← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 43 OF 89

Sashe 43

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read

zai biya kudin dinkin sallah saura yan kwana ki ne Jamil ya shigo min da wasu wando da riga na wani material da aka dinka mai sulbi. Ina ta murna yan gidan mu na zuwa waini an min abin arziki da murna na na dauko kayan ina nuna masu sai cewa summaiya kanwa ta tayi a cikin tsuki . Yanzu ke wanan gwajon da aka gyara ne kike wa murna wana zanin kuma fa karami ne naji haushin maganan ta nan dai na hauta da fada sosai inda nake shiga ba nan nake fita ba. Sunje gida suke fada wa iyayyen mu mata sai cewa anty tayi shi Allah ya hore mashi ya sai mata ina laifin hakan ai ta samu kudai ku daina sa ido ga abinda bai shafe ku ba tsakanin miji da mata sai Allah. Sai cewa dayan tayi kamar kin sani anty don dakin ta tun auren ta da sati biyu da mukaje har yau babu komai a cikin sa duk an sayar wai za a canza mata wasu. Cikin dafe kirji anty tace wasu kaya kuke magana nata an sayar nan dai suka shiga fada mata abinda nace dasu anyi da kayan dakin nawa. Hankalin anty ya tashi sosai a lokacin take fadin an sayar fa da kayan kuka ce sukace idan karya ne taje gidan ta gani da idon ta. Batai nauyi a kafa ba sai gurin baba tana fada mashi shima baba da makmaki yake fadin sun sayar fa kuma malam bai fada min ba gashi duk jumma,a ina zuwa gaida shi da sallah. Ran baba ya baci sosai da wanan maganan dayaji ya danyi shiru na dan wani lokaci kafin ya furta ku kyaleta muga iya gudun ta kan wanan magana don dole wata rana magana ya taso ai. Ba haka anty taso ba taso baba ya barsu su tafi gidan su gani da kan su sai dai hakan bai samu ba dole taja bakin ta tayi shiru sai dai ta kwana da takaicin hakan a ranta. Gashi tunda aka kaini bata je dakin nawa ba saboda kawaici irin nasu don dauka na da takeyi tankar yar cikin ta tun wanan lokacin hurdan mu da anty yayi sanyi sosai. Duk da nasan laifin na a gurin su sai dai fushin ta dani yana damuna sosai da sallah ma yadda yan uwana da sauran masu kawo masu abincin sallah sukeyi nawa ya sha banbam dana saura don ba wani cika ido da yake masu ga komai nan dai a lalace a gurina. Sa,adatu diyar baba ta haihu akai suna inda baba yayi mata sha tara na arziki don shi baba mutum ne mai kula da hakkin iyalin shi gaskiya. Na dawo gida ina fadin irin abin arzikin da baba kabiru yayiwa kanwata da ta haihu sai sarakuwa na ke fadin nima inyi in samu ciki su dangwali arziki a cikin gatse. Gashi turmi turmi yayan mu yasa muna ni ban samu turmin da zan saka ba sai anty ne ta saya ta bani in bayar a lokacin amma da zan dawo sai da aka cika min leda babba da kayan buki. Zaman dai muna yinsa da dadi da wuya sai dai duk abinda suke min ina shanyewa ban fadi gidan mu don boye sirin gidan aure na. Jamil ya tsiro min da zuwa gida kauyen mu wai bukin dan uwan shi inda yace idan naje inyi sati hudu kuma kada in sauka a gurin dangi na sai gidan yan uwan shi. Nace zuwa bukin ne zanje in share har sati hudu a kauye har mutane su gaji dani kan hakan yace su yaga daman bani kuma su yake son inyi a gida idan naje. Dole haka na shirya na tafi ya danyi min dinki kala biyu na fitan buki muka je kauye aka sha buki lafiya bayan kowa ya watse ne aka ga ni banda niyar komawa gida. Sai suka tambaye ni nace sati hudu yace inyi idan nazo gidan sunyi mamakin jin hakan sai dai basuyi magana ba tunda gidane na zo ko nan din. Wasa wasa na share har sati shida bai zo ba gashi yace kada in dawo sai idan yazo ga zaman kauye ya ishe ni tun ana min abin arziki har aka koma gashi mun maki shegiya. A cikin satin na bakwai da zamu shiga ne yazo gaida wani mara lafiya a kauyen na fara shirin komawa tunda naga ya dira garin nan yace wai ba dani zai koma ba. Muka fara rikici dashi har abin ya kaimu