← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 56

Sashe 33

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Awa guda da wasu
an mintuna na
auka ina gyaran, na ci wahala sosai don bayana kamar zai karye. bayan na gama na saka turaren wuta da air freshner sannan na fito na sameta ita da jikokinta, na kalli agogo
arfe tara da rabi, cikin girmamawa na dur
usa gefenta na ce,"Iyam na kammala ko za ki duba ki gani".
tashi tayi tana cewa,"mu je in gani Allah sa ba gyaran son zuciya kika yi ba".
tayi gaba ni kuma na
auka jakar kayanta na bita, hankalina sam ya
i kwanciya da zamanta
in a gidan. tsaye na sameta tana bin
akin da wani irin kallo, har cikin ranta nasan yayi mata amma kawai dai saboda a kushe a nuna baka iya ba don an tsaneka sai ta kya
e fuska ta dube ni ta ce,"kayana fa to?".
kafin na bata amsa sai ga
an nata ya shigo da
atuwar katifa wadda ta kan gadonsa ce ya ciro, wajen biyayya kam a wajen mahaifiya ba daga nan ba, shiyasa ita kanta kaf
an nata tafi sonsa.
na kama masa muka sanya katifar ya ba za mata sabon bedsheet me bala'in taushi, ya koma ya
auko sabon blanket da ya taho da shi daga saudiya ya ajiye, dama akwai sababbin fulalluka duk aka saka mata.
da yake da taimakonsa aka
arasa gyaran sai ta washe baki tana yabawa sai jera masa sannu take yi. sannan ne shi kuma yake cewa da ita tayi ha
uri zuwa gobe a kawo gado da wadrobe da dai sauran abubuwa
ata.

"a'a ni hakan ma ya ishe ni Nazifi Allah yay maka albarka, abu da ba zaman dindin zan yi ba, Malam ne fa yana dawowa zan koma gida, idan na zauna can ne hankalina sam ba zai kwanta ba tun da gidan naka ya rasa macen arzi
kallona yay ta gefen ido ina kallonsa, ya ja numfashi ya sauke ya ce,"duk da haka dai za'a saka komai zuwa gobe in sha Allahu, Malam ko da kwana
aya zai yi ai ba zan barki haka ba balle watanni da yawa zai yi".

"to ai shikenan, kaje ka kwanta ka huta sai da safe. yaran ka turo min su nan mu kwana tare".
ya juya ya fita nima na bi bayansa bayan na ce mata sai da safe, ba kuma ta tanka min ba banda tsaki da ta bini da shi.

Tun daga wannan ranar na janye jikina daga shi Nazifin, Yaran da kuma Uwarsa, tsakanina da su gaisuwa ce, shine ma kawai zan samu arzi
in ya amsa min amma ita Iyam kam dama naci daraja ta amsa ciki ciki, shi kuwa idan ba maganar da ta zama dole ba ko ganinsa ma bana tsayawa na yi.
an uwansa kuwa sai su zo su yini ban gansu ba, don yanzu sun mayar da gidan kamar na su, tunda mahaifiyarsu na ciki a sati bai fi sau uku ne basa zuwa ba, kuma in aka zo tun safe sai a yini ana nuna iko da isa, aita bidiri ni dai bana bi ta kansu tun gaisuwa da zata ha
amu wacca za'a amsa min a wula
ance, dama in suka zo bana girki da kansu su ke shiga kitchen su dafa son ransu, sunce suna da iko da gidan don haka ba za'ai masu iyaka ba, ni dai ko kusa bana ta
a biye musu zaman
akina ya fishshe min.

Ni a yanzu ba Nazifi ne ka
ai bana so ba hatta aurensa bana so, kuma har mutuwa ta na
e ba zan manta da ba
in cikin da ya dasa min a zuciya ba, bana tuna komai da yay min, haka bana tuna duk abin da
an uwansa da uwarsa ke min, abu
aya na ke tunawa da shi ka
ai ya tsaya a raina shiga tsakanina da mahaifina da yay, har ta kai yanzu idan na kira wayar Abbaa ba ko da yaushe ya ke
agawa ba, idan ya
aga kuwa magana sama sama, wataran ma sai dai na kira Ummani in ro
eta ta ha
a ni da shi. fushi da Abbaa ke yi da ni shi
aya ne ciwon da ke dashe a zuciyata, ba Nazifi da abin da ya dangace shi ba, hakan ne ka
ai yanzu abin da ke saka ni zubar da hawaye a kowacce rana amma ba akan Nazifi da takaicinsa ba, haka ina ji ina gani mahaifiyata ta kwana uku babu lafiya amma Abbaa ya ce in har na zo gida babu ni babu shi, ranar ban iya runtsawa ba, ban iya shan ko da ruwa ba, amma a haka muka yi waya da mahaifiyata tana bani ha
uri da shaida min ta sami lafiya bacin na san kawai ta fa
a ne saboda in kwantar da hankalina,
arshe sai yaran ne su ka zo suna ce min sunje duba Ummani har ma ta basu sabuwar atamfa a
inka musu, suna ta murna abinsu suka bani na aje musu na ce su kaiwa Kakarsu.

