← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 78 OF 89

Sashe 78

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

da tafiyan shi ko waya bai kiramu ba balle sakon shi ya iso gare mu. Gashi na dauke kafana ga kowa nawa don gudun wanan maganan kada in je inji takaici a raina don nasan nice banda gaskiya. Tunda munyi da anty cewa idan ya sake sayar min da wani abu da zafizafi in zo gida in fadi a dauki mataki a kan shi. Balle wanan din da dakaina na yanke shawaran sayarwa don sama wa kaina sallama sai ban mori kudin ba shi ya karbe abinshi ya tafi. Ga kuryan dakina ko dakin gwauro ya fishi dadin gani yanzu don babu komai a cikin shi sai tsohuwar katifana dake yashe a kasa da tsumakaran mu da ke gefe daya. Don hatta akwatunan auren da baba yayi min da gidan su Jamil basuyi min ba na sayar nayi lalura da kudin lokacin da naga ya sai min sabbi na haiwan karamar yata. Yanzu ko babu su tunda ya sace ya fita dasu basu dawo gidan ba har wanan lokacin, tundai ina saka damuwa a raina har yakai na hakkura na ci gaba da gudanar da rayuwana yadda na saba a baya cikin hakkuri. Mu ke nan ko yaushe cikin cin taliya ko garin kwaki don shinafi karfi a gidan yanzu. Duk da ba lalaifi indai shi zai sayo muna abinci abinda zamuci musan munci mai kyau yake sawo muna aci gaskiya.. Idan ina ba yan gida mu labari irin yadda nake baku yanzu sukan ce a cikin kudina muke cin dadin da yake sayo muna din ai. Ranan na gama abinda zanyi na kwanta barci da rana sai nayi mafalkin wai gashi tare sa wata mata da yaran su biyu wai nasa ne. Muna fada sosai dasu a cikin mafalki na falka daga barcin sai naga duk na jike da zufa jikina sai kyarma nakeyi kamar nayi fada a fili da wani. Nan na fara tunane a raina har tsawon wani lokaci ina zaune a gurin dana kwanta din ban iya tashi ba sai faman tunane nake kala kala a raina kan wanan mafalki da nayi dashi. Ina maimaitawa a cikin raina yara biyu fa a yadda na ganshi da yaran mace da namiji sai mafalkin yayi matukar tsaya mun a raina sosai. Da kyat na iya tashi na dan watsa ruwa a jikina sai ba samu na danji shakat a raina, sai dai na kasa cire zancen mafalkin a zuciya sai faman maimaita maganan nake har a fili kamar wata zautata dani. Bayan kwana biyu na fita zuwa gidan wanan kanwar tawa inda na samu aron waya na kirashi don abokin shi ya bamu lamban shi ranan. Kira biyu ya daga don baisan ko waye ya kirashi ba don nasan da yasan nice kila ba zai dauka ba ma ban sani ba. Yana dauka tare da fadin hello nace sallamu Alaikum baban Amira don haka yanzu nafi kiranshi dashi, yana jin muryana yace . Hadiza ce a ina kika samu layina wayan wa kika samu kika kirani dashi wani amsa zan bashi daga cikin don ko gaisawa bai bari munyi ba ya hauni da wanan tambayan haka a jere. Babu boyo nace na safiya ce kanwata yace kinje gidan ta ke nan ko nace eh yanzu nazo gidan ta don ta ara min waya in kiraka. Ya sauke ajiyan zuciya yana fadin to yaya gida ya yaran kunji kwana biyu shiru ko nace shiyasa ma na nemi layin ka don muji ko lafiya shiru haka ? Yace lafiya abubuwa ne suka dan cije min kwana biyu yasa ban kiraku ba ban turo maku sako ba har yanzu. Nace yanzu baba Amira don abubuwa sun tsaya sai ka kasa turo muna dan kudin da zamuci abinci dashi ka san fa baka barmu da komai ba ka tafi. Yace a hasale wanan wani irin magana ne haka ni ban fiki sanin halin da na barku a ciki bane gidan ke may yasa baki da fahinta ne wai hadiza ? Inda yake shiga ba nan yake fita ba idan da dane hakkuri zan bashi da yake fadan nan sai yaji har ya gama ban tanka shi ba sai da naji ya gama nace. Ni yanzu dai ka samu kudi ka turo min ko abinci mu samu mu saye ko ka turo min kudina idan ka samu mu sai abinci. Dan shiru yayi kamar mai nazarin magana na sai can naji muryan shi yana fadin naji zan turo idan na samu ya kashe wayan. Kallon juna mukayi dani da yar uwata kai kawai ta gyada tare da murmushi niko mamaki da takaici ya hanani magana. Hakkuri ta dinga bani inda ta hada min dan kayan abinci inzo dashi gida mu dan dafa da yara sai kwalla ya zubo min daga idona. Hawaye shar shar wani na bin wani a fuskana inda na kasa yin magana a lokacin saboda kunci da takaicin da ke cin zuciyata kamar ta fado min nake ji a lokacin. Na kasa fadin komai gare ta haka na mike zuwa gida sai Amira ne ta dauko dan kullin kayan da ta hadda min a cikin leda ta biyo bayana dashi zuwa gida. Ko da na shiga gida na dade zaune a falo na ina sakawa da kwancewa a zuciyata sai dai na rasa mafita a kan hakan. Ni, banga kudina, banga gadona, yanzun na tashi a tutar babu, ya yaudareni, ya cuce ni ya raba nida komai nawa na gado da wanda iyayyena dake raye sukai min na aure . Jamma,a ni haka tawa kaddaran tazo min da aure mayaudarin namiji wanda baida tausayi ko imani akan iyalin shi kanshi kawai ya sani a rayuwu. Nasan masu karatu duk kuna ganin laifi a wanan labarin sai dai ku sani Jamil ya yaudari mahaifin shi ya yaudari wasu maza yan uwan shi balle ni mace, macen ma kuma matar shi da yake ma kallon sakarai
Chapter 78 · 0% Book details