← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 70 OF 89

Sashe 70

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din. Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja. Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan. Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana lafiya dai ko ? Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin wai Allah dai ya jikan baba. Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta. Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo mashi a baki ba a lokacin. Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa. Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun mu har da fadin zai fito dani gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda shi. Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin. Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba yan kayan kwalama ba da sauran su. Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon. Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo. Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours. Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma shi bai shiga ba lokacin. Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan gida yaki shiga daga ciki. Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan . Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin wanan zancen. Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu. A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu. Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta iya magana lokacin. Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke. Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice zamu faso gari ke nan sosai wanan karon. Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai da ya kusanceni ranan . Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki. Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga yadda zasuyi muna dashi . Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala daga cikin kason mu din. Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna yadda sukaga dama da hakkin mu . Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil yana cewa. Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya. Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa yanzu yayi hankali ne. Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin . Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin. Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ? Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu. Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi. Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa.
Chapter 70 · 0% Book details