← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 56

Sashe 19

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka na yini a kwance cikin matsananciya damuwa,
angare
aya cike da fargabar dawowar su Yaya haka kuma cike da tsananin tsoron hukuncin da Hubbi zai yanke.
tashi kawai na ke in shan ruwa in koma in kwanta har magariba babu abin da ya shiga cikina sai ruwa, na galabaita sosai ga ciwo ga yunwa ga aman ruwa, kwata kwata na rasa me ya ke min da
in a duniyata, ban isa na tuhumi ubangijina kan jarabawa da
addarar da su ke ta
wallo da ni ba tun aure, sai dai zan ro
e shi da ya bani ikon cinyewa zuwa matakin nasara.
bayan nayi sallar magriba ina zaune jugum, lokacin na kira wayar Hubbi yafi sau goma bai
aga ba duk saboda naji ya jikin Atika, hatta ita Yaya da Iyam sai da na kira su amma babu wanda ya
aga wayata, ban san wanne asibiti ba ne balle na bi bayansu, sai Lubabatu na kira tace min duk suna asibiti itama an barta ne da yara a gida, amma sun yi waya ance jikin da sau
i. ajiyar zuciya na sauke don sai a sannn na sami relief, na kwantar da kaina gefen gado ina jan carbi, cikin tunanin da na ke zuciyata ke fa
a min ya kamata in kira mahaifina mu gaisa don mun kwana biyu bamu yi waya ba.
duk da ina fargabar in kira shi saboda yacca zai saurin gano damuwar da ke kan muryata, haka na daure na danna kiran saboda ko ba komai waya da shi
in zai yaye min damuwar da na ke ciki.
nemo lambarsa nayi, nafi
arfin minti uku ina sa
a da warwara akan in kira ko in fasa, can kawai na danna kiran ya tafi, kamar yanda ya saba duk lokacin da na kira shi yauma hakan ce ta kasance, ya katse kiran nawa sannan ya biyo baya.
da adu'a na samu raunina ya
oye da na
aga wayar nayi sallama.

"Salamu alaikum Abbaa".

"Wa'alaiki salam da ma'aikaciyar lafiya,
ar albarka ya aka yi sa
on zuciyata ya iso gareki da wuri haka, yanzun na ke cewa bara nayi sallar isha'i na kiraki, ina fatan lafiya kike da ke da mai gidan na ki ko?".
wani sanyi ya ratsa ni na farin ciki da jin muryar mahaifina. nayi dakiyar danne kukana na ce,"muna lafiya lau Abbaa, fatan kuma lafiya ku ke?, ya kasuwa?".

"lafiya lau fa Sa'ida, komai lafiya kinji, ba dai ki da wata matsala ko?".
kamar ina gabansa na
aga kai alamar ehh,"babu matsalan komai Abbaa".

"to ma sha Allah haka ake so ai, Allah yayi muku albarka gaba
ayanku, Allah ya
ara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kauda duk wata fitina da sa
ani a tsakaninku, Allah yay miki albarka kinji Sa'ida, Allah ya ba ki nasara da sa'a a rayuwa, mafi alkhairi yay ta bibiyarki. ki tura min lambar akawunt
inki zan saka miki
an abin da ya sawwa
"tom Abbaa na gode, Allah ya
ara arzi
i ya
ara muku lafiya da tsawancin kwana".

"amin ya hayyu ya qayyum, ya makarantar tahfeez
in na ki kuwa, ba dai kya wasa da zuwa ko?".

"ina zuwa Abbaa".

"kema da ke cikin masu saukar ta bana ne?".

"a'a sai wata shekarar Abbaa".

"to Allah ya bada ilimi mai albarka, ki gaida mijin naki. yanxu ina masallaci sai in na koma sai ta kira ki".
har nayi haka zan kashe kiran sunana da yay ya dakatar da ni. na amsa masa sai naji yay shiru, tunanin ko kiran ya yanke ne hakan yasa na kalli screen
in kafin na kuma mayarwa kunne in sake cewa,"hello Abbaa".
ajiyar zuciya naji ya sauke, shiru bai ce komai ba sai can yay nisa ya ce,"kina jina Sa'ida".
na ce,"ehh Abbaa ina ji".
ya ce,"walwala ta burin zuciyar
an Adam tsakanin abubuwa guda biyu take, farin ciki da ba
in ciki. idan abin farin ciki ya ratsa zuciya fuska zata nuna, za ta yi
yalli, zata sake sosai wajen bayyanar da farin cikinta, daga nan kuma murmushi da dariya su ziyarceta. idan kuma ba
in ciki ya ratsata sai tayi ba
i, ta turnu
e, idanu suyi jajur su cika da
walla, idan ya tsananta hawaye su ji
a fuska, murya ta bada labarin yanayin da ake ciki...
ata kar ki manta da wanda kike waya, mahaifinki ne mai iya gane halin da kike ciki ko bai kalle ki ba, Sa'ida saki kukan da kike ta dannewa tun a sallamar farko, yi kukanki yacca kike so ba zan hanaki ba kuma ba zan tuhume ki dalili ba, domin shi kuka hanya ce ta rage ra
in da ke cikin zuciya, sai dai ina so na tuna miki cewa kuka ba ya maganin matsala...yi kukan iyaka iyawarki ina sauraronki".
zuciyata naji ta matse wani abu ya daki
irjina, Abbaa da kansa yau ke bani izinin yin kuka, mutumin da sauyawar yanayina ka
ai ke tada hankalinsa amma yau shi ke ce min nayi kuka iyakar yina, shin ya san matsalar da na ke ciki ne?. lokaci guda dauriyata ta
wace na fashe da matsanancin kuka me ta
a zuciyar duk me saurare, kamar yanda Abbaa ya fa
a sam bai yi
arin hanani ba, bai kashe kiran ba haka bai ce komai ba, sai dai ina jiyo saukar numfashinsa, haka nayi kukana na gode Allah, murya a dusashe na ce,"Abbaa na gama, amma babu wata matsala, dama kukan soyayyarku ne kawai na ke yi".
*(9)*
murmushin manyance naji yayi, bana ganinsa amma ina da tabbacin sai da ya gya
a kai kafin ya ce,"yaro yaro ne". kana ya
ara cewa,"na sani soyayyar da kike mana zata iya sawa ki zubar da hawaye musamman idan kika tuna cewa akwai wani tabbataccen lokaci da dole mutuwa zata raba mu. sai dai ba hakan ne musababbin kukan na ki ba, muryarki kawai ta shaida min akwai matsala, haka ne?".
na rumtse ido nace,"haka ne Abbaa".

