← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 36 OF 89

Sashe 36

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Zaman mu da umma a gidan baba kabiru ba tsangwama ko kadan yadda takewa kowa a cikin jikokin ta haka muma muke da ita har ina mamakin ta. A cikin wanan yanayin ne Jamil ya labartawa wani dan mutumin da yake zaune a gidan shi labarin mu dana mahaifin mu shima yaji yana ra,ayin kanwata summaiya ya samu wanan gara basan na mahaifin mu da jamil ke labarta mai zamu samu. Haka yayi dabaran daya hada sumaiya da wanan dan gidan da yake zaune dasu yazo gurin summaiya da sunan soyayya a gare ta. Sai dai shi wanan ba rago bane kamar jamil dina don yana matakin kare karatun digree din shi a lokacin. Batai wani na,am da shi ba a lokacin don ta gane manufa hakan a gareta don anty amarya ta hasko dabaran su a gare mu bata kuma boye muna ba ta fada muna kai tsaye abinda suke nufi damu din. Sai dai irin matsin da yaron keyi na zuwa wurin kanwar tawa tare da dadin bakin jamil yasa har take dan sauraron shi don yace da zuciya daya yake sonta a yadda yace mata din . Wai yana jin labarin ta yaji hankalin shi ya kwanta da ita sosai saboda tausayin mune yaji yana matukar son ta a ran shi don rashin mahaifan mu da mukayi. Sannu a hankali suka kulle dashi har ta fara samun kanta sai dai korafin anty a kan haka da tashin hankalin ta yasa tana dan ja da baya ga zancen shi. Tafini farin jini don tafini kira sosai don ni irin matan nan ne na fada maku tun baya ni kwalliya ma bai damay ni ba haka mukan ta kwasa da anty akan gyara irin na yan mata kullun muna zaune da daurin zani a gaba a gida wanda take mana masifa akan hakan idan tana gida idan ko ranan aiki ne tana gurin aikinta sai mu zauna hakana a gidan ba wani gyaran jiki. Don muna ganin ai ba inda muke zuwa banda gida gyaran may zamuyi itako anty yar gayece ta karshe gyara dai na matan zamani ba wanda bata iya ba. Hakama girki da gyaran muhallinta bata sakaci da wanan don idan mutum yana zaune da ita sai yaso ya ketaci kanshi a kan gyara idan kaji fadan ta damu akan rashin gyara ne da bamu yi don haka muka saba mu tun a can da muka taso. Dole ta kawo ido tasa muna hakana a yadda ta ganmu kamar wasu yan kauye damu ga yan uwanta daga Niger state suna yawan zuwa gurinta duk yan gayune su amma mu hakan duk bai damay mu ba. Wata rana umma ta tashi da ciwo mai tsanani a gidan wanda kowa na gidan hankalin shi ya tashi sosai da ciwon nata. Allah da ikon shi ana treating din ta ta samu lafiya sai kuma gudawa ya biyo bayan samun lafiyan nata nan ma hankalin iyayyen namu ya tashi sosai da ciwon na umma da takeyi. Kwana uku tana fama da wanan laluran ranan muna barci da dare anty ta tayar damu daga barcin tana fadin mu tashi mu ga halin da kakan mu ke ciki a lokacin. Abin gwanin ban tausayi mun falka mu samay ta a wani irin yanayi sai sambatun take faman yi haka anty tayi dubaran karantu mata kalman shada sai take amsawa daga inda take din gashi a lokacin baba yayi tafiya don ganin umma ta samu lafiya. Ba wani shirine tsakanin umma da anty amarya ba don bata ra,ayin ta ko kadan haka dai anty ke shanye halin umma har Allah yasa ta hayyayafa a gidan tare da baba kabiru din don shi yana son matar shi. Kiri kiri umma zata nuna bata son ta bata son diyan ta data haifa a gidan da baba kabiru din sai uwar gidan ta yar asalin kauyen namu itace mata a gurin umma. Idan baku manta ba na fada maki haka mahaifiyata ta sha wanan faman da umma lokacin da take zaune a kauye akan uwargidan na baba kabir da umma keji tankar itace ta haifa ta sa cikin ta a duniya. Don har mutane na fadin ba a banza ta barta ba kan wanan halin da take nunawa da diyan ta ma sune jikokin da umma tafi so a cikin jikoki gaba daya. Idan anty amarya taji sun shagala da zancen da bata ji daga inda muke a zaune sai ta fadi kalman shahada sai umna din ta karba daga cikin dakin mama din da take kwance. Hankalin umma yayi matukar tashi sosai ta mike ta fita zuwa makwabta a kwai wani tsoho da muke makwabtaka dashi da wani ba haushe a uguwar duk sauran yarbawa ne da iyamurai don sabon uguwane sosai gurin ba mai kula harkan wani a cikin unguwan. Tsohon yazo ya duba umma shima hankalin shi yayi matukar tashi sosai da ganin yanayin na umma dayayi yace yanzu dare ne babu yadda za a yi da an kaita asibiti. Baifi