ga saki daya naje na samu wan mahaifin mu da suka hada uba dashi da kuka na fada mai abinda Jamil yayi min. Nan dai aka kirashi akai mai fada sosai aka shirya mu ba tare da gida sun sani ba ya kuma ce ba tare dani zai koma ba sai dai idan ya koma da kwana biyu in koma. Hakan akayi ko da na dawo ina shan kamshi dashi kan sakin dayai min din ko may ya gani ya sauko da kan shi ya bar fushin da yake yi din dani. Ashe abinda ban sani ba bayan tafiyana Jamil mata yake daukowa ya kwana dasu har dakina ya bude ta baya inda iyayyen shi basu ganin abinda yakeyi don muna da kofan baya a cikin falon mu ba lalai ne su san abinda yakeyi a gidan ba. Kanne na duk sun san wanan labarin suna kallo na ne kawai an rasa wanda zai iya fada min don gudun tashin hankali sai dai su basu sani ba aikin gama ya gama ko in ma har saki suke gudu a gare ni. Don haushin cewa da nayi zan koma gida yasa shi ya sake ni a kauye don zan bata mai jin dadin shi da yake a nan din. Jamil yakai dan duniya sosai don har abokiyar ta gwaicin yar hayan gidan mu ashe wata yar duniya ita batai aure ba kamar yar uwarta ya samu suna shedan cin su a dakina da ita. Na dawo ina hura hanci wai ni ga mai miji suna kallona sara mai bisa ruwa duk da dawowan nawa bai rage shi da komai ba don sai ya raba dare a waje suna iya shegen su can da ita wai shi auren ta zaiyi a cewar shi kuji fa yan uwa. Na dawo ban dade ba Allah ya ban ciki dama a can kauye nasha maganin gargajiya na mara wai mara ne ke damuna sukace wai shiyasa har lokacin aure da shekara ban samu haihuwa ba. A fili ya nuna min farin cikin shi na samun cikin da mukayi sai dai a can kasan zuciyar shi ba haka yaso ba don yace shi bai shirya ma haihuwa ba yanzu. Daga yin aure ace wai an fara samun ciki mafarin a tara iyali ke nan da wuri tun muna da kurciyar mu ke nan zamu fara tara iyali. Nikan dadin samun cikin nakeyi sai faman planning nakeyi ni da yan uwa na dake tayani murna na gaskiya kan cikin da na samu din a yanzu. Lokacin da kanwata Saadatu ta samu ciki ta kusa haihuwa ta danyi tanadin ta takai gida don taimakawa iyayyen mu dashi duk da baba yayi fadan haka yace ta bar shi tayi laluran gaban ta ai itaka tana da hidimar da zatayi na kawayen ta. Sai dai ni ba wani labari kan hakan don ban aje ba ban ba wani ajiya ba ko turmin zanin da baba kabiru ya aiko min dashi da sallah yaso ya lalashe ni ya karbe sai dana nuna mashi hakan ba mai yuyuwa bane don tare da sauran yan uwana dake aure baba din ya saya muna kayan . Dole yana kallon abin kudi a wurina ya kyale ni ba yadda zaiyi yayi fushin shi ya gaji har ya sake don yasan na fishi gaskiya a kan zancen zanin. Iskanci ko yanzu baijin kunya a gabana zai dinga waya da yan mata suna hira da farko naso in sa mashi ido sai naga zanja wa kaina damuwa gurin kyale hakan. Ranan ina zaune wata ta kirashi ya dauka sun fara fira ke nan na wauce wayan daga hannun shi na fara dura mata ashar cikin dakiyar fuska ya dauka zanji tsoron shi dana saba ji ne ya fara daka min tsawa akan in bashi wayan har yana fadin you very stupid ki ban wayana nace. Nima tsawa ba daka mai take na birkice mashi a dakin yana gudun iyayyen shi suji ko daya daga cikin yan hayan mu suji. Girman shi ya zube a gurin su don idan zai shigo gida sai ya daure fuska kamar hadarin marance fuska ba annuri ko kadan. Zakace shine maigidan da muke cikin sa yadda yake basu doka da iko a gidan nasan badon baba yasa yan hayan ba da zai iya koran su ma. Ganin da gaske ina shirin tona mai asiri yasa ya sauko yana fadi amma ke baki da wayau dafa budurwan yayana sa,idu nake waya kin dauka ko budurwa tace. Da yake wawiya nake sai na yarda da maganan shi na miko mai wayan yayi saurin kashewa ya kuta ya fita daga dakin bai dawo gida ba sai da dare ya raba sosai ya dawo.
Chapter 43 · 0% Book details