Sashe 10
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read
ya san shi. Mun dawo daga school muka samay shi nan na hau murna sai shamsiya ne da bata waye shi ba s taki zuwa wurin shi ta make gurin mama. Kiran da mama ta kwala min ne yasa na bar falon zuwa gurin ta kitchen inda take aikin abincin abinci na samu tana hada masu. Ta nuna min tire tace in hada abinsha a cikin dan karamin fridge din mu dake aiki a kitchen din na shiga hada kayan data umurce ni akan tire din tana gyara min. Lemu su zobo mai sanyi sai ruwan sha na leda shima dai mai sanyi sosai kofina na dauko na jera na dauka na kai masu a falon namu. Inda na samu suna magana akan umma nayi sallama suka amsa mun cike da fara,a a fuskokin su a gaban su na kawo na aje. Baba kabiru ne ya dube ni yace masha Allahu diyar tawa tayi wayo sosai wallahi ai umma bata gane ki idan ta ganki yanzu. Kunya naji na dan tsone kaina na dago ina fadin baba umma ta bar fada ne yanzu cikin yarinta zalla nake mashi tambayan. Mahaifina ne yayi min dakuwa a inda yake tare da fadin tabar ma furera fadan cewa yar shi watau gwagona shigowan mama bayana dauke da kayan abinci ne ya katse maganan. Sai da ta aje take fadin wai yaya ake magana baba yace wai tambaya take idan umma ta bar fada yanzu. Juyawa tayi tana fadin ga mara kunyan banza idan bata bar fada ba ke nan baki zuwa idan mun tashi tafiya da sauri nace wallahi ina zuwa mama suka sa min dariya. Muryan baba kabiru naji yana fadin idan kin gama aiki sai kije kiga mota dama ita nazo in nuna maku kusa min albarka. Mama ta fadada murmyshin ta tana murnan jin abinda yace din da sauri ta koma daki ta dauko hijja din ta zuwa waje inda muka mara mata baya zuwa ganin motar. Munyi murna sosai da ganin motar baba kabiru din sai albarka mama ke sakawa tana taya shi murna yana jin dadi har cikin ranshi. Sai lokacin ya sauke muna tsaraban da ya kawo muna abin kamar da gayya sai da babana ya sauke kai ya dago yana fadin kabiru may yasa kai muna haka. Yana dariya tare da fadin wanan ba komai bane ai nan dai baba ya rasa abinda zaice ya shiga yi mashi godiya. Sunyi hira sosai ranan kafin ya tafi masaukin daya sauka ya kwana a can din bai sauka a gidan mu ba kamar yadda ya saba. Sai washe garine da yazo ya karya yake fadin a ranan zai koma mama bata so jin hakan ba don ta dauka zai muna dan kwana biyu ne a nan. Da zai tafi ne baba yai mashi alkawarin muna nan tafe idan babban sallah yazo a gida yake so muyi sallah insha Allahu. Baba kabiru yace daka kyauta don umma ta damu da maganan ku idan kai ba zaka samu zuwa ba kabar iyalin ka suje suga gida hakana a gansu suma. Bai jima ba ya ba mama kudi ta g itama ya bata tayi mai godiya ya tafi ya barmu da kewan shi tare da kewan gida. Bayan komawan baba kabiru ne mama ta dinga tayarwa baba da hankali akan tafiyan namu don taga baida niyar zuwan namu kuma. Wanan dalilin yasa dole baba ya mayar da hankali gurin fara muna shirin tafiya gida don mu dubu su, suma su gane mu ba wani shiri baba yai muna na azo a gani ba. Amma haka mama tayi ta godiya ga abinda ya hada muna din inda suka aje magana idan mun fara isa zai zo shi daga baya sai mu dawo tare dashi. Bata ki ta hada kan mu munyi kumshi da kitso da duk wani gyara daya dace mace tayi idan zatai tafiya mun fito shar damu da kanshi ya kaimu tashan da zata sada mu da garin mu don indan munje ba wani wahala zamu kai kan mu gida. Sai bayan magariba muka isa garin sai ganin mu akayi daga sama ance mai hali baya barin halin sa don umma maimakon tayi murna da ganin mu sai cewa tayi haka kwatsam babu sanarwa da zuwan mu. Mama ta hade bacin ranta ga maganan umma din ta shiga gaida ita nan