awa daya da fita ba anty amarya kuma bata fasa fadan kalman shahadan da take fadi ba a bakin ta Allah ya karbi ran umma take a wurin . Wani sabon tasgin hankali kuma a gare mu mun koma ba uwa ba uba babu kakan da muke dan rabawa muji sanyin rashin iyayyen mu a gurin ta. Haka muna kallo washe gari aka kawar da umma zuwa makwancinta ubangiji yasa sun huta da duk kan musulmin Allah da suka rigamu idan namu yazo mu cika da imanin ubanginjin mu Amin. Anyi zaman uku aka watse lafiya tare da jimamay rashin umma da mukayi lokacin bamu da kowa sai Allah sai baba kabir da matar shi anty da ta rikemu amana a hannun ta. Do muna ganin tafi muna duk yan uwa a gurin mu tunda ta zauna damu da zuciya daya sai muka kara mayar da ita uwa sosai a gare mu da muke da ita yanzu a duniya. Soyayyan mu da jamil yana nan duk da ba wani karuwa da nake samu a gurin shi a matsayin na wace zai aura sai dai zuciyata da gangan jikina ya yarda dashi dari bisa dari sosai. Itama sumaiya duk da farin jinin da take dashi na samari hankalinta yafi karkata akan wanan usman din da jamil ya hada ta dashi saboda karin kwarin gwiwan da nake bata . Wanda ita ma anty takan ce ai gara dashi din yafi mata jamil do shi yana da ilimi ana sa ran alheri a gare shi nan gaba don ilimin da yake dashi din. Ya gama ya jona karatun master din shi duk suna tare da summaiya din har lokacin dole kowa ya kawo ido ta zuba muna don babu daman magana sai mutane damu suce ai don basu suka haife mu bane suke muna hakan. Shinedalili su na saka muna ido a gidan ba tare da sun matsa muna ba sai dai yawan magana dake damun mahaifin mu din akan mu tundai ni na naki aure ya sa min ido yasa baba kabir din amincewa da jamil din yanzu. Sai dai kuma inda matsalan yake babu wani zancen auren shi a gidan su don bai da wani sana,a takamaimai da yake amma koda yaushe zaka ganshi fes dashi kamar dan wani gwauna ne don karya. Ban taba hango illan hakan da mutane ke gani ba akan Jamil din asalima ni dadin ganin shi hakan nake ji don ina ganin na haska a gari ai tunda ina da mutum kamar Jamil a tare dani. Ana cikin haka ne mahaifin jamil ya tattaro ya dawo birni da zama gaba daya da iyalan shi suna zaune a gidan da yayan jamil din ya gina don yana aikin soja ne shi. Yasa ya dankara gida a birni sai mahaifan nasu suka tare a ciki kanin shi kuma yai aure ya zauna tare da matar nasa a ciki baba kabir yana daukan shi wa a gurin shi sosai don alakan zamantakewan tare tun iyayye da kakanni a gida. Yaje ya samay shi akan zancen namu sai mahaifin nasa yake fadin shikan ina zai masa aure yanzu baida wani cikakken sana,a da yakeyi. Baba kabir ya dawo gida da bacin rai babu yadda zaiyi ya zuba min ido maganan ta zauna a kan hakan yace in fito da wani ya aura min tunda ga abinda mahaifan jamil din suka ce. Anan inda akai maganar na bar zancen ban kara bi ta kan zancen ba zai zo wuna mu sha hiran mu ya tafi har dai abin ya ishi baba ya nemi shawaran yan uwan shi akan zancen namu da jamil din. Baba musa yace idan ban fitar da wani ba ya aurani ga wanda yake so mana ai dole in zauna ko ban wa Allah tunda na zama abinda na zama a cikin dangi. Shi bai taba ganin yarinya mai taurin kai irina ba a rayunwan shi sanyi hali irin na baba kabir din ya sa ya daga min kafa ga zancen. Ina zaune gida ga masifa da kanne na a gidan ban bar diyan su sun sakata su wala yanzu za a ji mu dasu wanan abin yana yawan bakanta ran baba kabir sosai sai dai bai yarda yayi ko ayi muna abinda ran mu zai baci. Da abin ya ishe shine ya tayar da yan hayan gidan mu da aka saya muna daga baya ya shiga gyaran gidan gadan gadan sai da ya kusa gamawa ne yake fadin ya tsayar da ranan bukin mu da jamil. Ya samu iyayyen jamil ya sheda masu basuyi wani na,am da zancen ba sai dai a gaban shi matan mahaifin nashi sun nuna farin cikin su a gaban shi. Babu kuya mahaifin Jamil bayan kwana biyu ya aika yana neman baba kabir da shawara bai ki zuwa ba ya samu lokaci yaje gurin amsa kiran mahaifin Jamil din. Sai cewa yayi da baba yana nema alfarma akan maganan da yazo mai da ita yana son gidan da zamu zauna da jamil din a gyara masu dayan part din amaryan shi ta zauna a ciki don barin yara su kaidai haka bai da alfanu. Kawaici irin na baba kabir sai baiki hakan ba amma yayi mamaki da jin hakan daga gurin dattijon da ya
Chapter 36 · 0% Book details