← Book details Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 56

Sashe 5

Kayar Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin in kira office
insa yazo min, sai dai ko da na kira aka tabbatar min da cewa ai tun biyar ya bar office. nan fa hankalina ya tashi, na rasa wa zan kira tun da shi ba wasu abokai gare shi ba, haka yake kamar mace mara son
awaye.
laluben lambar
aninsa na shiga yi, ko da ya
aga bamu wani tsaya gaisawa ba na tambayi ko Hubbi yaje gida, yace ba ya gidan tun da rana da yazo gaida Iyam. muna gama wayar na
ara gwada kiransa, wani sanyi naji a raina da ta fara ringing, sai da nayi kira har sau goma bai
aga ba sai daga ba ya message
insa ya shigo.

"Ba na son damu akwai abin da nake yi".
abin da ya rubuto min kenan, kuma ina gama karantawa na aje wayar jiki a sanyaye, ko ba komai naji dama-dama tun da lafiya yake, sai dai naji babu da
i sosai, domin kamata yay ace in akwai adalci ya
aga wayan ya fa
a min uzurinsa, ko kuma ya rubuta min idan babu daman
aga wayar, amma saboda rashin sanin hakkina da girmama aure yana can lafiya ya barni anan cikin damuwa da tashin hankalin halin da yake ciki, ko abinci na kasa ci haka cikina yake fayau tun ruwan safe da na sha.
gudun tunanin da ka iya rufe ni na mi
e na kwanta akan gadon.

Sai dai me? daga kwanciyar tawa na saki marayan kukan da nayi ta dauriyar ri
ewa tun tafiyar Yaya, sautin kukan ya cika
akin, kuka nake kamar wadda aka yowa aiken mutuwa don kawai in samu in fitar da ba
in cikin da ke raina. na janyo filo na toshe bakina da shi amma duk da haka sautin kukana bai
uya ba.

Lokaci
aya jikina ya
auki zafi na kama kyarma dama ni ban iya zazza
i ba.

A wannan lokacin duk wani mai imani ya ganni sai zuciyarsa ta motsa da tausayina.

Haka na ke ta faman zubar da hawaye, ban isa na goge su ba don ina gogewa wasu na sakkowa.

Na da
e ina kuka don har wajen sha
aya da rabi, zuwa wannan lokacin kam na fidda ran dawowar Hubbi, banga alamun yau zai kwana a gidan ba. saboda haka na mi
e na shiga ban
aki na wanko fuskata ina hana kaina ci gaba da kukan da baida amfani gare ni, adu'a maganin annoba ita ya kamata in ri
e ba wai damuwa da kuka ba.

Ina fitowa na wuce nasa key na kulle
ofa duk da zuciyata na fa
a min komin dare zai dawo, bai da wani wajen kwana a daren nan sama da nan
in dai da yake
auracewa, tsakin
asan ma
oshi nayi, to ina ruwana da dawowarsa, raina
ace na fita falo na bi duk
ofofi shigowa na saka musu ma
ulli, zanga ta in da zai shigo, ai sai dai yay kwanan
akin mai gadi, ba abar banza ba ce ni, auroni yay don yana so ba cusa masa aka yi ba, kuma a gidan iyayena ya
auko ni ba gidan marayu ba. kamar ma in koma
akina amma sai na dawo
akin nasa,
na murza key na kashe fitila me haske na bar mara hasken wacce ke kan durowar gefen gado.

Bacci nake ta so nayi amma gaba
aya na kasa, sai juyi da nake ta faman yi, zuciyata kuma cike da sa
e sa
e, kaina kuwa ya cika fal da tunani daban daban.

Ni dai lafiya
alau muke da mijina, sai dai tun bayan dawowarmu nan gidan da wata bai fi biyar ba komai ya canja na daga yanda muka saba rayuwa, ni da shi kamar abokai haka muke, amma yanzu ya zamar min wani horo har tsoronsa nake yi, magana ma shakkar masa na ke, komai nayi ban iya ba, sa
anin a baya duk abin da nayi ko da bai masa ba zai yaba min kuma yace nafi kowacce mace iyawa, yanzu abu ka
an zan yi ya zama laifi, zama da shi ban isa ba in ba haka ba ya din
unci kenan ni kuma bana son
uncinsa, hatta makarantar tahfeez
in da nake zuwa yanzu nema yake ya kashe zuwanta, don duk san da zan tafi sai yayi
orafi akai, sai yace ai tunda na iya karatun sallah na san wankan tsarki na kuma san zaman aure ya ishe ni, da nayi magana sai yace ai shi ke biyan ku
in ba wani ba saboda haka yana da ikon ya hana zuwan.

