← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 56

Sashe 49

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa mun ha
u sau biyu ranar ina kicin ta shigo muka gaisa da fara'arta, tayi min sannu da aiki tana cewa zata tayani na ce mata a'a ba na saka amarya aiki ba ta bari ta gama shan amarcinta, ta
i tafiya ta zauna muna hira da ita jefi jefi babu laifi dai tana da kirki a yanda na fahimta duk da ba lokaci guda ake gane halin mutum ba, har da cewarta yanayina na burgeta ita kam, sai kuma take tambayana ya yanayin cin abinci a gidan ya ke saboda ta san yanda zata tsara lokacinta, hutun sati biyu aka bata a wurin aiki ga shi aikinsu fitar
arfe bakwai ne kuma sai hu
u ta ke baro office, na fa
a mata duk lokacin da na ke girkina ta jinjina kai cikin harshen turanci tayi wata magana da ban shaida me tace ba haka kuma ban nuna mata ban gane me tace ba
Rana ta biyu kuwa da ta yini a
akin Iyam ranar ina yiwa Iyam gugar kaya, suna ta hira da ita akan wata mata da ita Zahra'un tace tana yi musu aiki ita kuma Iyam na cewa ai
ar garinsu ce, shine har ta
auko dutsen gugarta ta zo muka
arasa gugar tare duk da Iyam na ta ce mata ta
yale mini na yi amma tace babu damuwa taga ai na sha aiki.

Haka dai rayuwar taci gaba da tafiyar min zaman gidan Nazifi ha
uri kawai na ke yi domin ba da
insa na ke ji ba, duk wasu ayyuka da
awainiyar masu zama
ashinsa ni ce, idan na yi kuma kullum a ban iya ba nake a wajen Iyam, wula
anci kuwa ban fasa shansa ba sai wanda ya
aru ita ta min
an uwan idan sun zo suyi min duk da sun rage zuwa yanzu ina ga ko sun bari a gama cin amarci ne.

Yawan kuka da sanya damuwa a rai kawai na ragewa kaina saboda gudun kamuwa da wani ciwon, amma ha
urin duk da na ke kam ina yinsa ne saboda abu guda biyu zuwa uku, na farko ina tunawa da rantsuwar Kaka na cewa idan har na fito to ba zan zauna a gida ba sai in ya mutu, da kuma tunanin shin idan auren ya mutu to wa zai auri bazawara irina wacce ke da na
asun haihuwa?

Kuma idan ma auren zan yi wanne kalar mijin zan
ara aura? don ni tun daga kan Nazifi na sare da duk wani namiji da ita kanta rayuwar auren, ga mahaifiyata da na ke ta son gani amma har wa yanzu Abbaa bai sauka akan bakansa ba.

Ranar cikar sati guda da yamma lis ina
aki muna chart da Safiyya, Nazifi ya shigo, shigowar tasa kuma ta matu
ar bani mamaki da
aure kai gami da tunanin me ya kawo shi, domin rabonsa da
akina yau kwana biyar, ni sai naji gabana ma ya fa
i da zuwan nasa.

Na gaida shi ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, ya ce na tashi na
auko masa kujerar madubi zai zauna, na bisa da kallo na
an sakanni kamar dai lamarinsa babu lafiya ko kuma yana rashin lafiyar rabuwa da amaryarsa ne oho, na
auko na ajiye masa ya zauna ni kuma na ci gaba da danna wayata.

Tsakanin mata da miji sai Allah, duk irin yanda na ke matu
ar jin haushinsa da fushi da shi sai yanayin shirun nasa ya dame ni duk da hakan ba sabon abu ba ne, to amma yanayin yanda ya sakani a gaba ne kamar akwai damuwa babba, wani abu da na tuna yasa na
ago na dubesa na ce,"Baka da lafiya ne?".

Na tambaya cike da tsantsar kulawa har ina kai hannu na ta
a wuyansa sai dai naji jikin nasa sanyi
alau.

Ya ce,"Lafiya lau na ke.

Ya
arinki? na gode".

A hankali na ce,"babu godiya a tsakaninmu.

Amma sai dai ban yarda da babu komai
in ba, ka fa
a min don Allah akwai wata damuwar ne?".

Sai da ya gama
an kamekamensa kana ya ce,"ina so zamu yi magana ne da ke sai dai ban san ta yanda za ki kar
eta ba".

Ina kallonsa sosai da nazari nace,"ka fa
a kanka tsaye ba matsala zan fahimce ka".

Zamansa ya sake gyarawa kana ya mi
o min ba
ar leda nasa hannu na kar
a. na bu
e ledar idona ya sauka akan bandir
in ku
an dubu dubu sabbi masu uban yawa, na
aga kai na kalle shi ina jiran
arin bayani.

Ya murza hannunsa kafin ya ce,"Zahra'u ce bata da lafiya don yauma a asibiti mu ka yini, to likita dai yace tana da bu
atar kulawa, kinga
an uwanta duk ba anan su ke ba balle a samu wanda zai zo ya zauna da ita.

Na san ba ki da matsala Sa'ida shiyasa na ce zamu yi magana da ke ta fahimta ki fa
i farashin da za ki siyar min da kwanakinki na tsawon lokacin da zata ji sau
Yay shiru yana kallona, ni kam har ya gama maganarsa kallonsa kawai na ke yi idona waje tamkar za su fa
o, yayin da a wannan lokacin hawaye sun gama wanke min fuska.

