin qauna tasaka hannunta tafara tattare dogon gashinta,cikin sauri yasaka hannunsa yana tayata tattare gashin,cikin jin dad'i tace"Malam zafi naji,bansan lokacin da dankwalin yafad'i ba,da alama de yau kasamo mana abinci,na ganka da farinciki"
Murmushi yayi,sannan yasake gyara zamansa yana fuskantarta "wato Bilkisu duk lokacin dana tuna inada mace kamar ke acikin gidana,hankali na yana kwanciya,duk rashin kud'i na da talaucina,inde na kasance tare dake kina 'DEBE MIN KEWA,ina farinciki ne saboda nasamo mana kud'i masu yawa har kimanin naira dubu d'aya" ya qarasa maganar yana futo da kud'in daga aljihunsa ya ajiyesu agabanta.
Takardun naira ashirin-ashirin ne dayawa sai kuma qwandaloli da ficika.
Kyawawan fararen idonta ta zaro,cikin tsananin mamaki dakuma ganin yawan kud'in yasa ta kalli mijin nata tace"Malam Ina kasamo wannan kud'ad'en masu yawa haka?"
"kekena nasiyar Bilkisu,lissafa kigani cefanan kwana nawa zai mana?"
Manyan idonta ta lumshe sannan ta bud'e,taja hannunsa guda d'aya tad'ora akan qaton cikinta,cikin damuwa ta kalli mijin nata tace"dani da d'ana zamu jure duk wata yunwa amma ba zamu jure ganinka babu abinda kake sana'ah dashi ba,yanzu daka siyar da kekenka dame zaka dinga dako kana samo mana abinci?,meyasa kasiyar?"
Kansa ya sunkuyar qasa cikeda damuwa da rashin sanin makomarsa,cikin nata ya shafa sannan yace"Bilkisu bake kad'ai bace,idan ban sai dashi ba mezan baku kuci?"
Hannunta tad'ora akan nasa hannun wanda yake kan cikinta sannan tayi murmushi dimples dinta suka futo ta kalli cikin idonsa tace"shima yaron cikina zaiyi haquri,yasan cewa yau Babansa bai samo mana abinci ba"
Cikin jin d'adi ya kalli fuskarta yace"Bilkisu waye yace miki namiji zaki haifa ne?"
Cikinta ta shafa cikin kulawa dajin dad'i tace"Babu Wanda ya fad'amin,amma Ina fata,Ina Addu'ah Allah ya azurtani da d'a namiji,zan saka masa sunan mahaifina sannan kuma sunan fiyaiyen halittafi Annabi Muhammad (s.a.w)"
Murmushi yayi,ya kalli cikinta sannan yace"Bilkisu ko mace kika haifa,ko namiji, zanyi farinciki da duk abinda kika haifamin,kuma ko abinda na mallaka zai qare gaba d'aya,insha Allah abinda zamu haifa sai yayi karatun Boko,kwanaki dana shiga qasar Hadejia,Naga wani yaro matashi yasa wannan baqaqen kayan(Suit) irinta manyan ma'aikata,yana magana yana zaro turanci sai abun ya birgeni,naji duk duniya babu abinda nakeso irin boko,amma tunda ni Allah yasa banida rabon yin boko har iyayena suka rasu, insha Allahu zan tsaya tsayin daka,Inga jinina yayi karatun boko,sannan...."
Kafin yaci gaba da magana suka jiyo ana kwad'a sallama a qofar gida.
Tashi yayi yafita,yana zuwa qofar gidan nasa yaci karo da mutane kusan su bakwai,d'aya daga cikinsu mai kimanin shekaru ashirin da takwas yace"Malam MANU kud'in bashin mu mukazo kar6a,duk wanda kagani anan yaji labarin kasaida keken kane shine ya biyo bayanka kabashi haqqinsa,amma inaso kafara sallamata saboda bashina yakusa shekara biyu a kanka kullum kalmar haquri kake fad'amin"
Malam Manu yayi shiru kamar an doka masa sanda,yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya yad'ago kansa ya kallesu yace"jama'ah,dan Allah kuyi haquri,ku rufamin asiri kamar yanda Allah yarufa muku,wallahi zan biyaku bashin ku,bamuda abinda zamu ci nida iyalina...."
