← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 76 OF 89

Sashe 76

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 6 min read

ita shi. Daga waje kuma ina jin tana fadin ke nake jira fa don akwai inda zan tafi daga nan din ban samu kulawa daga gare shi ba dole na fito na bata hakkuri zan kawo mata zuwa anjima ta tafi. Ina aikin da nakeyi ina tunane a raina inda zan samo kudi in biyata tunda ni ta sani , har na gama ban samo mafita a raina. Ina gamawa nayi wanka na shirya lokacin shi har ya karya yayi sakkon fita daga gidan ya barni a zato shima neman kudin ya fita yi don mu biya bashin. Nima dai ban zauna ba fita nayi zuwa gidan yar uwata yar gurin baba kabir don bamu da nisa nida ita can naje na fada mata halin da nake ciki da kudin mutane. Sai da tayi min kwakwazon don may nasan halin mijina zan yarda in biye mashi inje ci mai bashi duk nassn ai ba biyana zaiyi ba . Da kyat da lalami ta aramin dubu biyar bayan nayi mata alkawarin zan biyata a cikin sati biyu abinka da dan uwa ganin yadda nake kuka ta tausaya min ta bani aro ban ko shiga gida ba da kudin naje nakaiwa matar kudin ta saura kuma nadan sayo abin bukatan gida dashi. Shiko bai shigo ba don yasan ba abinda zamu dafa da rana don haka bai damu ba ko yaya zanyi da yarana. Sai dare sosai ya shigo gidan yana wani cin magani dani nima ban kula shi ba hakana na kwanta na kyale shi. Ko tashin zancen kudin matar bai min ba ga kwanakin da na dauki alkawari wa yar uwata yana karasowa na bata kudin ta. Hankalina ya tashi sosai don haka na yanke shawaran zuwa gidan mu wurin anty don ta rokan min kanne na su bani wani abu in samu in biyata kudin ta. Da naje gidan kunya da nauyi ya hana in mata magana kamar yadda nayi niya sai ma itace taga damuwa a tare dani take tambayana ? Ko lafiya ta ganni a haka nake cewa ganinan dai anty sai kuma na fashe mata da kuka don ban san ta inda zan fara mata bayanin abinda ke tafe dani. Hakkuri ta shiga bani tana fadin hakkuri zakiyi hadiza matsalan mijin ki kin saba dashi nace cikin kuka anty bashi yasa naje naci yaki biya. Nan dai na kwashe komai na fada mata muna cikin magana ne sai ga kanni ya shigo dakin kallo daya yai min ya kawar da kan shi gareni. Don yanzu haushina suke ji suma ga shi sun gane Jamil yayi amfani damu mun saba da iyayyen mu masu kaunan mu tsakani da Allah. Don yanzu shekaru sun kora sun yi wayau fahintar wani abu daga iyayyen namu don haka suke jin haushi har dani baki daya. Anty ce ta iya mai magana akan abinda ke faruwa dani da Jamil din yace cikin tsaki anty bar wanan da kike gani ko yanzu ta samu kudi kara bashi zatayi wallahi. Ai tasan halin mijinta take biye mashi tasan mayaudari ne macuci tunda anyi daya anyi biyu yanzu jira yake na uku yazo ya cinye shike nan ya korata. Naji haushi maganan shi don ina neman abu a gurin su ban tsaya ya fada min maganan banza ba nan na haushi nima don ban son mutum yai min zancen mutuwan aure na ko kadan. Tunda nasan kowa hakkuri yake da auren shi kowa kuma da irin kaddaran da yake gani ga rayuwan shi ni da wanan na dogara na bashi amsa. Anty ce ta katse ni da fadin in bi a sannu tunda nema abu muke a hannun shi dole na sassauta harshena gareshi. Da kyat da sudin goshi ya yarda zai bani amma da sunan aro idan na samu zan biya shi abinshi sai bayan ya yarda ne ya kawo maganan kudin hayan da Jamil din ke cunyewa yanzu. Don lokaci ya kusa na biyan kudin yan hayan gidan mu don ba zasu yarda ina cinye kudi ko wani shekara ba da mijina mu kadai. Yace karshen shi ma ba nike cin kudin ba shine mai cinyewa ya kyale kowa ranan dai kanina ya fada min magana iya son ran shi sai da anty ta taushe ni. Na yace in tafi idan ya ciro kudin zai kawo min har gida da yamma ina komawa gida na samu Jamil yana cika yana batsewa wai na fita yawo na bar gida ba kowa. Kyaleshi nayi ban fada mai abinda naje yi ba don in har ya sani sai yasan yadda yayi yaci wani abu a cikin dubu goman da za a aramin din nan. Do haka naja bakina nayi shiru inda nayi sa, a koda kani yazo ya dan fita har ya bani kudin na boye bai gidan. Sai dai kafin ya tafi ya shigo ya samay mu muna hira ya zauna suka gaisa a cikin hiran ne yake tambayan wai yaushe ne sauran kudin mu zai fito har yanzu shiru. Amsan da Baffa di ya bashi ni kaina naji mamaki don cewa yayi dashi kudi tunda suna nan ko yaushe sukazo daidai ne. Don masu kudin ma basu damu kanar masu son cin banza ba ai yana fadi haka ya tashi yace zai tafi nayi mai sallama shi bai tanka shi ba. Yana fita Jamil din yace naga yanzu yaron nan yana son ya raina ni ko don yaga na damu da damuwan ku ne ko yana ganin yanzu ya kawo karfi ne shi ? Ni dai ban bashi amsa ba na share shi yaci gaba da fadin ni zai cewa masu son banza ke nan mune masu jira muci banza ke nan ko ? Ni abu ya damay ni ban tsaya bin ta nasa ba don tunanen maganan yaron kan kudin hayan da yayiwa anty ya damay ni a raina sosai . Tunda yace basu yafe min ba tunda ba ni kadai keda gadon kudin ba balle mijina yai ta karbewa yana ci shi kadai. Don haka wanan shekaran shi zai karbi kudin da kanshi gurin yan hayan nako san akwai tsiya da Jamil ke nan tunda ba kunya ke gare shi ba kan kudi da kowa yana ja tunda shi ya zama cima zaune. Ina samu kudin nan washe gari naje na kaiwa yar uwata kudin ta nan ta dorani ga sana,an da zanyi da sauran canji na daya rage min cikin dubu goman da akace an ara min ne. Na fara juyawa a hankali tunda banda komai ya karbe duk dan wanda nake juyawa a baya . Dan zaman ma da yake yanzu a gida sai ya gundure ni na kwammace ace ya fita din da yake yi yanzu zuwa wani gari neman kudi. Ko lalura zai rage min a gidan don na gane nisa da nisa dashi yanzu ya fiye min dadi da idan yana gari bai yi tafiya ba.
Chapter 76 · 0% Book details