← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 61 OF 89

Sashe 61

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Don girman Allah kuyi hakkuri ba laifina bane haka Allah ya tsara ma lamarina wallahi wallahi wutane bamu da har yanzu nakai caji wayata ta samu matsala dole yau sai da na sayi wata still bamu da wuta har yanzu don trasfomer din mune ya buga. 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo. Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani. Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ? Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba. Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana. Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar. Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai. Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin nata. Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata. Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su. Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya. Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban son wata mace yar uwana ta shiga min dakin. Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake. Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in je gurin shi da wanan maganan. A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine. Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi min abin kwarai don kafin in magana tace . Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana. Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do Allah. Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane suka sa masu hakanan. Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son zuciyan da suka saba ba. Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin su. Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su. Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin na bata rabin da mahaifin shi din ya bani. Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito ina hawaye gidan zuwa gidana. Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje. Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana. Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba. Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi ba wallahi. Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi da hakkin ka ka rataya a kaina . Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari. Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari sai da ba dafe wurin don zafi. Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji macuci kawai azzalumi. Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don kaine ka kwashe su . A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba. Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ? Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi bata min rai sosai wallahi. Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba damuwan shi bane hakan. Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito. Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba. Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba. Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina tukukin bakin ciki da na daman auren shi. Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi. Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne a gurin mace wallahi . Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi. Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a. Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a kan ka. Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi. Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana. Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi. Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida. Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake min a baya kan yan hayan mu. Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya. Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi. Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar. Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya
Chapter 61 · 0% Book details