← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 56

Sashe 9

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma dai na ce,"wai a jira na awa
aya".

Agogonsa ya kalla kafin ya ce,"to zauna mana kin wani tsayan aka".

Kaucewa nayi na basa wuri zan sauya kujera na ce,"bana zama wurin da yake da najasa".

Kuma kafin in zauna ya taso yana cewa,"muje mu dawo".

Bayan fitowar tamu daga asibitin wajen masu siyar da kayan marmari mu ka nufa, ina daga cikin mota ya fita, haka aka jido komai na kayan marmari sai da aka cika leda. ya bu
e bayan motar aka zuba su, sannan ya tafi wani kanti, bayan mintuna ya dawo tare da yaron shagon hannunsa ri
e da katan
in maltina da na madarar gwangwani peak ta ruwa.

Bayan ya dawo motar ya zauna ne ya ke cewa da ni,"sai mai ya kamata akaiwa mara lafiya?".

Na ce,"ko iya wannan ma yayi, amma in da dama a siya kaza gasashshiya ko nama balangu".

"Ok". ya ce, sannan ya tayar da motar muka wuce.

Kaji ya siya manya guda uku anan wajen wani cin abinci na albaik, daga nan kuma mu ka wuce asibitin Imamu Wali shi ma anan jan bulo
in ya ke gaba da asibitin da muka je.

Sai da muka isa asibitin ne tukunna ya sami damar bu
e baki yana min bayanin wai yaron da ya ka
e jiya zamu duba. da "to". kawai na amsa shi muka
ebi kayan dubiyar da muka siya muka wuce zuwa ciki.

Ni dai bin sa kawai na ke zuciyata na
issima min wasu abubuwan, emergency ward muka je, ashe da gaske ne yaron ya bige, ai da ya fa
a min ce na ke ya fa
i hakan ne kawai don ya kare kansa.

Kuma Allah sarki yaron
arami ne ya sha jiki don har karaya ya samu a
afa, sai dai jinin ma da Hubbi ke cewa zai bayar an samu wani
anin Baban yaron zai bayar.

Mun
an jima kafin mu yi musu sallama, suna ta godiya kuwa kamar yawun bakinsu zai
are, ni ban sani ba ma ashe kusan kowa ya zo a
an gidan su Hubbi, uwar yaron har da hawayenta wajen yi min godiya wai mijina mutumin arzi
i ne.

A can asibitin da muka je aka min test muna zuwa ya kar
o result
in, ya jima a ofishin likita kafin ya fito, ni dai tun da ya fito na kalli yanayin fuskarsa naji jikina yay sanyi, na nemi sukuni na rasa, hankalina duk ya tashi, ko magana bai yi min ba yay gaba na bi bayansa.

Motar ma yacca ya figeta ka ce wani bala'in ya
i za'a yi, da haka muka baro asibitin ni dai na kasa magana kuma maganar na ke so in yi, shi kuwa kana kallonsa zaka san cewar ransa babu da
i kwata kwata.

Lokaci
aya idona ya cika da ruwan hawaye, ba'a fa
a min gwajin da aka yi min ba, haka kuma ba'a fa
a min sakamakon da aka samu ba, amma tuni zuciyata ta gama raya min abin da sakamakon ya bayar, shikenan tawa kuma ta
are, ta tabbata da gaske bana haihuwa, yanzu cikin wannan tsananin halin wa zai rarrashe ni?, madafar da na ke gani in ji da
i yanzu bata ni ya ke ba, fatana
aya kar aurena ya dagule ta silar hakan.
hijabina na saka na goge hawayen da ya sakko min, Allah ka
ai ya san me na ke ji a zuciyata, yanzu shikenan har in koma ga mahallicina ba zan ga jinina ba?, ba zan haifi yaron da zai kalle ni ya kira ni da mahaifiya ba?, zan mutu ban bar wanda za'a ke gani ana tunawa da ni ba in ci arzi
in adu'a ta dalilinsa, shikenan duniya ba zata kira ni da sunan uwa ba?.
warai na san an bu
e min babin
alubalen dangin miji na tsantsar cin mutunci da gori akan rashin haihuwa?, canjin matsayi a wurin miji?,
arin aure ya tabbata lahu na sani, don haka dole ne cin zarafi daga kishiya, wani sabon kuka ya zo min, na kifa kaina a saman
afata ina rera shi a hankali, na sani tabbas duk wani abu da zai samu bawa daga Allah ne, kuma hakan alkhairi ne a gare shi, fatana
aya ubangiji ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar rayuwar.

Ina cikin kukan na jiyo muryarsa yana fa
in,"wai ke babu ranar da za ki girma ne?, kina wani kuka sai kace jaririya, mene hakan?, ba'a miki komai ba ki kama kuka, wannan ai shirmen banza ne".
aga ido ina kallonsa, gaba
aya babu wani tausayina a saman fuskarsa, balle a biyo ga batun rarrashi da ban ha
uri da nasiha, dama tuni ya saka hijabi a tsakaninmu kan wa
annan abu ukun. ba a komai ne ka ke da bu
atar ayi maka bayani ba, wani abun hankalinka da tunaninka zaka sa ka fahimta, tsawon watanni ban san matsalar da ta kawo canjin yanayin zama tsakanina da shi ba, amma daga abin da Yayarsa ta zo tayi min jiya na
ora samun sa
aninmu da shi akan hakan, don na san dai tabbas in har laifi nayi za'a fa
a min, shi mutum ne dai baya
oye wannan. hmmm
warai na sani yanzu zan shiga wata sabuwar rayuwa ne, ba fata na ke wa kaina ba, amma na sani na gama rayuwar farin ciki a gidan aurena, domin banga alamun Hubbi zai kar
i wannan
addarar tawa ba, banga alamun zai taya ni mu cinye jarabawar tare ba, lamarin zai zama tamkar ni na gaza ne.

