← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 81 OF 89

Sashe 81

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAN IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Jamil bai dawo ba sai da ya share wata shidda cif a can ko wanan dawowan don sallah karama daya gaba to ne yazo. Yadda ya tafi haka ya dawo min babu kudin gadona babu karuwa daga gare shi ni na tashi ga tutar babu ke nan yanzu. Duk cikin abinda yake min wanan sai yafi ci mun rai fiye da sauran don kudin gadon yafi tsaya min a rai. Ya dawo yana wani daure min fuska ko magana ya hadamu cikin tsawa zai mun magana da karfi yana daka min tsawa . Ganin haka yasa naja baya dashi sai dai ranan kanwata da sukazo gida sallah tazo gidan mu shine ya fito suna gaisawa da ita. Har ya jefoni a cikin zancen su harda fita ya sayo masu kayan sanyi na jika makoshi kamar wani na kirki dashi. Bai jima ba ya fita ya barmu gidan sai da ya fita take fadin kai mijin nan naki kamar wani na kirki idan yana wasu halaiya. Murmushi nayi bance da ita komai ba sai na dauko mata wani zance na daban wanda ya shafi hiran gidan mu sai muka shagala. Can lokacin sallah yayi ta mike ta fita don yin alwala ina Allah Allah ta tsaya iya falo kada tace zata shiga min kuryan dakina. Sai dai banyi sa,a ba don tana shigowa duk da na shimfida mata abin sallah a falo sai ta shige kuryan dakina direct don cire unders din ta. Kira naji ta kwala min daga dakin na dauka na wani abu ne sai na shiga tana cewa dani ina gadon ki anty ta tsare ni da idanuwan ta. Kasa amsa mata nayi lokacin take fadin yanzu har gadon kwsncin ku sai da wanan mayaudaron mijin naki yasa kika sayar wai may kika mayar da kanki for god sake ? Wallahi ban ganin laifin shi naki nake gani yanzu don kece mai bashi kwarin gwiwan yayi maki duk wani abinda yake maki.. Haka nazo nake jin wanan kangon da muka saya don gaba mu samu madogara wai ya sayar da naki ya tafi da kudin . Tsaye nake daga kofa ina sauraren ta ban san lokacin da na tafi baya ba suuuu zan fadi tayi saurin rike min hannu daga ciki. Falo ta fito dani tana fadin wai may ye haka ko dama baki da labarin ya sayar da kangon gidan da aka sai maki ne tana fadi tana kokarin zama a kusa dani lokacin. Wasu hawayen da sukaki tsayawa suke zubo min dafa idanuna lokaci guda na kasa controling din su in mata bayani. Taci gaba da fadi dama tunda nazo naji wanan zancen hankalina ya tashi gaki da yara mata a gaban ki yanzu kin san lalurar diya mace da kashin kudi ne komai na ya mace kudine tun tana yarinya. Duk bayanin da takeyi ban iya bata amsa ba ko daga kai in kalle ta banyi ba asalima na lula wani duniyan tunane ga baki daya. Sallah ta tayar har ta kare ina gurin a zaune ban iya dagawa ba waya ta dauko daga jakkar ta ta kira baffa kanina yazo ya samay mu agidan. Bai jima ba ya iso nan takw fada mai abinda ke faruwa dani numfasawa yayi tare da girgiza kanshi yace shike nan yana murmushi . Maimakon in ji haushin mai laifi Jamil sai haushin ya koma ga wanda baiji ba bai gani ba Baffa. Ban san lokacin da nace zakayi dariya mana tunda ba kai aka cuta ba yace nikan ai ya gama cutana wallahi . Sai dai ke ki zauna watarana sai ya sayar dake da yayan ki kuna zaune za a ce kuzo ku tafi ya sayar daku ya amshi kudin ku. Nikan yanzu wallahi kar nake kallon shi duk wani sallon yaudaran shi na sani tunkan ya min shi sai dai ke da yake tsarawa zai cuta amma bani ba. Ya mike har ya fara tafiya ya juyo yana dadin kuma bari kiji wallahi sai ya biya kudin wanan gidan daya sayar maki ko muyi sharia dashi wallahi . Yana fadin haka ya fice abinshi ya barmu zaune kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi zagi kan ranan ya sha,shi kwado kwado ba wurina ba wurin kanwata ba da tafini ma jin takaicin shi lokacin. Bai dawo gida ba har ta tafi kamar yasan muna jiran shi har ta tafi abinta sai dare sosai ya dawo ban jira ko ya zauna ba nace. Jamil may kake so da rayuwana ne wai Jamil may nai maka kake bina da cicin duduge na hakane ?. Ke ya fada cikin wani tsawa ya jiyo yana kallona tare da fadin wani irin magana kike fada min haka wai ? Na fada maka mayaudari kawai azzalumi na yarda da kai nabar kowa nawa saboda kai amma kazo ka cuce ni dan gidan da nake barazanar ina dashi don yaudara ashe ka sayar ban sani ba. Wani irin kallon mamaki yai min a lokaci guda yana mamakin yadda naji wanan maganan da yake ta boye min