← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 33 OF 89

Sashe 33

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Wanan yawan maganan da umma ke ta yada min a gida tare da korafi ga kuma wanda na karbi kudin a hannun su na dan kara ina juyawa sun sakani a gaba akan in basu kudin su. Sai nayi shawaran zuwa birni gidan baba kabiru ko zan samu sauki a raina a ranan da nazo ban samu baba a gida yayi tafiya zuwa headquater jahar mu don halartan wani taro da zasuyi a can. Na samu taro na mutunci kamar yadda suka saba min idan nazo na kebe da kanne na ina tambayan lafiyan su da yanayin zaman su a gidan inda suka nuna min basu cikin wani damuwa. Da dare ne muna hira anty ta sako min zancen kudin dana ba wa jamil ya ce ya bace din take min fada akan hakan zafi naji sosai a raina da sukaji wanan maganan. Haka ya hasalani na rufe ido nayi mata tujaran da sai da ta kwanmace batayi min maganan ba don komawa nayi kamar wata zarara na dora hannu a kai na dinga yanka masu ihu a gida har makwabta sai da suka shigo tambayan ko lafiya. Ina fadin don anga iyayyen mu basu da raine ake muna wanan nuna bambanci haka komai nayi sai ace banyi daidai ba a rayuwana ranan dai ba karamin tujara nayiwa wanan matar mai kainan mu ba da zuciya daya akan dan maganan gyara kayan ka kawai da tayi min. Don duk abinda zai bata min jamil bani kaunan shi a lokacin a raina sai nake ganin zata iya tunzura baba kabiru wanda nake da hope akan shi zai aura min jamil mu zauna lafiya a lokacin. Sai daga baya ne naji kunyan abinda na aikata mata din don washe gari bata dauke ni da komai a ranta ba yadda na zata zata fita batun mu. Wanan abin da nayi mata ya dawo yana damuna har baba ya dawo na dauka zata fada mai sai banji yai min maganan komai ba. Har na gama kwanakin da zan masu don ban iya zama a inda babu masoyi na a lokacin na tattara na koma kauyen inda nake jin dadin rayuwa kowa na zuba min ido ina dauka sona suke a hakan da suke min. Zaman na kauye a lokacin dai gashi nan dai ne a gare ni don yanzu ban wani sana,an kwarai don duk ya cinye min jarin da nake dashi wanda ni a lokacin ban dauki hakan komai ba a rayuwa na. Zaman hakana ga maganganu suna zuwa wa baba kabiru a kaina don har ya kai yanzu ina zuwa dakin jamil muna hira a can wanda hakan a kauye wani abin magana ne sosai koma birni ne wace duk ta san kanta da mutuncin kanta ba zata aikata hakan ba. Haka yasa baba kabiru ya shiga nema min addmition na nursing school don kokarin da nake dashi burin shi shine mu zama wani abu a rayuwan mu da zamu iya rike kan mu a gaba. Alhamdullahi an sama min addimition din baba ya saya min komai da zan tafi inda ya aika min kwantsam in taso tafiya makarantana ya tashi. Hankalina ya tashi da jin wanan maganan don ban taba tsanmanin hakan ba don ni burina shine muyi aure da jamil ko zan huta da kalubalin rayuwan da nake fuskanta a yanzu. Sai ga zancen tafiya ya taso min inda jamil ya zugani sosai kan shi sam bai yarda da zancen zuwana makaranta ba ai idab son samu ne shi ya kamata da yake namiji ya tafi karo ilimi. Ganin ranshi ya baci sosai akan tafiyan hankalina ya daga sai dai babu yadda zanyi don dole in tafi din don ba zan iya musa ma iyayyena maza ba a lokacin. Ganin ban da mafita do ko ranan da zan tafi din da dare sai da muka kai ruwa rana dashi inda muka gama yanke sharawa na kamo hanya da safe zuwa birni. Na samu baba ya gama min sayayyan komai da zan bukata a karatuna har abinci da kayan girki komai ya saya min da na iso washe gari ne zamu tafi. Da dare washe gariin ne aka nemay ni aka rasa a gidan baba kabiru din inda hankalin su ya gama tashi sosai da nema na a garin sai dai babu labari na ko ina. Ran baba ya mugun baci ya buga gida ance banzo ba abin ya kara tayar mai da hankali sosai gashi nursing ba gurin wasa bane da za a dan daga min kafa . Basu ganni ba sai kwana biyu na dawo masu kamar wata gigitatta dani ina fama da matsanancin ciwon mara dake addabana. Gashi ban son in zauna a gurin da mutane suke zaune nafison in kebe gurin daya indinga tunanen halin rayuwan dana tsinci kaina. Anty tajini shiru tazo falo don ta dubani don kowa na cikin daki suna kallo wasu ma sunyi barci a lokacin halin tashin hankali ta samay ni ciki don ni ban san ta tsaya ba a kaina ina zaune sai buga kafa da rike mara da nakeyi ina ciza