Sashe 13
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read
ya shigo dakin mu ya samay ni dashi. Ya dauka ya karanta sai da kanshi ya daure don ganin takardan da yayi da alama kuma takardan ya dade don har ya fara canza launi don ajiya. Dukan da naji ne a cikin barci ya falkar dani a gigice uban wa ya aiko maki da takardan nan yace dani sai lokcin na tuna da zancen wani takarda . Cikin inda inda nake fadin baba baba Jamilu ne na gida ya bani shi da zamu zo shine shine sai yau na gani ban san may ya rubuta a takardan ba nima. Ina karantawa ne ban gane ba barci ya dauke ni idon shi yai ja yace koma ki kwanta ya fita falo wurin mama da takardan a hannun shi yana fada. Yana fadin yaya tayi sakaci dani haka har maza suka fara min wasika har nawa nake da zan fara samun wasikun maza haka. Rantsuwan duniya mama tayi mai akan takarda yai fadan shi ya kare ya fice sai da safe ne mama take min fada akan takardan na nuna mata ban san ko na may ye ba nima. Mun koma garki wanan gidan yafi duk gidajen da muka zauna a baya girma sosai ga gari muna gani komai da zamuyi a saukake mukeyin shi gurin. Nan ma mun hadu da abokan arziki da dama inda mama har tana sa,a a nan tana sa kankara yan sari na zuwa suna kwashewa. Naci makarantar bowari Abuja na kwana don haka boarding zan tafi karatun secondry dina sai faman shiri ake muna don tafiyan na can din. Ban dade ba na tafi karanta inda kowa yasan dan aji daya irin wahalan da yake fuskanta farkon zuwan shi makaranta haka nima nayi ta fuskantar wanan daga mutane . Mun dawo hutun farko ina ta dokin ganin mahaifana da yan uwa na a gida sai na samu mama da ciki kuma a jikin ta. Bandai yi magana ba sai binta da kallo da nakeyi idan ta gilma har ya kai ta tsargu tayi min magana tace ai kila in haihu kuna makaranta wanan karon. Nace lah mama kina da ciki ne dakuwa tayi min na kama dariya tace wanan manyatacen kallon da kike min na maiye shi in ba cikin kike kallo ba. Na kama dariya ta wuce ina ta murnan zamu kara yawa a gidan mu muma har hutu ya kare na koma mama bata haihu ba. Da mahaifina yazo min visting yake fada min haihuwan mama ta samu namiji har anyi suna ko nayi ta murna da dokin son ganin jaririn da mama ta haifa din. Sai da aka samu hutu muka je gida inda mahaina ne ke zuwa dauka na sai gashi na ganshi yazo da mota. A hanya ne yake fada min ai yasai mota bayana itace wanan din da nake gani nayi ta murna ina bin motar da kallo a cikin farin ciki. Mun isa gida inda na samu mama ta shiryawa dawowan nawa haka muke cikin son juna da kauna na karbi dan kanina dake kama da mahaifin mu sak wurin kama. Yaron ya shiga raina sosai a wanan hutun mahaifin mu yazo gida sai dai wanan karon shi kadai ya samu zuwa bada mu yace sai mun samu long voccation zamu tafi tare da mama. Yaje gida yayi masu abin arziki sai dai shi baba halin yahudawa gare shi kyautan shi sai sa, a mutum ke samu wanda ba a zata ba yake samun alherin sa da zai dawo ya dawo tare da umma don taga inda muke zaune. Mun ji dadin zuwan umma din mama ta kama ina aka saka da umma din cikin jin dadi da so da kauna hutun mu ya kare a nan nabar kakan mu na koma makaranta. Yanzu Alhamdullahi iyayyen mu sun samu walwala kamar a gariki arzikin baba yake ga karin girma da yake samu a gurin aikin shi haka yasa muke tasowa a cikin jin dadi sosai. Bamu da sauran damuwa ko kadan a tare damu komai a wadace mukeyin shi watan umma uku a wurin su ta koma gida dauke da abin arziki mai yawa. Wanda hakan ya faranta ma mama rai sosai ta koma gida cikin jin dadi ga abubuwan da baba ya saya mata a can mota guda ya dauka zai kaita har gida ba tare da kowa ba.