← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 56

Sashe 44

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashe har da Nazifin shima yana wajen naji yana ce masa,"Kai kuma susun banza ai da iliminka, ina addini ya ce saboda ka aurota ka bar mahaifiyarka da
an uwanka su wula
antata?

Ina ce addini ce yay ka tsareta ka tsare mata mutuncinta da kimarta, ko ita
in jaka ce ko daga sama ta fa
o ka tsinceta ka aura da zaka bar
an uwanka na cin zarafinta?...".

Iyam ta iso wajen tana cewa,"Sam sam sam ban yarda da hakan ba, babu ruwanka da shishshigi, idan matarka ka zo
auka to
aukarta ku tafi ba zaka saka yarana a gaba kana faman yi musu fa
a ba".

Tana yin shiru ya ka
a kai yace,"tom shikenan".

Ya juya ya
are musu kallo ya ce,"ku ci gaba da zama, wallahi duk wadda ta kwana a gidan nan sai dai gobe taje kwaso kayanta a gidan aurenta".

Ya kalli matarsa ya ce,"ke kuma tashi mu wuce".

Yana fa
ar haka ya fice fuuuu, ni dai nayi ta mamakin inda yaji labarin, amma nafi tunanin Lubabatu ce ta zayyana masa komai.

Da daddare har na fara bacci kiransa ya shigo wayata wai na zo na sameshi, har zan banza da shi kuma dai na fita.

Ina sakkowa naji suna maganar a Abuja za'a
aura auren, wasu za su bi jirgi wasu a mota kuma duk shi ya
auki nauyi, raina na ce an gaida me ku
in duniya, na kya
e ba ki na shige
akin nasa.

Na sameshi yana faman shan
amshi ban wani bi ta kansa ba na haye gado na kwanta, sai can bacci ya fara
aukata naji yana lalubena, yanda ya nuna min yunwarsa dan dole na sallama masa yayi yanda ya so da ni.

Bayan lafawar komai ni na fara wanka kafin shi, ni dai wannan daren shi yay bacci ni ina daga gefensa ina kallonsa, azababben kishinsa mai tsanani naji ya mamaye zuciyata, tunani da lissafi kawai na ke yi akan ta yanda abunda na mallaka tsawon shekaru takwas zai koma mallakinmu mu biyu, shikenan yanzu duk irin salon abubuwan da yake yi min a shimfi
a itama sai yayi mata?

Kuma yanzu yafi sonta akaina?

Na rumtse ido ina jin zuciyata na fa
a min dole in mi
e tsaye don ba zai yiwu na bar mata shi ba.

Da asuba bayan ya dawo daga masallaci ina ji ta kirasa a waya, ina ga da wata lambar ta kirasa don sai bayan ya
aga ne ya ke cewa,"wannan numbern fa ina na ki wayan?". da haka kuma ya tashi ya fice yayin da na ke jin zuciyata kamar zata yi bindiga.

Ya jima kafin ya dawo ciki, kuma sai lokacin ne ma yake kashe wayar don ina ji yana ce mata,"Kishiyar Iyam ce sai Yayyuna biyu da
anwar Malam.

Sai dai mun
araso
in nan da sha
aya jirgin namu zai ta so".

Idona ya cika da ruwan hawaye inda na ke kallon fuskarsa da ke bayyana annurinta. da
yar na mayar da hawayen idona da ke son zubowa, na rufe
ur'anin da na ke karantawa na tashi tare da ninke sallayar duk na mayar da su ma'adanarsu. na zauna gefen gadon ina cewa da shi,"ina kwana".

"Lafiya lau". ya amsa a gajarce.

Tun daga haka ban
ara magana ba, kuma kamar jira ake gari ya waye sai ga kira na ta shigowa wayarsa, ba ya numfasawar minti guda wani kiran zai
ara shigowa, har sai da shima ya fara gajiya da hakan don dama tun daren jiyan na lura a gajiye ya ke sosai.

Fita nayi na bar masa
akin na kama hidimar gyaran gidana, sun yi kaca kaca da falon har
arni yake yi kuma an rasa me gyarawa duk uban
an matan cikinsu, gidan dai tsit ina ga sunji kashedin Yaya Babba sun kama gabansu, cikin
anan lokaci na kimtsa falon na tashe shi da
amshi, kana na koma sama nayi wanka na shirya tsab abina na ci kwalliyata ina ta yin iya
arina wajen basar da lamarin bikin nan, kuma Allah sai ya saka min natsuwa a zuciyata, duk da babu
unshi babu gyaran kai amma fess na fito nayi kyau da ni, ban baro
akina ba sai da na gyara shi na sanya karatun
ur'ani.

Lokacin da na sakko
arfe takwas da rabi, na le
akin ina ce masa,"Zan
ora abinci ne da kai?".

Wani kallo yay min kafin yace,"Da sai kin tambayeni?".

"Yau
in kamawa tayi na tambaya".

"Kiyi duk yanda yay miki".

Kafa
a na
aga na fita, kunun tsamiya na
ora da soyayyar doya babu
wai, ina ga
wan sun cinye shi daga shekaranjiya zuwa jiya, dama kiret uku ne yay saura yana cewa za'a kawo ba'a kawo ba.

