Sashe 5
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Ina lungun momy da tazo daga lagos ganin gida can muke tarewa idan sunzo muna kallon su ita da yaranta don komai nasu burge mu yakeyi. Muna ganin shi bakon yanayi a gurin mu ga abincin su mai dadi da suke dafawa suna bamu duk da a gurin zubawan dan diban muna akeyi sai yaran ta ne zamu ga anzubawa cike a plate ga ruwan leda suna ci. Wanan bai damun mu don muna samu muna ci ko yayane daga gare su ga baki yan birnin garin mu masu shigowa wirin ta a duk lokacin da take gari gidan mu baya rabuwa da mutane. Sai idan ta koma kafa ke daukewa na kawayen ta har bamu son ta koma idan tazo gaskiya matar ba laifi don tayi sosai. Saboda abinta bai rufe mata ido ba ita ko masu zuwa wurin ta basu tafiya hakana sai da dan abu da take basu. Misalin sha biyun rana mama ta leko shiyan bayan sun gaisa ne ta kirani wai inzo zata aike ni na biyo ta a baya muka fito daga shiyan. Wanka tayi mun tare da shirya ni tana karasa girkin da takeyi bayan na saka rigan da nake maitan sakawa a jikina fuskana yana dauke da murmushin jin dadi. Nima na fito yar birni irin yaran mama na lagos ina daukin fita in zaga sako da lungun gidan nami kowa yaga na saka rigar da babu irin shi a gidan sai naji muryan mama na fadin. Tana zuba miyan yakuwan da yaji kuli kuli a cikin sa tace yar kabiru dauki abincin nan ki kaiwa umma idan kin dawo ki kaiwa inna nata cewan kishiyar mama dake gidan a wani gefe. Nace to mama ina daki ina kara gyara make up din fuskana dakyau irin ta yaran kauye banyi saurin mikewa na fito kamar yadda take bukata ba. Muryan ta na karaji tana fadin yi maza mana ki fito kada abincin yai huce na amsa da to mama gani tafe na fito dakin da sauri na. Ban samay ta a gurin ba ta dan kewaya ban daki ina zuwa na dauki tuwon Inna na kaiwa umma itama umma bata nan na dawo na dauki na umma nakai wa inna. Tana ta faman saka ma mama albarka damu na fito ina murna don yaba kyau riigan jikina da tayi bayan albarkan da take saka muna din. Ina dawowa daga aiken ne na samu fitina a shiyan mu umma tana masifa da mama akan may ta saka mata abinci cikin kwanon da take sakawa inna yau. Son son nayi na fara rabe rabe donn jin abinda mama tace laifina ne don ta saka ina daki ban fito ba ta zaga ban daki na zo na dauki na inna na kai mata kamar yar kabiru za a ce bata san kwanon ki ba kuma inna. Tana fada tana kallon gurin da nake labe shiyasa umma juyowa gare ni tace munafuka yar bakin ciki da hassada abincin naku ne baki son inci da kikai min bukulu. Na kara bin bangon dana ja na tsaya a gurin ina sauraren maganan su umma tace sai ki koma ki karbo min abinci na don ba hakkin ta bane ai. Da sauri mama tace don Allah umma kiyi hakkkuri sai in zuba maki wani mu muci wanan din na wuri ki ta juya zuwa daki ta dauko sabin samira a cikin kayan ta tazo ta hada ma umma wani abinci. Har lokacin umma na tsaye tana zagina da rawqn kan da take fadin a gurin uwata na kwaso shi sallaman inna daidai ne da kawowa umma abincin da mama tayi a shiyan. Tana fadin ke kuma kawata nace ki jirani in zo sai kika gudu ingo wanan kya sai alwa don nayi niya yasa na biyo ki dashi ai umma bata ji nauyin fadin . Dama shiyasa ta dauki abincina takai maki gashi ta samu biyar din yin kwalama ai a gurin ki maketaciyan banza kawai. Sororo inna tayi tana salalami tare da tafa hannayen ta tace shirmay yara ne sai hakkuri bari na dauko maki Allah yasa ban saka hannu a ciki ba. Umma tace wa haba dai ai uwarta ta biyani da wani mama ce tayi saurin gyara zancen umna wurin inna tana fadin inna gidimin yar kabiru ne kawai fa ga naki kwanon ta sani sai ta dauki na umma takai maki. Sai hakkuri inna ta kara fada tana jawo hannu na zuwa cikin gidan namu ina dan turje mata tajani zuwa gurin mahaifiyana tana fadin kada ki duke ta don Allah halin kurciya ne irin na yarinta. Baba kabaru ne ya shigo hannun shi rike da ledan bacco baka ya nufu mama dashi yana fadin ga sakon ku yanzu ya iso gare ni daga mijin ki. Umma dake tsaye tana mai wani kallo tunda ya tunkari mamana da ledan tace to isashe sai kuma akace idan dana yayo sako ita zaka dankawa a hannun ta ko ? Yace umma wanan ba sakon ki bane kayan amfanin su ne ya turo mata dashi banga abinda zakiyi da omo da sabulu ba tunda