mutanen gidan namu suka shiga zuwa taron mu da zuwa suna nuna jin dadin ganin mu. Lokacin na dan kara tasawa ina aji biyar na primary don haka yan garin mu ke ganin na girma sosai a lokacin na isa budurwa a gurin su kowa yazo maganan girmana yake yi. Yadda matar baban mu na lagos suke zuwa ana kallon su muma haka muka koma a gurin yan garin mu don har zuwa ake kallon mu wai hausan mu daya canza yanzu. Mama sai faman raba dan tsaraban da tayo take yi masu wanda sai yanzu na fahinci hikimarta nayo wanan tsaraban har baba na fada da ita wai ta dauki kaya da yawa. Ashe da shirin ta tazo gida do fitar da kanta kunya mun samu baba kabiru ya auro wata mace a birni yar boko itace amaryan baba yanzu dake tashe a gidan. Munje gidan kakanin mu na fannin mahaifiyar mu mun gaida su mun wuni acan tare dasu suna nuna muna so da kauna irin na kakani. Satin mu daya da zuwa gida akai sallah baba na wanan shekaran mun shiga mun fita don ba laifi mahaifin mu ya muna dinkuna wanda zai fitar damu daban da mutane garin mu. Mun fita tare da yan uwana mun zaga gidajen yan uwa da abokan arziki duk gidan da muka je maganan tufafin jikina suke wanda a lokacin ban gane may suke nufi ba. Ranan sallah da dare mun fita wasa tunda sallah ne ba a hanamu fitan dare lokacin wasa ake irin na kauye maza da mata. Sai ga wasu sun zo inda muke zaune saman dan dakalin kofar gidan mu yan uwan mu ne don zuri,an mu daya dasu nan muka buge da wasa dasu sai daya daga ciki yake cewa wai yana so na. Maganan daya bata min wasana na ranan ke nan na shige gida ina kuka tare da fada ma umma nan umma ta fita da tujara ta zage shu tas har iyayyen shi. Tare da fadin da safe zataje har gida ta yiwa iyayyen shi kashedi kan wanan wasan banzan daya tsiro min dashi don ni ban san wanan ba kada su lalatani. Ashe tun shigowa ina kuka suka gudu daga kofan gidan don sun san dama umma na iya fitowa taci masu mutunci . Can daga baya suka labe suna sauraren fadan ta har taci ta sude ta koma ciki ni a lokacin har nayi barci ban san shigowan ta ba gidan. Washe gari ma da fitinan umma ta tashi sai da baba kabiru yai mata waigi kan maganan yace haba umma kurciyane fa yana ganin shima yana zuwa birni yana karatu. Don yace yana son ta ai ba ana nufin shine son ba ko dole taja bakin ta tayi shiru don taga ran baba kabiru din ya baci yanzun ko ko dan ka ne idan yana da hali tsoron saba mashi kake ji. Munyi hutu tun muna saka idon zuwan baba shiru baba bai zo ba har muka share wata da kwanaki shiru baba baizo ba. Tun mama na damuwa da rashin zuwan shi akan lokaci don karatun mu da zamu rasa don rashin zuwan shi zai iya kawo illa ga karatun namu da mukeyi a can. Sai dai shiru har wanan lokacin tun tana dan maneji da dan kudin dake hannun ta har komai ya fara yi muna tsaye sai dai baba kabiru yana yawan taimaka mata sosai ta fannin abin amfanin yau da kulun da abinda zamuci. Haka yasa damuwa ya rage a zuciyar mama din don dan abinda take samu na taimako a wurin dan uwan baba din a yanzu ba kamar da can baya ba. Dadai taga zaman ba mai karewa bane haka yasa ta dan fara sana, ar mata na cikin gida don rage zaman banza ga irin sana,an data ga anayi acan inda muka fito. Mu kan bamu da wani damuwa ganin yan uwa ta ko ina bai barmu mun shiga damuwa kamar yadda mama ta shiga ba sai dai wanan Jamilun yana matsa min har yanzu a rayuwana. Rana kasuwa garin zai dan sawo abu ya aiko mun dashi a boye umma bata sani ba don masu kawowan sun san halin umma har su zata iya yaga idan ta gani. Haka yasa a can wani lungu suke ajewa sai suzo su kirani idan na fito su bani sai in hau kuka suna dariya zasu cinye a gaba su koma suce sun bani na karba.