Yashaik kusan duk sati biyu sai ya zo gidana, ko in bai zo ba ya kirani a waya ya ce in ba su, da kansa zai saka yaran a gaba da tambayar ina yi musu wani abun ne, wannan kuma na san sawar Kaka ne, to da yake dai
an sharrin basa kansu sai suce masa bana musu komai, ban sani ba ko da na fita a sabgarsu ne yasa su ka fara sanyi da makircinsu oho, ni yanzu abu ma idan ina da bu
ata Ummani na ke kira, ita ke tura min ku
i in kashe sabgar gabana da yake yaga idan na tambayi fita yana bari.
kuma dalilin rashin zuwana gida duba Ummani Maman Yasmin ta kira ni a waya, na zayyana mata duk abin da ya faru tace ashe shiyasa Yashaik ya
i ha
a kayan sallah da ni wannan karan, ta tuna ranar har itama sai da yay mata masifa, nan fa ta hau min fa
a da ke jarababba ce itama shiyasa ita
aya ke iyawa da jarabar mijinta, kafin ta shiga ro
ona akan in aje ha
urina da sanyina a gefe na
an wani lokaci in fara rama abin da ake min hakan zai saka duk su saduda, amma wannan ha
urin da na ke shi ke basu lasisin ci min fuska har shi mijin. saboda haka na aro rigar rashin mutunci da masifa da bala'i in saka in zama kamar wuta saboda zafin rai, in ci kutumar uban duk
an iskan da yay min ko da kallon banza ne balle ya nemi ya gaya min magana, ta ce harta uwarsa kar in raga mata,
ari in koyi kissa in yi kaman zan mata sujjada a gabansa amma a bayan idonsa in nuna mata karrr na ke bani da mutunci ko
was, idan na fara hakan za su rabu da ni su kama abun da yake gabansu nima in huta.
na ji shawarartata na
an hau kan wata, tun da lalla
awa na ke kar na za
e da yawa ya kuma kai
arata gidanmu in shiga uku. yanzun dai yadda nake ha
e rai idan na gansa har shakkar yi min magana yake, na fita harkarsa gaba
aya na cire tsoro sai ya fara mamakina hakan kuma ya dame shi, ya fara neman shishshige min yana neman shiri, ni kuwa sam na
i basa fuska na nuna masa nima mutum ce me zuciya a
irji. ko fita zai yi bana damuwa da in bisa in masa a dawo lafiya, sai ga shi in yaga dama wani lokacin idan zai fita ya zo yace min zai fita, ba kuwa na
aga ko gashin gira na kalli inda ya ke, hatta
akinsa yanzu tsakanina da shi in kai masa abinci da na gama gyara kuma sai washegari, karatu ma sai na so nake zama yay min, ranar nan babu yanda bai da ni ba akan in zo
akinsa cikin dare nayi mursisi na
i zuwa, domin na
udurci ni da zuwa
akinsa sai ranar da ya san darajata.
______________________________________
*(17)*
To haka dai na ke ta zaman babu da
i, duk wani nawa da ya kamata ya zo gidan in gansa inji da
i Abbaa ya hana domin da kansa yasa aka kira masa me gadi da shi Nazifin ya fa
awa me gadin duk ba
on da aka yi ya tambaye shi wurin wa ya zo, in dai wurina aka zo to kar ya bari a shiga. to Yashaik
in ma da yake zuwa ya daina, in ya zo dai fa
a ne ke kawo shi to amma a haka na ke farin ciki.
angarensa yanzu ba na da wata matsala tunda babu abunda ke ha
amu, daga wajen Iyam ne dai da kuma
an uwan nasa abun babu sau
i matsalar ta tsananta har tafi da, sun matsa min sosai cin mutuncina su ke yanda suka so. duk abunda su ke min haka nake shanyewa in hana kaina damuwa tun da dai haihuwar ba ni zan bawa kaina ba, haka kuma shi da su ke yi akansa
in ba ya yi min, tunda ba shi su Atika ya rage nuna damuwa akan rashin haihuwar.

Maman Yasmin kuwa ranar ta saci hanya tazo ta din
a fa
an maita da rashin zuciya irin nawa ne yasa na ke zaune a gidan, in bar musu gidan mana rabuwa da Nazifi ai ba shi zai hana ni
ara yin aure ba. na ce mata sam ba rashin zuciya ba ne ina gudun bakin mutane ne da kuma
acin ran iyaye, domin duk ranar da Abbaa ya tashi zai ce min babbar biyayyar da zan masa ita ce na zauna gidan mijina, Ummani kuwa da ta tashi yi min nasiha zata fara ne da ha
uri sannan ta tafi ga batun babbar suturar
a mace shine aure, kuma gidan miji shine mafi daraja wajen
a mace.
Chapter 33 · 0% Book details