wata da watanni. Jin ban yi shiru ba yasa yace na sayar din idan ban sayar ba kina da kudin da zaki karasa ginashi ne komay. Ranan kaca kaca mukayi dashi har da dukana yayi kan abina saboda irin kalaman da nake fada mai masu daci duk abinda yazo min a baki fada mai nakeyi. Sai da yan hayan gidan mu suka rabamu a cikin daren nan abinda ba a taba yi muna ba wani yaji mu muna rikici irin haka. Asuban farko na nufi gidan iyayyen shi duk da yanzu ba shirin nan da mahaifin shi ke yi dashi irin baya can tunda ya yaudare shi kan kudi. Mahaifin shi ke nan balle ni haka dai na daure na tafi gidan nice na tayar dasu da barci ranan na shigo da kukana wiwi . Cikin tashin hankali suke tambayana ko wani abu ya samu dan nasu ne a cikin dare zama nayi nai masu bayanin komai dake faruwa. Sai tsuki mahaufin nashi yayi yana fadin wanan ai ba yanzu kuka fara ba ko don haka kije ki hakkuri ku shirya kan ku. Don ko biya akace yayi baida kudin biyan wanan gidan kin sani tunda ya mayar da kanshi mutumin banza a cikin yan uwa. Ban gane komai ba haka na juyo na dawo gida raina bace ina danasanin zuwa wurin mahaifan nasa. Ina dawowa gida na samu wani rikici a gida mu don kanina Baffa ne ya bugo sammako zuwa gidan mu ya samu Jamil din da tashin hankali kan maganan. Rikici sukayi sosai da kanina din kan sai ya biya wanab kudin shiko yana fadin ina ruwan Baffa din cikin magana mu. Shima ya rikice mai sunyi fitina sosai ranan tsakanin su sai da Jamil din yaje ya kira mijin kanwata suka zo tare aka hade nan tare aka aje magana yace zai biya idan ya samu kudi. Haka aka aje maganan rayuka dai basuyi dadi ba don Jamil din yan uwana sun bashi mamaki sosai ranan don basuyi mai ragowa ba. Haka dai muka hau sama muka fado yana ta faman fushi dani da kowa nawq da yazo min yawon sallah bai sakewa dasu koda sun gaida shi sai kace bashine mai laifin ba. Abinda ban sani ba shine jamil ya na zaman rayuwa can da wata yana yaudarana anan shine yake kwasan dukiyana yana karya dashi. Kanwata diyar baba kabir ke fada min wanan maganan da tazo gidan mu gaidani da sallah maimakon in kwantar da hankalina in fahinci may take nufi. Sai na tare ta da masifa kuma ina fadin yace wanan karya ake mai don yace duk wanda yaji yana wanan maganan sai yayi kotu da mau shi. Tace tau tau nayi shiru anty hadiza dama nima naga abindai tayi yawa ne yasa nace haka tana kokarin tashi tsaye tana saka hijabin ta a jiki. Haka ta tafi tana tsaron in kwashe in fada mashi bata san bamu cikin dadin raima dashi ba lokacin. Don bayan kanne na da muke ciki daya dasu lokacin ban yarda na fada wa wani wanan maganan dake cina ba kaf a cikin dangin mu. Waini ban son kowa yaji aimin dariya da gwai tunda naki uban mu na zabi mijina fiye dashi din yanzu ashe abin ba hala bane. Abin duniya baya boyuwa don kowa kallo na yake da maganan har baba kabir yasan da zancen sai da kangona da Jamil din yayi yanzu. Sai yanzu nake jin zafin aikina da baba kabir ya sama min nace aba Jamil ni yar dadi aure gashi yanzu dan wanda aka samo min ina dan samun rufin asiri an dakartar damu shekara biyu da wattani. Shine dalilin da nake cikin matse sosai ga sana, a ina son yi ba jari mai kwari da zanyi sana, ar dashi hakana. Sana,a sai da jari mai kwaro don idan baka da jari abin bai kai ko ina sai mutum ya cinye kwana biyu da farawa. Zaman jiran tsamani kawai muke na sauran kudin mu kullun ko zai fito mu dan samu sa,ida a gurin gashi shiru har yanzu ba labarin komai. Ashe ban sani ba mijin yar uwata ganin Jamil yaci bulus shima daya tashi sai ya sayar da kangayen kanne na gaba daya su uku ya sai mota dashi da mahaifin shi. Sai dai nasa akwai banbanci da nawa don da niyar idan ya samu sai ya sai masu wani nan gaba yayi haka kunga ke nan akwai banbanci sosai da nawa matsalan. Sai dai lokacin da kanina ya samu wanan labarin hankalin shi ya tashi yasa mijin nata a gaba dole ya samu kudi su sai dai saida ya bashi lokaci. Daya samu ya biya su nasu matar shi ce bamu san yadda suka kare da nata ba har yau don banji tai min maganan komai ba akan hakan. Haka yasa nasan cikin maza akwai mayaudara da dama sai sa, a abindai ke nan don wasu abin matan su bai ishe su kallo ba balle har su taba. Sai dai muka bamuyi dace da bagari ba gaskiya musanman ma ni da komai ci yake babu biyan bukata gare ni ko kadan banda riban kwana dashi da nake samu
Chapter 81 · 0% Book details