← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 55 OF 89

Sashe 55

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 6 min read

ba inda ya nuna na more ma kudin ko kadan. Muna a haka ne rikici na da uwar mijina yaki ci yaki karewa a tsakanin mu ga Jamil ya matsa min akan shifa zaman su a gidan damu ta ishe shi yanzu don suna hanashi walawa a gida. Haka yasa na fara daure mata fuska ina mata abinda ban mata a da can baya yanzu hankalin ta ya tashi har yakai ga taje ta nemi wani gida don su kama haya su koma ciki. Ina murna zamu rabu da kaya idan sun tashi wanda ban hango illan yin hakan da nai masu ba wanda da sunana suka tashi daga gidan bada sunan dan su Jamil ba. Don ni sukace ina masu wulakanci tunda ni yake izawa inyi mata rashin mutunci a fili shiko yana nokewa kamar bai sani ba. Yan uwana kaf sun dauke kafan su da gidan mu yanzu sun mayar da hankalin su gurin iyayye su sun ware mu inda muma muka kara dinkwa da junan mu a tsakanin mu. Jamil ya bamu shawara muyi dabara karbe kudade su Baffa dake hannun baba kabir da sunan ajiya kada azo a nema a samu babu su a cewan sa wai gwano baya jin warin kanshi ashe. Ni ga nawa tun ba akai ko ina ba duk ya halaka min su sai kamay kamay nake wa mutane da yan hayan gidan mu suka fahinci komai ya kare min sai habaici ya tashi tsakani na dasu. Wata daya da muke shiri ne take fada min gaskiya ta kebe dani tana fadin kinyi wauta hadiza may yakaiki bawa namiji kudi irin haka masu yawa. Na miji fa baida tabbas ko kadan baki gudun nan gaba ya karo maki kishiya da kudin naki may zaki fada nan dai tayi min nasiha sosai wanda yasa ni natsuwa. Ta nuna min abinda mukai wa kanin mahaifin mu mai kaunar mu bamuyi daidai ba wallahi gara inje in nemi gafaran shi kan abinda mukai mai mu koma daidai da iyalin shi dake fushi damu. Don ko wane ma haka ya faru dashi fushi zai dauka dakai tace da bakin ki kike fada min irin yadda yake nuna maku banbanci da iyalinshi har yau basu taba nuna jin zafin hakan ba don may zaku saka mai da hakan akan kudi ku ? Ta dai yi min nasihs sosai a matsayin ta na mai kaunata a gidan kuma ba laifi nayi kamar yadda tace din inyi don naje mun sasanta da yan gidan mu an fahinci juna don sun gane muna amfani ne da zugin mazajen mu. Don kanwata har ta fini daukan zugin mijin ta yanzu nake gani do ko ni banjin dadin ta bansan kuma irin yanayin da suke ciki da mijin ta ba a gidan su. Don ko naje ban gane komai haka nake juyowa in dawo don bata bari in fahinci komai sai dai na gane itama din duk abinda ya kwaso ni shiya kwaso ta yanzu don babu kudin a hannun ta kuma. Itama mijin ta ya kashe sunyi wani abinda kudin tunda kudin nata a hannun mijin nata suka gashi da daure fuska ga kowa bai sakin fuska balle ya bada kafa a fada mai wani magana. Har gara Jamil don shi yana dan wasa da yan uwana idan yaso yana kuma ziyaran iyayyena idan ya tashi yaso don kan shi yana yi. Ranan dai da talauci ya damay ni na shirya naje gidan wurin ta neman dan dubu daya in rike don lalurar yau da kullun don a takure nake ba walwala. Sai nake ganin ita ta dan rage da wani abu a gurin ta sai cewa tayi min wanan kudin fa kamar yadda nima nake fadin babu su itama gaskiya babu su a hannun ta yanzu don ko abinda zasu karya yau uwar mijin tane ta aiko masu dashi. Ban san lojacin da na bude baki nace sumaiyaay kikayi da kudi ki ba ni ansan mijina ne ya cinye min nawa naki fa ta hauni da fada tana daure fuska akan may zanzo in tasa ta gaba da tambaya kudi dai ne an bawa kowa hakkin sa ai. Ban dai gane komai ba haka na bar wurin ta don mijin ta da ya dawo yana wani daure fuska kamar yaji zancen mu da ita dama ya shigo yana shan kamshi daya ganni a gidan. Ban san dadin firan da ya kwashe wurin Jamil ba na kwashe zancen da mukayi da yar hayan gidan mu na fada mai ranan tun wanan lokacin ya matsa akan lalai sai na sallamay ta daga gidan din tana saka muna ido ga al,amuran mu dashi. Ban so haka ba don a wurin ta nake dan samun shawaran karuwa sai na rasa yadda zan mata magana kan matsin da yake min a kan su gashi shida mijin ta suna shiri sosai a gidan na gani. Amma haka yake matsa min a daki akan in kore su su bar gidan nan ko raina ya baci dashi banda yadda zanyi haka na daure na fara nuna mata wasu halaye na daban da ban saba nuna mata ba sai data ga haka ta fara jan jikin ta dani itama. Har ya kaimu da fara sa,insa a tsakanin mu in rufe ido in mata cin mutunci ala dole ni ga maigida sai fadi nake sufita su ba ni gidana tunda bada su aka sai muna ba. Takan ce ai nima saukin abin bani kadai ke da gidan ba namu na taro ne na algaje ni kadai sai munafukin miji dake yaudarana don banda wayo ya cinye min komai nawa tunda ina sakara yana fita yana neman mata da kudina. Wanan zancen ya bata min rai sosai nake jin zafi a raina kan abinda ta fada min sai ya bata min da Jamil din da ita a lokaci guda. Ko da ya shigo nan na haushi da sababi ina jidali kan zancen da maman Ahmed ta fada min nasa nake fadin idan har mata ya nema da kudina ba zan yafe mai ba. Wanan magana ya bata mashi rai sosai yasa ya kara fushi da mama Ahmed din kan yau ba gobe ba zasu tashi gidan sai da maigidan ta yaje gurin iyayye na akai muna magana na hakkura da zancen sai idan sun samu gida don mijin yana gina bai karasa ba lokacin. Wanan yasa muka dan samu saukin fitinan mu sai dai sama sama muka koma da ita a gidan ba wanan dogon shirin da mukeyi da ita. Ya koma ban wani dogon shiri da kowa a gidan yanzu don duk sun hada min kai ban gane masu nima ban shiga shirgin su dana yaran su kamar yadda mukeyi a baya.
Chapter 55 · 0% Book details