Sashe 86
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Narasa inda zan sa kaina da rikicin Jamil akan kudin nan daya kwallafa ranshi gare su. Gashini bako ganin kudin nayi bawa a idona va do Baffa ya rike ya hanani komai daga cikin kudin. Gashi shi kuma Jamil har yana kirarin zai iya sakina idan na hanashi wana kudi do baiga amfnin zama dani va tunda zan iya samu in hanashi yanzu. Wai da sani na aikai komai na rike kudina a gidan mu don ai va haka aka saba yi ba a baya cn da yanzu za a kirkiro mai da wani sallon kanina ya rike kudina. Da abin ya ishe ni na aika akira min kanwata dake aure yar gurin baba kabir a kusa damu do ya hanani fita ko ina inga kowa nawa lokacj saboda baki rai da yakeyi dani a gida daga ni sai shi sai yan hayan mu dake gefe daya a gidan da ba wani shiri mm nake dasu ba sosai. Wanda duk sherin shi ne hakan ya hanani zaman lafiya da kowa a gidan don ba halin ya gano ina shiri da daya daga ciki matan gidan yanzu zai fara sukan mai shi har sai naji na tsaneta a raina. Mu bar shiri hankalin shi zai kwanta wasa wasa sai da yasa na kore duk hausawan dake gida suna haya ya zuba matan yare a gida sai bahausa daya ta saura muke zama da ita. Ko ita do tana matar abokin shine da suke shiri shi kuma mijin ba mazauni gari bane dama sai lokaci lokaci yake zuwa gurin iyalin shi yayi yan kwanaki ya koma. Abin da na kula dashi shine matar da muna zaman lafiya kasancewar mu hausawa a gidan dani da ita sai yanzu naga canjin fuska a gare ta kuma har da diyana. Abu kadan sai taso fada ya hada ni da ita sai dai ban biye mata nakan share ta idan naga tana jin fitina dani lokacin nakan fita batun ta sai ta sauka da kanta zamu shirya. Sai na fahinci na wanan lokacin yafi tsananta don magana take dashi a bakin ta da take son samun kafa ta fada min shi a cikin fada. Rashin kulata da banyi ba yasa ban ji ko may take da niyar fada min ba a lokacin wanan ke nan. Bayan kanwata tazo nake fada mata halin da muke ciki da jamil da abinda yake fada min a yanzu bata ko bari nakai ayaba ta karbe zancen da fadin shiko Jamil dai. Duk irin halarcin da kikai mashi da kudin ki da farko bai gani ba sai wanan da baida wani yawa kuma shine na karshe. Tace a fusace ki fita batun shi duk abinda zaiyi yaje yayi kawai kudi daine suna hannun baffa a yanzu bai iya kwatar su kuma. Watau shi ya saba cin banza yanzu ya sa rai a wayan nan yaga sunzo basu shiga hannun shi ba shine yake jin haushin akan hakan. Ki ma godewa Allah da akai dabaran yin hakan gareki don kila wanan a samu a sai maki abin kwarai dashi. Kinga ko ba zai so haka ba shi don yasan kece da karuwa a kan hakan da za ai maki din nan gaba, surutu take zubawa. Wanda ni ba haka naso daga gare taba don kiranta nayi ta ban shawaran yadda zan karbo kudina hannun baffa in bawa jamil nake so ba wanan dogon sharhin da take min ba a yanzu. Ta fahinci maganan bai mun dadi a raina yadda taga ina bata fuskana kamar zancen ya isheni ji hakana sai ta dawo fadin yanzun dai shawara ya rage gare ki . Idan kinga zaki karba ki bashi ne don kada ku samu matsala sai kiwa baffa magana ya baki ki bashi a zauna lafiya. Sai lokacin na iya magana tunda ta fara magana nace nima dai haka naga yafi sauki ya bani kudin in bashi a zauna lafiya idan ya kashe sai kwadan shi ya fada. Wani kallo tayi min tare da mikewa tana gyara goyon yarta dake bayan ta tare da fadin ni zan tafi Allah ya sauwa ka. Saurin tare ta nayi ina fadin yanzu in turo maki Baffa din gidan ki ki masa magana ko zai yarda ya bani kudin na fada cikin yanayin son ta taimakeni din. Tace ba matsala indai zai yarda ya bada kudin ai ta bafa cikin son ta bar gidana a gagauce don ko bata fada ba ranta ya baci dani sosai don bata samu hadin kai a gurina ba. Kamar yadda tace zata kira baffa din gidan ta haka ta aika yazo suka zauna sukai min tas kan rashin sanin ciwon kaina da banyi ba. Karshe dai baffa din yace ta barshi da Jamil din yasan hanyan da zai bullo mashi akan maganan kudin . Washe gari sai gashi ya sallama gidan namu da safe na tare shi a cikin daure fuska muka gaisa sama sama dashi yace dani bayan mun gama gaisawa. Naji sakon ki gurin anty sai dai ki sani na riga da nayi maki amfani da