Murmushi na yi me ciwo sai dai daga ni har shi zamu iya rantsewa tunda muke tare da juna irin wannan murmushin bai ta
a fita a fuskata ba, cikin wani irin murya da ban san ina da shi ba na ce,"uhmm sai kuma me?".

Na fa
a ina ha
iye
ullutun wani abu me masifar
aci.

"Nan dubu
ari biyar ne, idan kinga kina da bu
atar
ari ki fa
a ko nawa ne a shirye na ke da na
ara miki muddin kin amincewa bu
atar da na zo miki da ita".

Na ka
u da maganar Nazifi sosai, na rasa me zan ma ce da shi kamar yanda na rasa a wanne sahu zan sanya Nazifi, tunani na ke anya kuwa Nazifi cikin hankalinsa ya ke?

Me ya ke nufi da wannan maganar da ya zo min da ita?

Idan ni ce bai bu
ata mene dalilin da yasa yake zaman dole da ni?

Ina tarin ilimin addinin da na sani a
on kan Nazifi?

Dukkan tunanina ya tsaya cak lokacin da Atika ta fa
akin tana haki,
ago idona itama Rumana ta shigo kamar an jefota, kafin nayi tambayar lafiya saboda yanayinsu da ke shaida akwai matsala, sai ji nayi Atika na cewa da shi,"Abba ka je Iyam ta fa
i".

Maganar Rumana ta kutsa cikin tata itama tana cewa,"Abba Anti Amarya ce ta mari Anti Fati kuma Iyam taje wucewa hannun Anti Amarya ya bigeta ta fa
i a
asa tana can ta kasa tashi, Abba ka taso da sauri Anti Fati tana cewa sai sun yi rigima da Anti Amarya ita kuma Anti Amarya ta ce sai ta faffasa mata baki".

Da saurinsa ya mi
e ya fita yaran suka mara masa baya, ni dai idona ya ma
ale akan
ofar
akin ina tunanin na tashi na bi bayansu ko nayi zamana?.

Zuciyata ta hane ni da tashi na fita, na zauna cikin girgizar lamarin da Nazifi ya zo min da shi, siyan kwanana! bai damu da nawa hakkin ba!

Jiyo sautin muryar Zahra'u a sama na mi
e na fita, har zan sauka na fasa na le
a ta saman ina kallonsu. ta na tsaye tasa hannu ta matse bakin Fati wacce ke tsaye a gabanta tana faman matsutsun
wacewa.

Shi kuma yana tambayar ba'asin abin da ya faru.

Ran Zahra'un a
ace babu sau
i ta ce,"Honey wa
anna irin gidadawan mutane ka ke bari suna shigo maka gida anyhow?

Kawai fa na sakko ne zan je wurin Iyam sai na isketa bisa gaban dining tana bu
e flask na abinci, to ni ban san wacece ba tunda ban san face
in nata ba dalilin da yasa na dakata na iskota ina tambayanta, daga tambaya kuma saboda fitsararriya ce unguwar zoma bata mata gashin baki ba shine take da zarran yi min tsaki tana fa
in na raina mata hankali, Honey can you just imagine
anwata ta kusan hu
u na min tsaki?

Impossible i must teach her a lesson ba na tolerating raini ko ka
an".

Iyam wadda ta mi
e da
yar ta ce,"To Zahra'u yi ha
uri ki cikata ai rashin sani ne. kinga kwana biyu bata gidan shiyasa ba ki shaidata ba Amma daga yanzu ki shaida fuskarta
anwarki ce ita ce
ar Autata, nan take tare da mu ai, ranar biki ne ta koma can gida".

Iyam na yin shiru Zahra'u ta ka
a kai tace,"Am so sorry to say Iyam amma wannan ba magana kika yi me kyau ba, ba hanyar gyara kuma a ciki, kamata yay ki dubeta kiyi mata fa
a kice ta bani ha
uri before then na saketa, amma ba in
yaleta ba gobe taji da
in repeating ma wani, ban sani ba ko halinta ne haka kuma wata
ila tana yiwa matar gidan tana
auka sai dai ni ba me
auka ba ce".

Sai tayi shiru tana mayar da kallonta ga Fatin ta ce,"yanzu za ki iyama Yayanki Nazifi tsakin da kika min ko za ki iya yiwa Maijidda(Yaya)?

To ki sani ba sa'arki ba ce ni, ke imfact ko da shekaru guda muke da ke tunda har Yayanki ya auro ni na wuci ki min rashin kunya biyayyarki dole garen".
yasta yatsu da
ara cewa,"And just for today zan
aga miki
afa amma for the next time idan kika
ara wallahi sai na sa
a miki kamanni".

Ta saki bakin Fatin da ke aikin zare ido don da alama ru
on bakin da aka mata ba na da
i ba ne.

Kana ta koma ga Nazifin tana ce masa,"you just kept silent ka
i cewa komai.

Anyway ka garga
anwarka, idan ma akwai wasu irinta to ka tara su kaja musu kunne, ba
ar iska ka auro ba so they have to respect me kaman yanda su ke respecting na ka.

Kuma zai fi kyau ku yi shari'a da wadda tayi muku rainonta domin bata yi mata tarbiya me kyau ba ta cuceku".
Chapter 49 · 0% Book details