naga mun sai maki shekaran jiya ai. Tace wai kabiru in tambaye ka kai ka haifar min dan ko ni ko ita ta haifa min shi wai daidai lokacin mama ta karaso da ledan ta kai dakin umma ta girke mata. Baba kabiru bai tankata ba ya shige gurin shi wurin iyalin shi ya barta tana jidalinta tayi ta gaji ta koma ta bude ledan kayan ta zazage shi saman tabarman ta. Tanz buda tana yamutse fuskan ta ta tsince abinda take so ta kwalawa mama dake zaune a inda ta idar da sallah kira da sauri mamata mike ta tafi. Dunguro ledan tayi tana fadin ga shinan na debi nawa saura kuma ki kwashe ki rabawa mutane don neman suna a gurin su ki dawo kina kiran baki dashi daga baya. Murmushi mama tayi ta duka ta dauki ledan tana fadin angode kin dai ji abinda na fada maki umma ta kara maimaita kalamin ta ga mama. Tana shigowa daki naga ta zazage kayan ta kura masu ido sai ta girgiza kanta ta juya bata kara kallon kayan ba ban iya debe dayan biyu idan ba zargi nakeyi ba kuka maman mu tayi wanda ban san ko kukan maye ba a lokacin. Jin umma ta fita unguwa sai da aka dan jima kadan tabani sabulu guda guda in rabawa mutanen gidan namu in kai ko wani shiya. Sai yan kadan daga cikin kayan muka tsira dashi bayan rabawa biyun da umma tayi har ma nata yafi namu yawa ta dauka. Wasu sun karba wasu basu karba ba sai da tasa na mayar ma wanda basu karba din ba sai dai suna tambayana halan umma bata gidan ne ? Ince masu eh ta fita zuwa wankan jarirai sai suce bari suje suyi godiya kafin ta dawo baba kabiru najin umma ta fita ya shigo ya mikawa mama kudi yana fadin sai da ta diba ko ? Dariya mama tayi mai tare da fadin bata debi wani abu mai yawa ba ai ya kalli sauran kayan dake zube tsakar dakin mu ya gyada kai. Yace kiyi hakkuri saude kin dai san halin gwagon naki ai tace ba komai ai hakkin ta take ci koba yayan ka nake aure ba ai zata iya cin abina don yarta nake. Muna tsakar gida da yan gidan mu muna ta raye raye duk mun cika shiya da surutu kasamcewa yau alhamis bamu shiga islamiya. Tun kan ta karaso mukaji muryan ta tana fadin kai kai wanan wani iya shege ne haka ku rasa wurin da zakuyi gada sai shiyana duk fadin gidan nan da wajen shi. Wace tazo fita farko ta kaiwa rankwashe akai duk sauran suka ja da baya don sanin halin ta suka kalli juna don idan da sabo sun saba da halin umma. Gaba dayan mu har ni muka sheko da gudu mukai cikin ta ta rasa wanda zata doka a cikin mu muka fice muna dariya. Ni ta azawa laifin da cewa ai zan dawo zata kamani idan na shigo tana fada kamar wace ta samu sa,anta damu. Mama dai sai tukin tuwon ta take bata ce komai ba ta gama ta gyara gurin har lokacin ban shigo ba ga magariba daya gabato sai da ta kaiwa inna abinci ta gargado ni muka dawo gurin mu. Kwanci tashi har bakin gidan mu lokacin komawan su yayi suka fara shirin tafiya dama hutu suka zo muna da ganin gida. Ashe mama da karfin hali tana nan tana tara abinda zata bata sai da taga umma ta fita ta dauki galon din data tara mata man shanu ta nufi gurin su dashi. Tayi mamaki tace keda mijin ki bai gari kikai wanan wahalan tace ai yiwa kaine don ke ma haka kike dawai niya damu ko yaushe. Tace wanan yayi yawa tace babu komai Allah ya kara sadamu da alherin sa washe gari suka juya suka barmu da kewan su. Haka dai rayuwan mu ke gudana a kauyen mu tare da umma da mama zama ne na kuntatawa a tsakanin su kamar ba jinin ta bace mama. An wayi gari shamsiya ta tashi da zazzabi mai karfi hakan ya dauke ma mama hankali ta shiga damuwa da tunanen yadda zatayi da yarinyar. Gashi tasan halin umma ba dama ta nufe ta idan kuma ta je gurin wani a gidan ya zamay mata fitina kuma dole haka ta tasa yar a gaba har lokacin da baba kabiru ya shigo ta fito tana fada mashi. Da sauri yace subbahanallahi ina yarinyar take ta shiga daki ta dauko ta jin maganan su yasa umma fitowa daga dakin ta tana fadin . Lalai saude kin kai munafuka yanzu da nace ki jikawa yarinyar ganye baki jiki mata ba ashe tun dazu ga kabiru mai kudin banza kina jiran shi yazo ki daura mashi nauyin da ba nasa ba ko. Haba umma wanan wani irin magana ne haka ina saude ko ba dan uwana take aure ba zan iya ma diyan ta abinda zan ma nawa ai don Allah dai umma ki daina haka. Yana magana yana kokarin fita da yarinyar bayan fitan su ne ta koma kan mama tana fada inda