← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 51 OF 89

Sashe 51

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

watsewa su dafa maka ya juyo cikin mamaki yana kallo na . Kafin ya furta wani abu muryan mahaifin shi ne yake kiran shi yasa shi juyawa a hasale ya fice daga falon zuwa karba kiran mahaifin nasa. Ni dai ban san yadda akayi ba sai gashi ya dawo yana cicika yana fadin ni hussai zata dora wa sheri wai ke harda yarda da maganan ta. Wallahi sai sun bar gidan nan a cikin kwanan nan kuwa nace sherin may kai kadai ne namiji a gidan nan da ba a dorawa sauran sheri ba sai kai kadai da yake yasan baida gaskiya sai ya shiga yan kamay kamay yana fada har na fara yarda da abinda yake fadi din. Mun danyi zaman sama sama dashi na kwana biyu sai ranan naga ya dawo da wuri yana wani haba haba dani da yar goyona Amira . Abinda bai saba yi min ba ni kuma rashin wayau ya hanani gane halin shi da sai wani abin arziki zai faru dani yake min hakan da naga yanayi din zaiyi. Ashe sun hadu da kanina a waje yake fada mai ai mutumin nan ya kira baba yace mu sa rai a cikin sabon wata zamu samu kudin mu insha Allahu. Lokacin har na kashe yan kaya haihuwana da anty tasa aka dinka min dana haihu har sun fara shan ruwa sosai banda zanin shiga jama,a na kwarai a dakina. Sai daga bayane yake labarta min abinda ake ciki akan kudin yake fadin idan kudi sun zo sai mu gyara dakin mu muyi wanan muyi wancan. Ni dai kallon shi nakeyi sai da ya kare nace ni duk ba wanan ba indai samu abinyin sana,a daga ciki shine burina a yanzu don zama haka ba sana,a ya fara isata a gidan . Dan dadin bakin yace ki kwantar da hankalin ki sana,a ai kamar kinyi kin gama nima kaina sana, an nake son yi yanzu sosai don zaman nan haka ya isheni sosai. Yan matan gidan mu ne suka kawo min ziyara ashe suna kule da zancen neman kanwar yar hayan da naje masu da labari yayi ranan dai sai da sukayi shi ba dadi da matar gidan namu inda suka zage ta fes daga ita har yar uwan nata da take kurin yana nema din. Ya samu labari sai dai ban san a inda yaji labarin hakan ba nan yazo da cin mutunci wai shi nake son inwa tonon asiri da har zan gyato yan uwa suzo har gida suyi cin mutunci haka. Sai daga baya nake ji wata yar gidan dake haya take fada min wai matar mahaifin shi ne ta tare shi waje ta labarta mai komai daya faru. Wanan bai damay ni ba don cewa nayi idan da baiyi ba ai da hakan bai faru ba nima tan uwa sun kwatar min yanci ne a gurin su su san ba banza nake ba. Yayi fushin shi ya gaji ya sake hakan bai sa ya fasa halin shi ba kullu fes yake kamar wani mai zuwa office dashi haka zai dauki wanka ya fice daga gidan sai wani lokaci ya dawo. A cikin haka ne bukin kanwata Sumaiya ya kawo jiki ana ta shirin buki iyaka ta ido sai kamay kamay danakeyi do banda wani katabus a gurin sha,anin tunda banda shi. An nuna mata gata sosai don an mata abinda ko rabin shi ba ai min ba don komai nata yafi nawa tsada sosai suma gida mijin sun nuna nasu bajintan sosai don set din akwatuna ne da zanuwa ciki masu tsada sosai suka saka mata. Ana cikin harka bukin ne na dawo gida don daukan kayan dana manta na rista matar mahaifin Jamil mama suna gulma da yan hayan gidana inda suke shiga banan suke fita ba mama harda cewa wai ni din ba sa,an auren Jamil bace matsa mashi akayi ya aure ni. Nan kan idona ya rufe ranan na mayar mata da ansa sosai ga maganan ta inda ta shiga kamay kamay wai nayi mata kage da sheri ba abinda tace ke nan ba ita. Nan dai mukayishi ba dadi na dawo gidan mu ina labartawa yan uwana abinda mama din tayi min aiko suka shiga yaba bakar magana a kanta . Kowa da irin abinda yake fadi mai zafi don bacin rai can kuma gida jamil na dawowa ra samay shi da kukan munafunci wai nayi mata tono asiri don anga bata haihu da mahaifin su ba ake mata haka. Shiko Jamil ya daure min ko dana dawo yaki min magana nima na daure mai da safe na shirya zan tafi gidan mu ya hau bala,i wai na raina shi da iyayyen shi don naga basu da hali yasa nake masu wulakanci shi sai ya rabu dani ba komai bane a guri shi. Nima nayi zuciya ranan nace arabu din mana sai may ko shi ya samu ana gulman shi yadda na samu mama da yan haya suna gulma na dole ya dauki mataki. Yace ai shi ba haka ta fada mai ba nace ai ba zata fada ma gaskiya ba don tasan da kazo baka binkici zaka hauni da fada nan dai na kwashe yadda akayi na labarta mai komai. Yace ita mama din ke fadin hakan nace kwarai kuwa don da kunne na naji ba wani ne ya labarta min ba yace yayi kyau nan ya fice nima na rufe zuwa gidan mu wurin bukin yar uwata ta haihuwa. Anyi buki lafiya ankai amarya lafiya da na dawone naga canji sosai a gurin iyayyen mijina sai wata yar hayan ne take labarta min abinda ya faru a bayana tsakanin su da dan su. Inda tace Jamil din ya goyi bayana don anyi turke turke a gidan tun wanan lokaci ta fara tayar da hankalin ta a kan zama damu a gidan muka koma kamar kishiyoyi da ita kuma. Zaman kanwata da mijin ta kowa yana yabawa don zamane na mutunci sosai sukeyi ko ni din banda matsalan wurin abinci don muna cin maikyau mu sha mai kyau. Sai dai ta fannin sutura ne nake ganin ba daidai ba gare ni ga dakina ko macen data dade da aure ta bani lafiya har kunyan baki so zo min dakin nake ji sai in kama kamay kamay idan nayi baki. Shiko gogon haka bai damun shi kullun a cikin jiran kudin magaifin mu su fito yake a gyara daki dashi shine burin shi a kullun bai ko jin kunyan hakan. Neman mata kan sai ma abunda ya karu gare shi don yanzu baya kunya ko shayin kowa kai tsaye yake abinshi yadda yake son yi
Chapter 51 · 0% Book details