Na kau da tunanin matsalata da mijina, na koma tunanin furucin Yaya na za su sa ya
ara aure, tabbas na sani
arin aurensa tozarcin da nake sha sai ya ninku, don sai na
wammaci ina ma ban auresa ba, Allah
aya ya san irin wula
ancin da matarsa zata dinga min, balle ta san don manufar da aka aurota, zata goranta min fiye da yanda dangin miji za su min, kuma daga zarar ance ta sami ciki ta haihu shikenan tawa ta
are, zaman auren sai ya ishe ni, takaicin da zan sha ba daga wurinta ba ka
ai har da shi uban gayyar. ni kaina na sani Hubbi yayi
ari, ba kowanne namiji ne za'a kai wannan lokacin ace bai yi
orafi ba, kamar yanda Yaya ta fa
a shekara takwas ban ta
atan wata ba balle azo ga maganar
ari, kuma ko da wasa Hubbi bai ta
a min magana ba, balle ya nuna min damuwarsa ko
orafi, ni ce
in ma na ke damuwa, don sau tari har kuka na kan yi, sai yay ta min nasiha yana
ara fa
a min lokaci da rabo ne, idan na
ata masa rai akan nuna masa kar a fara cewa bana haihuwa ya din
i fa
a kenan, yace min duk wanda ya fasa fa
ar hakan ba ya
aunar Allah, kai duk wanda ma yay min gorin haihuwa in sanar masa hukuma ce zata raba su, watarana kuwa da nace masa muje asibiti a duba ni bai ci abincina ba. yanzu kuwa yanda muke zaman babu da
i da shi ai nayi ka
an in kai masa
arar Yaya akan cin mutuncin da tazo ta min, kuma ko da ace shima wannan ne dalilin samun matsalarmu ba zanga laifinsa ba, a yanzu kam yana da bu
atar magajinsa, wanda zai
ora akan kasuwancinsa ya kuma mallakawa kadarorinsa. sai dai fa ya tuna ana barin halak don kunya, ko mai zai yi min banda wula
anci, don ni na sha gaban ya wula
anta ni a rayuwa, domin na masa abin da ko
an uwansa basu masa ba, ya kuma san hakan, sai dai in ya butulce, kuma shi butulci dama ai ba sabon abu ba ne a wajen
an adam musamman wanda ka yiwa rana.

Haka dai a wannan dare nayi ta tunane tunane, in raya wancan in sa
a wancan, in lissafa wancan, sai dai na kasa warware komai, haka duk na
osa gari ya waye, ni ba sallah ba balle in yi nafilfili, a haka dai har
arawon bacci ya
auke ni a lokacin da ban san ko
arfe nawa ba.
*(3)*
Washegari ban farka ba sai wajen
arfe tara da rabi na safe dalilin bacci da wuri da ban samu nayi ba, sai dai Alhamdulillahi isassan baccin da na samu yau
in da ya kaini har wannan lokacin sai ya zamana ban tashi da ciwon kai da zazza
i kamar yanda na saba tashi da su ba a
an kwanakin nan.

Sai da na gyara
akinsa tukunna na fita na wuce
akina, kafin na haura saman kuma sai da na tsaya na bu
ofa saboda zuwan mai yi min wanke wanke da share share.

Ko da nayi wanka na ke shiryawa zuciyata cike take fal da matu
ar mamaki gami da sa
e-sa
e daban daban akan al'ammarin nan mai girman gaske, yo mai girman gaske mana tunda miji bai kwana a gida ba bayan ba tafiya yayi ba, kuma abin da bai ta
a faruwa ba tsawon shekaru.

Har yanzu
arfe goma sha
aya da na ke muku wannan maganar banga alamun Hubbi ya dawo gidan ba, na le
a farfajiyar gidan babu motar da ya fita da ita.

Nauyayyan numfashi na sauke, tarin tambayoyin da ke kaina a game da inda ya kwana da rashin dawowarsa da abin da ya tsaresa suna da yawan da har suke neman fasa min kai.

Wayata da ke ajiye kan madubi na
auka zan kira wayarsa, ina bu
eta kuwa na fara cin karo da sa
onsa na jiya da yake fa
a min ba ya son damu.

Da sauri kuwa na dire wayar ina kulle idona kafin na bu
e bayan wucewar da
aya. zuciyata cike da
unci na fita a
aki na sauka
asa, a falo na tarar da mai aiki tana goge gogen gilasai, wanda tuni ta gama shara, ko'ina ya
amshi, dama ni
in gwanar
amshi baka ta
a zuwa ka riski gidana ba ya tashin
amashi tun daga harabar waje.

Muka gaisa da ita na wuce kitchen, ruwan shayi na dafa na soya
wai, na zubo nawa na barwa mai aiki nata, falon na dawo na zauna na kunna tv, ina shan shayin ina kallo hankali da tunanina kuma na can wani wajen.

Motsin bu
ofa yasa na juya kaina wurin, Hubbi na gani ya shigo yanayinsa kamar tashin bom, ko inda na ke zaune bai kalla ba yay wucewarsa sama fuuuu kai kace tashin iska, ni kuwa nabi bayansa da kallo zuciyata na zullo, kamar in share shi amma sai naji ba zan iya ba, lokaci
aya naji abin da nake ci ya fita akaina, hakan yasa na dire na mi
e nabi bayansa da sassarfa.

Ina shiga
akin na tarar har ya shiga ban
aki, nayi tsaye bakin wadrobe kamar munafuka
irjina sai bugawa yake saboda bala'in tsoron da ban san ta ina ya zo ba, wucewar wasu mintuna na dawo hayyacina na bu
e wadrobe
in na kwaso masa kayan da zai saka na zaman gida, na ajiye anan gefen gado, duk wani abu da na san zai bu
ata na
auko na ajiye masa.
Chapter 5 · 0% Book details