← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 56

Sashe 42

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga tambayar kuma sai ta kama balbale shi da masifa, ai ya barni duk na raina su bana ganinsu da
ima,
arshema rashin mutuncin nawa har ya kai ga kan mahaifiyarsu, shi kuma da bai san darajar uwarsa ba ya bar matarsa na barinta da yunwa, to ko ya
au mataki ko kuma ita ta
auka da kanta.

Shi kuwa cikin girmamawa ya shiga bata ha
uri kana ya juyo gareni nima yace na bata ha
urin, ba don raina ya so ba na ce tayi ha
uri kana suka fita a
akin su ka barmu.

Tun bayan fitarsu ban kalle shi ba na nemi wuri na zauna.

Ina jin kallonsa a jikina wanda na ke hango fuskarsa ta cikin madubi na shaida tsananin
acin ransa.

Can yay nisa ya ce da ni,"me ya hanaki yin girki?".

Kai tsaye na ce,"saboda bana jin yunwa".

"Idan ke ba kya ji
sauran mutanen da ke cikin gidan fa?".

"Wanda nauyin dafa masa ke kaina ma ban dafa na ba shi ba".

"Kina nufin me kenan Sa'ida?".

"Ina nufin mijina ma ban dafa na ba shi ba balle wasu da hakkin ci da su ba a kaina ko na me gidan yake ba, wanda ya damu da yaci ai ya san hanyar kitchen".

"Har da mahaifiyata?".

Nayi shiru ban ce masa komai ba, ya
aga murya da ke shaida
acin ransa ya ce,"tambayarki na ke yi har da mahaifiyata ma sai dai ta shiga ta dafa da kanta?".

Shiru na yi na
i cewa komai.

Yay
wafa yana jijjiga kai kafin ya
auko waya a aljihu, bayan wucewar sakannin da ba su wuce goma ba na ji yana fa
in,"Kiyi ha
uri Hajjo zan takura ki, kamar yanda na fa
a miki ne dai a
azu na kasa yin shiru kan abubuwan da Sa'ida ke min a gidana saboda bana so azo ga matakin da kowa ba zai ji da
insa ba, ta san me ya faru a baya to ina tausaya mata shiyasa ba zan mayar da ita gaban su Kaka ba don har yanzu ta kan hukuncin Abbaa da ya yanke mata na rashin zuwa gida, amma hakan bai sa ta gyara
in ba".

Ai yana cewa Hajjo na zuba masa ido, idan nasa mamaki a matsayin kallon da nake masa tabbas na yiwa kalmar rashin adalci.

"Tom shikenan gata". ya mi
o min wayar na kar
a ina kallon screen
in da ke
auke da sunan Yayar mahaifiyata Hajjo,
irjina ya buga na runtse ido nasa wayar a kunne, ina ga dai hankalinsa ba zai kwanta sai ya shiga tsakanina da kowa nawa tukunna, ita kuma ko me ha
a ya fa
a mata oho, kai Namiji
ayar ruwa baka san da ita ba sai ka taka, kamar yanda ban san da wannan
oyayyan halin na Nazifi ba sai a yanzu da duniya ke gara masa.

Hajjo ta katse Sallamata da ce min,"ke kuma mijinki yay ta kai
ararki hakan kika za
arwa kanki ko Sa'ida?".
______________________________________
*(21)*
Na rumtse ido ina jin zuciyata na bala'in matsewa, muryana a hankali kuma a raunane na ce,"ba haka ba ne Hajjo kiyi min alfarmar tsayawa kiji ta bakina kar ki yanke irin hukuncin su Kaka...".

Murya ta
aga wajen dakatar da ni,"dalla can rufe min baki, wanne irin iskanci ne da rashin sanin darajar iyaye yasa za ki
i dafa abinci ki bawa uwar mijinki, dan ubanki da bata haiifa ba har kya ganshi ki so ki aure, wawiya kawai idan ba ki bi uwar miji ba ta ina za ki kama mijin naki a tafin hannu, ko haka kika ga matan yayyunki na wa mahaifiyarki, ba gida guda su ke ba amma kullum da kwanon abincinta a gidan matar Sa'id.

Kishiya kuma akanki a ka soma? kaf cikin mu biyar da mahaifiyarmu ta haifa wa kike gani tana zaune ita
aya banda mahaifiyarki?

Kuma
an uwanki Samira da Husna duk ba kishiyoyin ne da su ba, kin ta
a zuwa kinga wacca kishiyarta ta zauna akanta?

Ko kin ta
a jin wata cikinsu mijinta ya kai
ararta akan kishiya, sai ke saboda sakarci da shashanci za ki
ata rawarki da tsalle, to ki shiga taitayinki wallahi, kar na
ara jin makamanciyar magana irin haka ta kin hana uwar mijinki abinci, ita kam ko ce tayi ki kwanta tabi ta kanki ki kwanta biyayya dole, Saboda haka yanzu muna gama wayar da ke ki wuce ki girka abinci ki kai mata tare da bata ha
uri kina jina".
aga kai kamar ina gabanta na ce,"zan bi umarninki in yi yacca kika ce in sha Allah".

Sai kuma ta kama yi min fa
a sosai akan rashin bashi hakkinsa da na ke, shi ko kunyar kai mata wannan
arar ma bai yi ba.

Tana fa
an tana ha
awa da aya da hadisi har ta gama kana mu kai sallama da ita bayan ce min da tayi tana tafe nan da anjima zata zo in gwada mata kalar iskancin da nake yi tunda har an iya akai min akwatuna na watso su waje.