'Daya daga cikinsu wanda yadan manyanta yace"kaga dakata malam Manu,yaushe mukai dakai zaka biyani kud'ina?"
Cikin sanyin jiki yace"Tun wata uku dasuka wuce yadace nabiyaka"
Cikin rashin tausayi mutumin yameqa masa hannu sannan yace"to Alhamdulillah,qirgosu naji d'uminsu..."
Malam Manu baisake cedasu komai ba yajuya yashigo gida,baqin ciki da taqaici yasa baisan lokacin dayaji wani irin hawaye mezafi yazubo daga idonsa ba.
Tana ganin haka tasan cewa ba qalau ba,tashi tayi daqyar ta qarasa wajansa,cikin damuwa tace"Malam meyake faruwa? Yanaga jikinka a sanyaye mutuwa akayi?"
Hawayen idonsa yashare daqyar sannan yace"Bilkisu masu kar6ar bashi ne,nabasu haquri sunqi tafiya,Ina murna na saida kekena zamu samu abinci ashe duk da haka ban tsira ba,bamuda komai a gidannan wanda zan d'aga in siyar,babu abinda yarage min saide wannan kayan na jikina zan saida musamu muci abinci"
Ya qarasa maganar yana mata nuni da kod'ad'd'an yadin dayake jikinsa.
Cikin son kwantar masa da hankali tace"ya'isa,kayi haquri kadena kuka Ina zuwa"
Dan kwalin kanta tacire,dogon gashinta na asalin buzuwa ya bayyana,ta warware dankwalin tayafashi akanta sannan ta qarasa qofar gidan da sallama, d'aya daga cikinsu ne yazaburo tun kafin tayi magana yace"kudin ne?"
Yayinda sauran suka qura mata ido suna kallonta saboda tsananin kyawunta dasuka gani,cikin zuciyarsu kuwa mamaki suke dama acikin wannan qauyen nasu na Garin Malam ashe akwai matan India aciki?🤔
Murmushin qarfin hali tayi tace"A a, kuyi haquri,dan Allah ku qara masa lokaci insha Allahu zai biyaku kud'in"
Wanda yafara tambayarta kud'in da farko yanzu ma shine yasake yimata magana yace"kinga...idan kud'in ki kazo kawowa to kawo kiwuce, idan ba kud'in kika kawo mana ba,juya kituro mana Sulaimanu"
Murmushi tayi idonta na kawo ruwa,sannan ta meqa musu dubu d'ayan hannunta wanda malam Manu yabata,cikin rawar murya tace dasu "gashi"
Babu musu suka kar6a, lokaci d'aya hawaye yazubo daga cikin idonta zuwa kan farar fatar fuskarsa,hawayen ta goge tace"dan Allah kubamu ko naira ashirin ne mu sayo wani abun muci..."
ko sauraren ta ba suyi ba suka fara fad'a akan kud'in kowa yanaso a bashi kasonsa aciki,saboda kud'in sunyi kad'an akan yanda sukebin Malam Manu bashi, ahankali ta girgiza kanta tajuya tadawo gida tana jiyo hayaniyar su suna fad'a akan yanda za'a raba kud'in.
Zama tayi akusa dashi baisan ma ta'iso ta zauna ba yayi nisa acikin tunanin halin dasuke ciki,shiba kowa ba duk danginsa sun rasu, ita ba kowa ba dan'uwan ta qwaya d'ayane shima yana qasar nijar,ya kalli katangar gidansa ta Kara da zana gaba d'aya duk ta mutu gara ta cinyeta kad'an yarage afara ganinsu daga waje,kana ta6ata zata Iya fad'uwa.
Maganar data masa ne yasa yadawo hayyacinsa,yasaka hannu yagoge hawayen idonsa bayan yagama jin kalaman ban haquri daga matar tasa.