"to me yasa za ki
oye min?".

"kayi ha
uri Abbaa".
yay shiru na
an sakanni kafin yay gyaran murya.

"saurare ni da kyau Sa'ida. mu iyayenki ne, babu wanda zai tsaya miki tsayin daka a duniyar nan sama da mu bayan mahallicinki. adu'armu a gareki ka
ai ta isa ta magance miki kowacce matsala da kike ciki, kuma ki sani adu'a na canja
addara". yay amfani da kwantaccen lafazi wajen fa
in hakan.
murya na rawa na amasa,"haka ne Abbaa, ba wai na
oye muku ba ne saboda tunanin ba zaku iya min komai ba, kawai shiga damuwarku akan hakan yasa Abbaa, amma kayi ha
uri Abbaa, adu'arka kawai na ke so".
nayi maganar da muryar kuka ina me share hawayena.

"Sa'ida ni mahaifinki ne, ba lallai sai kin
oye min kina cikin matsala da damuwa ba, muryarki zata bayyana min. ba zan tsaya shiga sha'anin aurenki ba, sai dai ina so na tuna miki duk lokacin da tsananin rayuwa ya dame ki, abu na farko da zai sa ki farin ciki shi ne ki tuna ke musulma ce kuma Masoyiyar Manzon ALLAH [S.A.W].

Duk tsananin da kike ciki ki tuna cewa akwai wanda ya fiki shiga tsanani, Ki tuna cewa kinfi mutane da yawa jin da
in rayuwa. wannan rayuwar tamu ta duniya da kike gani gaba
ayanta jarrabawa ce, Sa'ida aure kan saka mutum ya yi farin ciki a rayuwa sai dai duk tsananin farin ciki ba shi zai hana ma
aurata fuskantar matsaloli ba. ba abin mamaki ba ne idan a wasu lokuta anata fuskantar matsaloli a auratayya, domin rayuwar aure gaba
ayanta ha
uri ce, haka kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan auranta. ko babu komai ki gode Allah da ya baki miji me tsananin sonki da
aunarki gami da tausayinki. ni dai abin da na ke so da ke kar da ki din
a barin damuwa a ranki, hakan zai cutar da ke. kamata yayi duk san da kika kasance cikin halin tsanani, to ki
aura alwala ki fuskanci al
ibla ki gana da ubangijinki, a gaban mahallicinki ya kamata ki zubda tarin hawayenki, ki
askantar da kanki a gabansa kina me ro
onsa cikin kirari da tsarkakewa, shi ya san halin da kike ciki kuma shi zai magance miki. kuma hakan zai sa ki samu rangwamen komai, tun haihuwarki mu ke miki addu'a kuma ba zamu daina ba har mu kai ga kushewa, kuma ina miki al
awarin
ara dagewa akan yi miki adu'a
ata.

Allah bai hanaki don baya sonki ba, bai bawa wasu don yafi sonsu akanki ba, kema yana sonki kuma zai ba ki mafificin alkhairi cikin yardarsa da amincinsa.

Allah yay miki albarka, Allah ya shiga dukkan lamuranki, ya yaye miki dukkan
unci, ya kawo miki salama da natsuwa. ayi ha
uri a
ara ha
uri a kuma ci gaba da ha
uri kinji
ar albarka, ina fa
a miki hakan ba kuma zan fasa fa
a miki ba ko da yaushe; ha
uri, uzuri, kawar da kai da kuma yafiya, ki kamasu tabbas kin kama makaman nasara da farin ciki, Sa'ida wanda ba ya ha
uri ba ya uzuri ba kuma ya yafiya to shi ne ke samun na
asun farin ciki, amma me ha
uri da tawakkali da fawwalawa Allah komai wallahi ba ya tawaya, bayan tsanani sai da
i da izinin Allah".
yay shiru, ni kuma kukana ya
wace, cikin muryar da ta disashe da majina na ce,"na gode Abbaa nah, na gode sosai, ubangiji Allah
ara muku lafiya, yaja min da ranku, yasa kuyi kyakykyawan
arshe".

"amin ya Allah
ar albarka. amma ki daina kukan, ki kuma yi min al
awarin ba za ki
ara ba".

"in sha Allahu Abbaa".

"zan tura miki ku
i sai dai kiyi hakuri babu yawa".
Chapter 19 · 0% Book details