← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 50 OF 89

Sashe 50

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Tun wanan ranan da muka dawo daga Jamil har iyayyen shi ban kara gane kan su ba a gidan kowa zafi zafi yake dani a gidan har Jamil din kan shi ba wani maganan girma da arzikin dake hada mu dashi inji sanyi. Daki nake kwance da yar diyana anyi ruwan sama an dauke a lokacin misalin karfe goma na safe na ranan laraba hayaniya nake ji na mutanen gidan mu sama sama yasa na mike na fito don in ganewa idona abinda ke faruwa. Na samu data daga cikin matan hanyan gidan mu ne suke fitina sai dai ban san da wanda take fadan ba a lokacin maimakon in tsaya sauraren ta in gane kan maganan sai kawai na shiga aiki abina don lokacin dora girki na yayi kusa. Wanke wanke na tara don in yi sai da na hada kayan a gurin da muke zama mu wanke kayan mu na koma daki in dauko omo da zanyi amfani dashi gurin wanke kayan na fito naji matar na fadin mu za aiwa burgan aiki ana muna kurin ana da arziki babu kwarjini ga miji. Tambayan ta nayi wai yau waya taba ki ne haka da wanan sanyin haka ta wani kallo ni shekeke tare da fadin wai ke baki ma san da wanda nake fada ba ke nan ? Kai na girgiza mata ba tare da niyar yin hakan ba a gare ta take fadin amma ke kin kai yar rainin hankali wallahi to dake da mijin ki nake fada ba da kowa ba. A cikin mamaki nake fadin nidin nan kuma may mukai maki haka mai zafi da zaki tashi damu a rai haka da sanyin safiyan nan naga tun asuba dana fito hadari ya kora mu daki ban kara fitowa ba sai yanzu. Zaki ce hakan mana tunda kun san abinda kuka kulla min tun jiya din to bari kiji ni ba irin ki bane da miji ya mayar wata bi can don nasan ciwon kaina dana iyayyena da kuma darajan aure na. Tsaye nayi galala ina son jin inda wanan maganan nata ya nufa akan mu haka da take ta faman budan baki har makwabta zasu iya jin mu a lokacin. Ganin ban fahince ta ba ta buda baki tana fadin kina nufin baki san da zaman mijin ki ya fara jan baban Ahmed zuwa wurin shiririnta shi ba har tsakiyan dare jiya baban Ahmed bai dawo ba gidan nan. Ni ba yar rakiyan mata nake ba da zan saka ido wanan abin yana gudana a tsakanin su haka a zafafe nace wai ko kina da hankali maman Ahmed may ye nawa yanzu ni a cikin wanan zancen. Tace keko keda ruwa a wanan zancen don haka kiwa mijin ki kashedi akan mijina don zan debe kunyan da nake ji nasa in masa rashin mutunci yanzu a gidan nan idan bai fita harkata ba. Sale salin ya fara koya mai neman kannen da yan uwan matan gidan nan ke nan don shi ba abin kunya bane a gurin shi yin hakan. Nace na gane dai dani kike jin fada ba da baban Amira ba don shi bai gidan bai san kina yi ba ma san nan kuma yar uwar wace daga cikin mu kika ga baban Amira yana nema. Kafin ta bani amsa sai ga dayan ta fito daga daki tana fadin dama nasan dani kike wanan maganganun naki ai don ki fada mata mijin ta yana neman yar uwar tagwaici na ko. To ko taji may zatayi tunda shi yaje ba ita taje neman shi ba idona na ne naji ya rufe ga maganganun da suke yaba min dukkan su su biyu din a lokacin. Na rasa abinda zance kan zancen don raina yakai kololuwar baci da maganan su duk kokarin da nakeyi inga na kaice ma wani fitina dasu hakan bai yuyu ba sai da Jamil yayi sanadin hada ni fitina dasu a gidan nan . Kafin inyi yunkurin basu amsa sai ga sarakuwana ta fito daga dakin su tana fadin nasan dama wanan magana da kuke tun asuba da wata manufa kuke yin shi don ku tayar da zaune tsaye a gidan nan tsakanin yaran nan biyu ne. Idan ma ya nema mace nawa aka halasta wa namiji ya nema a rayuwan shi yayi idan ma har kun fada mata din taji za ta hanashi kara abinda Allah yace yayi ne ke da kike fadan yana jan mijin ki zai koya mai yawon banza daure shi yayi a kafan shi ko may ? Wanke wanke nakeyi ina jin raina yana min zafi nan dai sukai ta sa insa a tsakanin su ban iya tanka masu ba don mijina nane yaja min haka a gurin su din. Da ya kama kan shi da mutuncin shi kamar yadda sauran mazan gidan suka kama da duk wanan abin bai faru haka ba a yanzu har ana kokarin fada min magana a kan shi. Na gama na shiga daki sai naji ba zan iya zama ba na fakaici idon mutane na nufi gidan mu