Muryata gwanin ban tausayi na ce masa,"Hubbi ba ka fa
a min abin da likitan ya ce ba".

"ke kika kawo kanki?".

"Ba ni na kawo kaina ba amma kuma tawa lafiyar aka duba ai, ina son sanin abin da likita ya fa
a kaji, ina son sanin abin da yake damuna".

Maimakon amsar tambayana sai jan tsaki yay. a maimakon gida sai naga mun
auki hanyar gidansu, haka kawai kuma a karo na farko naji ina tsoron zuwa gidan, daga waje ya ajiye motar bamu shiga da ita ciki ba.

Ni ya bawa ledar siyayyar da mu ka yiwa Iyam, ginin gidan irin ginin tsakiyar nan ne, babban parlo zaka fara shiga, a ciki kuma kowa da
angarensa ta can ciki. shigarmu falon mu ka tarar da Amarya, tana ganinmu fara'a ta wanzu a fuskarta tana tafa hannu wajen yi mana lale lale.

Nayi
arfin halin
oye damuwata na aro jarumtar fara'a da walwala na yafa. na du
asa na gaisheta daga bisani kuma su ka shiga gaisawa da Hubbi. nan yake cewa da ita,"na ji gidan tsit".

Ta ce,"umm suna can falon Malam ana hira".

"Iyam ma tana can?".

Ya tambaya a lokacin da yake cire hularsa yana susa.

"anya kuwa, kamar dai tana
akinta".
sai kuma ta dube ni tana cewa,"kin san bamu jima da gama hirarku ba, na ke cewa ya kamata in samu lokaci in shiga in duba ku, ashe ma kuna tafe a hanya. to fatan dai duk kuna lafiya".

Ina murmushin ya
e na ce,"muna lafiya lau, ya muka same ku?".

Ta ce,"lafiya lau.

Tashi ku shiga ciki nima zan
aukowa Malam abincinsa ne".

Hubbi zai wuce ta dakatar da shi da cewa,"Malam yini yay yau bai ji da
i ba fa, ku fara biyawa ta wurinsa,
azu ma da
yar ya iya zuwa asibiti duba yaron da ka bige...yauwa Nazifi kaga anata mantawa, AC
in falon nan da fankar
akin Gwaggoje sun lalace, ita ma Ummaa naji tana akwai gyara a
akinta".

Ya ce,"tom shikenan za'a gyara da wuri in sha Allahu".

"Madallah Allah yay muku albarka, ya
ara maka bu
i da wadata ko don taimakawa ahalinka da ka ke yi".

Sashin Malam mu ka wuce, ina saka
afata a falon sai kuwa
an yaran su ka taso kowannensu da murnar yana fa
in,"oyoyo ga Anti Ca'ida".

Su ka cukwikwiye ni sai farin ciki su ke da ganin nawa, Lubabatu ce me cewa da su,"ba za ku
yaleta ba sai kun yar da ita".

"Ni dai ce matar Yaya kayami ta bani biccit zan caketa".
cewar Sahura
ar gidan Anti Aisha, cikin muryar gwarancinta me abin dariya.

Abasiyya ta ce,"ai ko to duk wanda bai rabu da ita ba ba za'a ba shi abin da aka siyo ba, tun da duk ba ku iya gaisuwa ba".
da saurinsu su ka sakeni kowacce na gaishe da ni cikin maganarsu ta
an koyo, da yake cikinsu duk babu wacce ta haura shekara biyar, Mansur ne ma da ya
ara wayo kwanan nan maganarsa ke fita sosai.

Shigowar Hubbi falon kuma duk sai suka yi kansa, dama shi gwanin son yara haka ya tarbesu da fara'a yana ba su hannu su tafa.

Malam ya fito daga cikin
akinsa muka gaishe shi tare da yi masa sannu da jiki, yaji da
in zuwan namu kuwa sosai, nan aka
ora hirar da ake yi da mu, Amarya ta kawo mana abinci, ni dai na ce ta ha
e mana da su Lubabatu mu ci tare, dama shi Hubbi bai tsaya wata wata ba ana kawo masa ya tankwashe
afafu ya shiga ciki, da ike ma'abocin tuwan masara miyar ku
ewa busashshiya ne.

Bayan mun gama cin abinci mu ka mi
e don wucewa, kamar kullum in muka zo Malam yay mana nasihohin da ya saba, da
ara bamu tarin adu'oin da ya kamata mu ri
e a ko da yaushe musamman na tsari. mu ka yi godiya da adu'ar Allah ya
ara lafiya sannan mu ka fito zuwa wajen Iyam.

Can na baro Hubbi ya shiga
akin Yayan Shago.
Chapter 9 · 0% Book details