kudin ki kamar yadda nace zanyi Raina ya baci kafin ya gama magana nace kudin wai ko nawa nace kaban abina inyi yadda nake so da abina zaka kawo min wani magana yanzu kuma. Mikewa tsaye yayi yana fadin kiyi duk abinda zakiyi kudi dai ne na hana bazan bayar ba kiyi abinda zakiyi dake da mijin naki yana fadin haka ya fice daga gidan rai bace. Nima na bishi da zagi na fitan arziki har ya bace min a gidan na zauna ina huci sai ga jamil din ya fito daga daki don yana ciki kwace. Dama nasan da gaiyya akai min wanan abin don wanan ba shawaran baffa bane shi kadai da munafukar nan anty suka hada baki a karbe kudin nan. Suci, su rike zasu ga abinda zanyi nan gaba wallahi don kowa ai ya iya iskanci shi karami dashi zai kawowa mutane rainin wayo don ya raina mutane. In akwai abinda nake tsoro shine Jamil ya furta zai sakeni a duniyan nan don irin son da nake mashi a raina ba na wasa bane. Wanda mutane suke min kallon tababba ko mara wayo don ban san ciwon kaina ba dole na shirya zuwa gidan kanwata again don ta kara lalasan min Baffa din ya bani kudin in bashi . Don ban son iyayyen mu su san da wanan zancen ga kudin da aka bani in ba yan uwa daya karbe ya zama min fitina sai zargina da zagi yan uwa keyi kan an basu kudi na cinye. A gidan ta baffa yazo ya samay mu inda da kyat yace sai dai indan shi zai arawa Jamil din kudin shi inya yarda suyi aggrement a rubuce . Don kudina ya riga ya juya min su kamar yadda yace min da farko dole na yarda da wanan shawaran don nasan su suna da kudin ko nawane a hannun su. Da wanan shawaran na dawo gida sai zuwa hudu na yamma Jamil din ya shigo yana wani cicika dani na fada mai cikin daurewa abinda Baffa din ya ce min. Kamar maye don na dauka zaiyi fushi yace bai karba sai naji yace idan haka yaga zaiyi ai ba matsala . Shi a zato shi zai dai ci kudin ko ta halin kaka don haka ya dai samu su shigo hannun shi din shike nan yadai ci kudin ke nan. Ba musu ko wani zance yace sai baffa din yazo zuwa yamma ko sai gashi gidan mu nan suka zauna don tsaban iya makirci na Jamil ya nuna mai karmar bashine mai fushi da fada ba a kan kudin. Nan ya fara dadin baki wa baffa din yana fadin ba wani abu yasa nake son rike kudin nan ba sai don yanzu sana,an kifi yana tashi sosai daga nan zuwa kasan Niger nake son in dan juya in samu nima. Baffa ya katse shi da fadin zuwa yaushe zaka dawo min da kudin ke nan yace zuwa nan da wata hudu idan damana ya sauko kasuwa ya kwanta ke nan. Yace ba matsala yanzu a kawo takarda muyi shi a rubuce don gudun abinda kaje ya dawo nan gaba kaga kowa yasan munyi abu a cikin wayewan kai ke nan. Bai ki ba nan ya mile ya dauko biro da takarda sukayi shi a rubuce yace dari biyu ko da hamsim yake son a bashi. Baffa yace su dai tsaya a dari don shima yana son yin lalura da kudin ne nan gaba. Ranshi ya bata sosai don jin abinda Baffa din yace amma ba yadda zaiyi ya karbi dari din a rubuce kamar yadda yace zai bashi. Wanan ya kawo zaman lafiya a tsakanin mu yanzu kwana biyu da bashi kudin ya tattara ya bar garin ya tafi inda yake zuwa a cewar shi. Sai bayan tafiyan shi ne na samu sauki ga duk alamuran gabana Baffa ya samay ni gida yana fada min cewa kudina saura suna ban zai shiga kano ya saro muna kanani atamfofi mu sayar. Nayi murna kwarai da jin hakan inda bai kara kwanaki ba ya wuce zuwa kano komai daidai ya saya muna ya turo muna dashi. Nan na fara sana,a dadi dadi ana saye ana sayo min wasu idan na sayar na tura mai kudin sai ya turo min da wasu. Sana,an ya karbe ni sosai don dama haka nake da sana,a idan inayi sai ya karbe ni sai dai matsalan da aka samu daga baya shine. Tun tafiyan Jamil ba aike ba waya shiru kamar an aiki bawa garin su ga yara dole muci abinci na fara amfani da dan kudin dake a hannu na na turamay da nake sayarwa din. Sai kudin suka fara lalace min ga sana,a yanzu sai da bashi mutane sai su rike kudi kaita bi basu baka ba sai wani lokaci abaka su a lalace. Abin dai nawa sai ya koma min kamar mai bakin iyayye akai ba wani ci gaba kuma har yakai na kasa tura ma Baffa din da kudin da nake aikawa a sayo min yan turamay dashi. Kamar nawa matsalan itama sumaiya kanwata haka abin nata ya lalace sai dai ita ba a jin komai daga