Ban
ora da yawa ba, daidai cikina da na Iyam da na yaran ne, yanda na ke ta abuna kamar ba wadda za'ai wa kishiya ba. na zuba doya a flask
in zan kai mata sai ga shi ya shigo kicin
in sanye cikin dakakkiyar shadda fara sai uban
yalli da
aukar ido take yi, an yiwa babbar rigar azababben
inki irin na sarakai, fuskarsa sai fidda annuri yake irin na sabbin angwaye masu
oki,
amshi kuwa la'ila ha'ilallah ban ta
a dai jin
amshi me irin wannan da
in ba.

Kibiyar kishi ta soke ni naji hannayena sun shiga karkarwa, da
yar na iya saita kaina.

Muryarsa a tausashe yace da ni,"Zamu wuce can wajen
aurin auren, a Abuja ne na san kin gani a katin, ban san lokacin da zamu dawo ba amma ba zama zamu yi ba ana
aurawa zamu taho.

Amarya sai gobe za'a kawota, babu wani abu da kika bu
ata zan iya tafiya?".

"Babu komai".

Na fa
a a sanyaye.

"Don Allah Sa'ida kar inji wata fitina. ko Iyam ba wani taro zata yi ba duk
an uwa ne".

Na ce,"fitina ai sai fitinanne, ni da banda matsala da kowa".

Ya ce,"Na tafi to".

Na ce,"Allah ya kiyaye ya tsare hanya, a dawo lafiya".

Ya amsa da amin kana ya juya ya fita ni kuma na rakashi da ido, babu yacca ban ba hawaye karsu zubo min amma ina marayan kuka na saki ina dur
ushewa a kicin
_____________________________________
*(22)*
Ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawa shi ka
ai yasan irin zafi da ra
in da zuciyata ke yi a wannan lokacin.

Haka na ci kukana na gode Allah kafin in mi
e da
yar in wanke fuskata a cikin sink
in kicin, kaina kuwa kamar zai tsage saboda azababben ciwo, ga jikina da ke karkarwa kamar me shirin kwancewa zazza
i.

Abincin da na gama ha
awa na kwasa, sai da na ha
e har da nawa na juye a ciki don sam bana tunanin a yau dai wani abu shi abinci zai shiga cikina, ai ko yawun bakina jinsa na ke tamkar ma
aci.

Ina shiga
akin Iyam na aje mata abincinta, kallo ta bini da shi da mamakinta na ganina fess kamar ba wadda miji ke
ara aure ba, kuma saboda an fi son ganinka a
untatace har ce take to Allah sa ba mugun abu na
ulla ba don ita bata ta
a ganin wacca za'a kishiya na harkokin gabanta ba rai fess a ranar biki.

Na fito ina
wala kiran su Rumana Iyam ta le
o tana shaida min ai da su aka tafi jiya, ta fa
a tana ta
are min kallo gami da
ara cika da mamakina, kicin na koma na aje abincin na su kana na koma
aki, ina shiga kuwa na tarar da wayata na
ara da sauri naje na
auka sai dai ganin sunan da ke kan screen
in yasa ban
aga ba.
_"zan yo hayar
an daba mu zo gobe"._
Maganar ta Safiyya a jiya ta haska min cikin kai, don haka kawai na mayar da wayar na ajiye, na sani Safiyya me matu
ar damuwa da damuwa ta ce, tana kira ne don taji a wanne hali na ke, to sai dai raunin da ke tare da ni ba zai iya
oye halin da zuciyata ke ciki ba wanda ko da na fa
i akasin hakan don
oyewa za'a
aryata ni, kuma ina tsoronta da ta
ara tambayar adireshin gidana don Safiyya na daga cikin mutanen da ke tabbatar da maganarsu idan sun fa
a, ko bata zo da
an daba ba to tabbas zuwanta sai ya haifar da rashin da
i.

Sai bayan kiran ma ya katse na ga ashe tun kusan da na fita ne ta ke kira miscalls goma haka ta bar mini, na shiga message ina duba sa
on da ta turo.
_"Beb na kasa yin breakfast, zuciyata ta
i yarda da cewa Nazifi ne zai yi miki kishiya, don Allah ki
aga kirana ko ki turo min da address na gidanki, yanzu haka ina shirin baro legos nan da awa
aya da mintuna zan shigo kano jirgi zan biyo, kuma don girman Allah ki daina kuka na sanki sarai, am on my way to na zo nayi haukar da zata sa a fasa auren nan yau"._
Girgiza kaina kawai nayi ina sauke numfashi a fili na furta Allah ya sanyaya miki.

Ina kwance nayi nisa cikin tunani Ummani ta kira ni, Allah sarki uwa muryarta kawai ya shaida min cikin damuwa take, bayan mun gama gaisawa ta tambayeni babu dai wata matsala ko na ce mata ehh babu komai har ma na shaida mata masu tada hatsaniyar basa gidan jiya Yaya Babba ya zo duk ya kora su sai dai ban sani ba ko sai anjima za su zo amma dai yanzu daga ni sai Iyam ne sai ba
auye mutum uku da suka zo.
Chapter 44 · 0% Book details