← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

a falon shi yake fada muna sunyi shawara da yan uwan shi sun sayar da gidan mu na Abuja sun saya muna wani a nan garin don nan din yafi kusa da gida. Don haka yan haya ke cikin gidan za a dinga karban kudin haya ana muna abinda ya dace damu. Mukai mashi godiya bayan ya gama muna bayani ya fada muna zamu iya zuwa idan mun dawo muga gidan da ko yan uwan mu maza su tafi su gani. Wanan maganan ya kara kwantar muna da hankalin mu summaiya ke fadin kun gani nace daku abi sannu don ban sa baba zai iya muna hakan ba da ake fadi. Gashi mahaifin mu ashe duk takardun shi sunan baba kabiru ne a ciki sai nawa dana baffa daya saka magadan shi. Mun koma makaranta zuciyar mu ba wani zargi ko tunanen komai a ciki don yadda mutane ke zuzuta zancen kan mahaifin mu yabar dukiya mai yawa sai bamuyi tunanen a ina dukiyan yake ba wanda mu bamu san dashi ba. Bamuyi kuma la,akari da irin samun da baba kabiru yake yi ba don shi din yanzu shahararen dan siya sa ne da ake damawa dashi sosai. Ga kokarin da yake muna wanda mu bamu gani a lokacin don ma iyalin shi suna da hakuri da hangen nesa ne yasa basu damuwa da irin yadda yake gwada muna banbanci a tsakanin mu da nasa iyalan. Don kirikiri zai muna abu bai ma diyan cikin shi ba kuma basu damuwa da hakan da yake muna din sai dai duk da haka mutane masu hana ruwa gudu suna nuna muna ai cutar mu akeyi kawai. Matsin da shamsiya ke muna na mu gudu daga gidan na baba kabiru ne yayi yawa ganin bamu gudu ba yasa ranan muka wayi gari babu shamsiya ta tattara kayan ta ta gudu daga gidan baba kabiru din. Wanda hakan ya batawa baba rai sosai har yakai ga kiran wayan mahaifinta yana tambayan shi sai cewa yayi eh tana nan gida ai ta iso da yamman nan yace to ku barta a gurin ku don dai ni nasan gidana banda yunwar komai a tare dani. Maganan yaso hada zumunci fada don mahaifin nata na rufe ido ya goyi bayan yar shi ya mance da irin halarcin da akai muna din a gidan kanin nasa. A wani yammaci jamil ya kawo min ziyara yana saye a cikin dinkin shada da hula ya fito dan bahaushe shi sak sai dan glass din daya kafa a fuskan shi. Na fito na samay shi tsaye a waje yana jiran fitowa na lokacin yana gani na ya sakar min wani dan murmushi mai laushe yana a fuskan shi na jin dadin ganina a lokacin. Dadin ganin shi naji a lokacin ban san lokacin dana mayar mai da murmushin ba na karaso da sallama na gurin ina mashi sannu da zuwa. Ya amsa min da yar fara,a a fuskan shi tare da fadin gani dai na biyo ki don yanzu naga alaman kin samu wasu anan kin fara mantawa dani. Na dan ji zafin maganan a raina don ban ci wanan maganan ba a gare shi idan yayi duba ga yadda nake samun matsi a kan shi a gida akanshi gurin umma don tabi ta bata zancen shi ta ko ina. Gashi idan na tuna shi sai naji kamar nima in gudu yadda shamsiya ta gudu daga gidan baba kabiru din duk a kan shi. Sai dai ba zan iya yin hakan ga baba kabiru ba don ya nuna muna duk wani kauna daya dace a duniya dashi da matan shi. Naja dogon nunfashi tare da fadin wanan zaton kake mun kuma yanzu duk irin halaracin da nake nunawa akan ka yace. Kin san garin yafi namu matasa wayayu na sani ko wani ke son min yankan baya akan ki wanan dadewa da kika yi bamu hadu ba ya fara sani a shakun soyayyan mu. Murmushi nayi a raina ina kallon shi dayasan kewan shi na hanani sakat a raina da bai fada min wanan maganan ba tunanen sa yana hanani jin dadin zaman garin. Sai dai a fili nace bayan ajiyan zuciya ban yarda da uzurin ka ba jamil don da ka damu dani yadda kake fadin wani nisane a tsakanin mu da zai hanaka zuwa nan din kai. Yanisa yana murmushi yace kin san abu ga mara hali yanzun ma da kin san yarda nazo nan din dakin tausaya min. Nayi walwal da ido nace da fatan dai ba wani rikici ka jefa kanka ba don kazo nan din ya girgiza kai tare da fadin ko daya wallahi. Mun dauki lokaci har baba kabiru ya dawo ya samay mu a gurin na dauka zai min fada sai naga babu wani alaman baci rai a tare dashi dana shigo. Bayan tafiyan shi ne zuciyana ta shiga garari akan sa ashe duk yadda nake daukan shi a raina yafi hakan damuwa dani don irin dadan kalaman daya shimfida min ya tafi. Alhamdullahi na gama karatuna lafiya inda na samu kyautar jam daga hukumar makarantar da nake ciki mu uku muka samu wanan kyautar a shekaran. Zuwa lokacin tsakanina da jamil soyayya ne mai karfi wanda har lokacin umma na saman bakin ta akan bazan aure shi ba ko bayan ranta ne kuwa don ba zata hada zuria da irin gidan su ba. Ban damuwa da maganan ta don yanzu akai back din da ban tsoron ta na fahinci ita din kakace a wurina ba uwa ba sai dai akwai shakku da tsoron ta a raina.
Chapter 28 · 0% Book details