← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 87 OF 89

Sashe 87

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read

gareta don bata kusa da gida haka yasa ba a sanin halin da suke ciki da mijin ta can. Sai ni dake kusa ake sanin nawa din kowa ke magana sai dai ko may ye ita ta fini dama gaskiya sosai. Don ko ba komai ba aganin ta a gane don tana da yan suturorin ta na rufin asiri sai dai ba yanda mutum zaiyi tsamani bane. Sannu sannu abubuwa suka fara rikice min na rayuwa na ramay na lalace duk na fita cikin hayaci banda komai kuma kowa ya sani aka kawo ido aka samun a hakan nake rayuwa. Don an san ban son maganan da za a soki Jamil a gaba haka yasa haushina a rayukan yan uwa ya kara karuwa sai baba kabir me mai dan taimaka min wani lokaci can ba a rasa ba. Sai kuma anty daga dan muna hade hade idan naje gidan taga irin yanayin da nake ciki nida yara na idan zan dawo sai ta dan hada min abubuwa kamar yadda iyayye mata ke yiwa diyan su wani lokaci. Ranan kwatsan sai gashi da yammaci ya dawo min yanayin shi kawai na kalla nasan ba dawowan arziki yayi min ba a lokacin. Bayan ya huta yai wanka yaci abinci ya kwanta yayi barci da ya taso ne yake ban labarin wai tafiya bai mai dadi ba yasa muka jishi shiru haka. Don wanda suke sana, a tare ne ya gudu mai da kudi kasan mali da sunan zai tafi can ya saro masu kifi ashe gudu yayi da kudin sunje can kasan ance dasu baizo nan ba. Nan dai ya shiga bani labarin karya ina taya shi zagin mutumin tare da bashi hakkuri kan abinda ya samay shi din. Don sai ka rantse da Allah hakan daya tsara gaskiyane abin ya faru dashi ne a yadda ya tsara maganan nasa. Haka na koma nike laluran komai a gidan wahalce dani sai dai yayi wanka ya saka kaya ya feshe jikin shi da turare da komai ritse baya rasa su ya fice yawo sai dare zai dawo gida. Sai jefi jefi nake samu ya dan yo cefane a gidan duk wanan bai damuna idan dai zamu zauna lafiya a gidan dashi wanan bai damuna. Sai dai mutane suji min haushin abinda yake min din nikan ko a jikina waini mai zaman auren hakkuri sai dai ga nawa wautan banyi tsamanin mutane suna fahintar halin da muke ciki ba dashi. Na manta cewa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba komai da kakeyi akan idon mutane yake ban san may ya hada shi da yar hayan nan bahausa ba. Sai ji nayi yana fadin ya kamata matar nan tabar gidan nan ita ma don halin ta baida kyau wallahi. Sai kuma bayan ya fita ita kuma naji tana jinini wai haka kawai mutum zai lalata mata yara don iskanci ta kyale shi. Nake tambayan da ita dawa ke fada kuma don muna dan shiri a lokacin takw ce min barni da dan iska ko waye ai yasan kanshi don wallahi sai na tona mashi asiri zai bari. Tun lokacin nasha jinin jikina da Jamil ne saboda shima yayi min maganan ta kan ta bargidan bata da hali mai kyau zata iya kashe mai yara saboda bakin halin ta ko ta illanta ni nikaina idan bai gari. Ai sai na dauki fushi da ita tun jin hakan da tace min nace bazatai ma mijina sheri in shirya da itaba niko. Har ya gama zaman garin da yake damu don bai dade ba yace zai koma don zaman gari ba nasa bane nan dai ya tafi ya barmu muna rikici da wanan matar. Rashin shi gida bai sa mun shirya da ita ba har wani lokaci ranan kan yar karamar ya ta mukai fada abunda take so ke nan ta fada min abinda ke ranta. Naji cewa wai Jamil yana kokarin bata mata yaranta yan mata dake gabanta bayan ya nemay ta ita bai samay ta ba ya koma ga yaranta. Wanan maganan da tai min ya bata min rai sosai don ban dauka Jamil din zai iya mata haka ba matar da ta haifi ganda gandan yan mata kamar ta mai Jamil din zai nema a gurin tayi kuma. Na hau fada nace sai ta bar min gida na tunda sherin ta yakai har ga mijina kuma yanzu. Yanzu tace ba zata tashi ba sai mijin ta ya dawo kuma ko ya dawo din sai kudin su na shakara ya kare zasu tashi min gida.
Chapter 87 · 0% Book details