baki. Hankalin ta ya tashi da yanayin da ta riske ni din daki ta koma hankali a tashe tana fadawa kanwa ta summaiya da suke matukar dasawa da ita anya ba ciki yar uwarki ta zubar ba kuwa. Hankalin shamsiya yayi matukar tashi dajin zancen inda ta samay ni a falo hankali tashe tana tambayana may damuna na dai boye mata komai . Abinka da dan uwa take fada min abinda anty ta fada mata a kaina wanda jin hakan yayi matukar girgizani don ban sauka kowa ya fahinci halin da nake ciki ba. Ashe abin ba haka bane duk wata uwa ta gari tana saka ido akan yarta tasan duk takon da yarta ke takawa nan dai na hau fadan karya inda nake shiga ba nan nake fita ba sai da sumaiya ta taushe ni a kan zancen kada aji ace kuma wani abu. Ido kawai baba ya saka min don bai iya cewa dani komai ba sai idon da ya saka min a gidan sai dai banyi zaton bacin rashin yakai haka dani ba sai lokacin dana tashi komawa kauye yace ai na dawo nan ke nan don babu inda zan tafi kuma mutane suna zagin shi. Hankalina ya daga sosai da jin hakan na shiga jin haushin kowa har kannena takaicin su nake ji a raina kan wanan zancen. Dole ina ji ina gani zama na ya dawo a hannun baba kabiru na bar kauyen da sana,ata na dawo muka hade da yan uwa na wanda hakan yayi wa umma dadi a ranta sosai. Don tana ganin rabuwana da Jamil yazo ke nan a lokacin don taji komai ta kuma san halin da ake ciki sai dai zaman ta na kaka a gare ni ba yadda zatayi ne ga tsufan da ya kamata a lokacin . Zaman dai gashinan ba wani dadi har lokacin da yar uwata ta kare karatun ta muna zaune tare inda muna samun manema sai dai ni har lokacin ba wanda ya kwanta min a raina kamar Jamil dina. Kwatsam sai jamil shima ya tattaro ya dawo birni da zama gidan wanan abokin mahaifin nasa haka yai min dadi so sai a raina don masoyina da ke zaune yanzu a kusa dani. Tsagumi bai kare ba ga bakunan yan kauyen mu don har nan din ma basu barmu ba don maganan dayace koda yaushe shine su baba kabir sun cinye muna gadon kudin mu. Maganan bai yi zafi ba sai lokacin da dan kudin birnewan da gwaunati ke bayarwa na mahaifina da ya fito inda aka raba muna aka ware ma mahaifiyar shi nata. Nan mutane suka shiga tofa albarkacin bakin su wai kudin yafi haka yawa an dai san yadda akayi dasu ne inda mu kuma jin hakan ya fara daga muna hankali. Bamuyi kallon irin fadi tashin da baba kabiru yakeyi akan komai na mahaifin namu ya fito ba sai dai burin mu muji ina dukiyan iyayyen mu ya shiga. Wanda Jamil na daya daga cikin masu hasasa muna wuta akan hakan har takai zugan su ya shiga kawunan mu sosai mun fara dauka don haka muka tafi kauye muka samu umma kan muna son jin inda motar mahaifin mu da sauran dukiyan shi suke. Wanda hakan ba shawaran kowa bane sai nawa ni dake daukan zuga sai kanina Baffa da yanzu ya tasa shima burin shi na akan son jin komai don mun zugu da yawa a gurin mutane. Kakan mu batayi sanyi a gwiwa ba ta aika iyayyen mu maza suka zo ta tara su inda ta fito masu da maganan da muka zo mata dashi. Kai baba kabiru ya jijiga yana fadin Allahu akabar da yaran nan sun san komai akan dukiya da basuyi muna wanan fahintar ba sai dai yanzu a kira su muyi masu bayanin komai don suji su sani. Umma tasa a kiramu muka shigo idona ya bushe banjin nauyi kowa a cikin su a lokacin ni dai burina kawai in san inda dukiyan mu ya shiga don Jamil yace idan mun samu zamu iya rufawa kan mu asiri muyi aure da dukiyan. Ga wautana da rashin wayona da mahaifana suke kiramin kullun a lokacin da suke a raye sai nake ganin ai yin hakan shine daidai a gare mu. Baba kabiru ne ya fara da addua tare da fadin umma ta fada muna maganan da kuka samay ta dashi sai dai ina son ku sani mu bamu ci kwandala a cikin dukiyan mahaifin ku ba. Abinda bamu son ku sani yau ya zama dole gare ku ku sani don mahaifin ku ya mutu da bashin banki a tare dashi. Wanan nauyin ne muke ta kokarin ganin mun sauke a kanshi da abinda kuke hasashen mun ciye maku din nan dai ya shiga yi muna bayanin inda ya dora da fadin yanzu kuma Alhamdullahi don mun sauke mashi wanan nauyin a kan shi mun biya bankin bashin shi da kudin gida da motan da muka sayar nashi. Da fatan zaku fahince mu yanzu tsuru tsuru mukayi a dakin babu wanda ke iya magana a cikin mu lokacin ga nauyin da mukaje nasu kan kokarin da suke akan mahaifin mu din. Baba musa ya dora
Chapter 33 · 0% Book details