Na mi
a masa wayarsa suka ci gaba da magana da ita, ina ji tana ce masa,"kayi ha
uri Nazifi, na dai yi mata fa
a idan taji ta gyara shikenan, idan kuwa bata gyara ba kanta ta yiwa kuma ba kowa ta wula
anta ba sai iyayenta".

Yay mata godiya suka yi sallama, ya fita a
akin na raka shi da kallo, kafin na mi
e cikin karaya wasu zafafan hawaye na sauka akan kuncina yayinda a zuciyata na ke fa
in tsakanina da Nazifi sai Allah ya saka min.

Shayi na dafa na zuba a flask daidai cikin mutum guda, kana na
ora taliya fara dama akwai sauran miya.

Don haka abincin da na ha
a na daidai cikin Iyam ne ita ka
ai, na
eba na kai mata
aki, basu ma san da shigowata ba saboda shewa da hayaniyar da suke yi, can na hango Iyam daga wajen wadrobe
inta
an jikoki sun sakata gaba tana yi musu wasa, na wuce mutanen kan hanyar da babu wanda ya amsa sallamata a cikinsu, na dur
usa har
asa na bata ha
uri bata dai ce da ni komai ba na ta shi na fita bayan na aje mata abincin, ina jin Ummaa na fa
in Allah ya shiryeni yasa kishiya ta koya min hankali, a raina na ce ta dai koya muku.

Da rana ina zaune da waya a hannu, na kunna data na hau whatsapp, da ma ni shi ka
ai na ke dan shi kawai Nazifi ya yarje min in ke yi, babbar wayar ma da
a ya bari na ri
e, Ina cikin kallon status na bu
e na Adamu
aninsa, nan take na yi karo da hoton da ya zamar min yajin albasa a ido.

Hotuna da bidiyo na Nazifi da Amayarsa, irin hotunan nan da ake yi na kafin aure, kasa
auke
wayar idona nayi akai, kyan da suka yi ko hasidin iza hasadun, shi ya saka yadi me tsada ita kuma cikin wata doguwar riga ta net, kana ganinta ka ga jinin shuwa, hanci kaman tsinin biro ga ido da gashin ido masha'Allah, ba
arya tana da kyau iyakar kyau irin kyan da namiji ba zai gani ya
yale ba, wata
ila kuma wannan kyan shi ya ru
e shi domin a rayuwarsa yana matu
ar son kyakykyawar mace. da gani ta girmeni kam zata iya ba ni shekaru uku, idonta ka
ai zai shaida maka a waye take kuma tasha boko kamar yanda ya fa
a, ban san lokacin da na jefar da wayata ba ganin yacca a bidiyon yake faman ru
ota zuwa jikinsa ita kuma har tana kwantar da kai a
irjinsa.

Kaina na jinginar jikin gado ina hawaye sosai.

Tsawon wani lokaci wayata tayi
ara na
auko, sabuwar lamba na gani a jiki, muryata na saita kana na
aga tare da yin sallama.

Daga can
angaren aka ce,"Ke Sauna ba hoton mijinki da wata na ke gani ba yana yawo a IG?".

Muryar kawai ta shaida min wacece, kuma sosai nayi farin ciki da kiran nata, Safiyya ce
awata ta
ud da
ud tun aji
aya a makarantar boko, ita ka
ai ce wadda yau zan nuna in kirata da sunan
awa, ina sonta fiye da yanda take sona kamar yanda itama ke cewa tana sona fiye da yanda na ke sonta, rabona da ita kusan shekara uku da rabi kenan da Babansu Allah ya
aga shi gwamnati ta ba shi matsayi suka koma Abuja da zama.

"Hello Beb".

Na murmusa kuncina ka
an murya a sanyaye na ce,"Na'am Beb".

Ta sauke numfashi da cewar,"ohh i thought i was mistaken in ce wa kuma zan
ara nema ya ban numbernki...hey tukunna ma are you well naji muryanki somehow cool".

Na ce,"Safiyya natsu muyi waya da kyau mana har yanzu kina nan yanda kike, kuma ni ki min hausa zalla ki daina ha
a min da turancinki tunda kin zama baturiya".

Tayi dariya sosai kana tace,"To matar Ustaz ai ni ban iya larabci ba balle nayi miki.

Beb ba fa ki da mutunci wallahi, kinga wahalan da na sha before i gat your number, i so much missed you almost four years.

Bamu da zumunci gaba
ayanmu mun zama wasu
an banza".

Na ce,"ai ni ina gwada lambarki bana samu".

"Eyyah that number ai ba yayi, tun da naje saudiya na jefar da layin shikenan nima sai na rasa na ki, ba yanda ban yi ba wajen in sameki na rasa, in ta shiga kafafen sadarwa ina searching sunanki bana gani, ke har yanzu kina nan da duhun kai".

Da murmushi nace,"Yanzu ai na kika samo lamban nawa?".

"Akwai wata something Tijjani oho that fat girl dai da ta nace miki na tsaneta, sai da na
auke numfashi aka rirri
eni kana na iya kiranta fa na ce ta bani lambanki, itama numban nata wurin Uncle Maths na samu kin san Yayanta ne, Beb ina kishinki sosai".

"Hmm Allah ya shirya min ke. yanzu dai mu gaisa ina Baba da Mama?".
Chapter 42 · 0% Book details