hankali a tashe dani na isa gidan kowa ya ganni yasan ba lafiya nake ba. Ban samu anty gida ba tana gurin aiki sai mama uwar gidan baba kabiru na sama a gidan da ita muka fara zancen abinda ke damuna kafin anty ta dawo daga gurin aiki da ta tafi. Muna kan zancen ne ta dawo ta samay ni a gidan da mamaki take kallona don tasan ban faye shigowa gidan haka da rana ba sai da dare nafi zuwa gaida su. Bayan mun gaisa ne take tambaya na ko lafiya a yadda ta samay ni naci kuka har na gaji nan mama ke fada mata abinda ke faruwa a gidan namu. Allah ya sauwaka tace min wanda ni ba haka naso naji daga gare su ba so nayi su goya min baya akan maganan sai kuma ba wace ta furta komai daga hakan sai cewa da sukayi a bari baban mu ya shigo gidan. Wanda ni naji haushin hakan sosai a raina don haka na dauka ko baba yazo shima abinda zai fada min ke nan bayan wanan. Na dora hannu a kai na fara rusa masu kuka a gidan cikin tashin hankali duk na daga masu hankali sosai a gidan ba, a fi minti talatin ba baba kabiru ya dawo gida. Tun daga kofa yake tambayan may ke faruwa ne a gidan nan dai anty ke fada mai maganan dana zo dashi gida kai ya gyada kawai tare da fadin abinda kowa ya guje maki ke nan tun farko. Kika nuna don bamu haife ki bane yasa bamu son abinda kike so din yanzu sai ki koma kiyi hakkuri zan ganshi in masa magana daga baya. Ba haka naso ji daga gurin baba kabiru din ba naso ya goya min baya ne akan maganan sai kuma ban samu haka din ba a gurin shi haka yasa na kara kargin kukana a lokacin. Anty tace hadiza wa zai furta wani kalami mara kyau akan mijin ki idan zuciyar ki tayi sanyi ki kwashe ki fada mai babu abinda zamuce sai hakkuri da zamu baki a yanzu. Raina ya kara baci sosai baba yace wanan yaron ba yaron kirki bane sam ni dake fita a garin nan nasan ko waye Jamil don bai aje kanshi a kusa ba. Baya hali irin na diyan tallakawa sai na diyan attajirai masu hali zaka dauka dan wani gwauna ne ko minister shi yaya ko mai wanan halin za a rabashi da neman mata. Tun farko abinda hajiya tayi maki duba ke nan a kanshi wanan na daya daga cikin abinda take maki gudu da halin su. Wani irin gululun bakin ciki ne ta ziyarci zuciyana a lokacin don may sai yanzu ake fada min abinda ni ba kasa hangowa kaina a baya aka rufeni ta baibai ina hauka. Muryan baba ne ke fadin yanzu shi da yaron arziki ne har zamu kai maki kaya ya kwashe ya sayar don baida kunya data idanu ga iyayyen shi a gida basu fada muna komai ba kan hakan. Tun wanan lokacin na raina halin shi dana mahaifin shi shine zaman da sukace zasu zo gidan su zauna daku don kada a barku ku yara zallah a gida babu babba a cikin ku din. Sai kuma ya koma bani hakkuri akan in koma in san hanyar da zan bullo mashi ya daina wanan halin daya tsiro min don rainin wayau ma a cikin gidan daya kanwar yar hayana yake nema kuma. Haka dai ya samu har na natsu na daina kukan fili da nakeyi sai na zuciya yanzu na koma yi ina maijin wani irin zafin Jamil din a raina ga wanan rainin wayau daya ja min gun yan hayan gida na. Duk zaman lafiyan da nakeyi dasu sai da yayi kokari ya zubar min da mutunci na a gare su ta hanyar neman yar uwarsu da yajeyi wanda nake ganin kasawa ne a hakan gare ni. Nan dai anty ta lalabani na koma daki na zauna aka kawo min abinci naci sai dai ban iya cin wani abin kirki ba duk da son abincin da nakeyi in ci a raina don tun safe ban samu na karya ba saboda ruwan saman da akai tayi da tun bayan sallah asuba din ranan. Bayan la,asar sai ga mama matar mahaifin shi ta biyo bayana tana fadin ita bata san ban gidan ba ta dauka ko ina daki na kwanta ne bayan da aka gama hayaniya da yan hanya aka lafa. Nan dai sukai ta magana kan hakan da matan baba inda suka nuna mata rashin dacewan hakan da yake min a gidan dake da mata da yawa. Ta samu ta bada hakkuri muka koma gida tare da ita kamar komai bai faru ba a baya har dare gogan bai leko gida ba sai dai ban sani ba ko ya shigo bayana don ban ga alaman hakan ba tunda banga ta canza tufafi ba . Daya shigo gidan kai tsaye abinci ya tambaya nace ban yi ba har da dan barazanan shi don may ba a girka abinci ba nima a hasale na bashi amsa da kaje gurin yan iskan da kuke
Chapter 50 · 0% Book details