Sashe 48
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Jamil zai dan zo ya dubani kacal yake zuwa a cikin sati a haka har haihuwa yazo min Allah ya sauke ni lafiya na haifi yar diya mace mai kama da mahaifinta sak. Murna wurin yan gidan mu ba,a cewa komai haka ma yan gidan su Jamil gwargwado sunzo sunyi barkan haihuwa su tare da farin ciki. Ba wani abinda suka kawo gidan mu wai don na haihu din do mahaifin shi har gida ta samu baba wai basu da halin kawo irin kayan da ake kawowa idan mace ta haihu a gida din nan. Baba yace ba dai an haihu lafiya ba shine dama abinda muke fata a gare ta wanan maganan ya kara masu kwarin gwiwa suna cewa wai baba ya rike zumunci dake tsakanin gidajen mu din biyu. Suna kwana hudu Jamil yazo gidan mu mun dade dashi muna sakawa da warwarewa a tsakanin mu karshe muka aje magana akan anty zai roka ta shige mai gaba ta samo mashi bashin turamay zani idan ya samu albashi ya rage mata taba mai kaya kudin ta. Na kira anty ta samay mu a daki muka fada mata shawara da muka yanke anty tayi shiru tana tunane muryan shi ne ya katse mata shirun yana dan wani kamay kamay. Ya kara kwantar da murya tare da fadin anty don Allah kada kiji komai da an samu kudi zan kawo maki kudin nan ko na samu wani hanya zan rage da yardan Allah. Don kin san da aure ban samu halin yin lefe ba shine nake son wanan karon in mata abinda mutane zasu gani su sheda nayi. Tace ba komai bari ta kira matar mai kaya sai aji turamay nawa nawa suke a gaban shi sai ya fadi wanda yake so. Yace har akwati da komai kada a wuce dubu hamsin gaba daya nan dai aka kira matar niko har da fadin haba anty ba zamu baki kunya ba ai nan fa gidan sarakunene. An shirya da matar inda tace ya zo su duba kayan ya yi ta ma anty godiya ya tafi ya karbo ya kaima iyayyen shi yana washe baki ala dole yayi abin kwarai da kanshi. A bangaren gidan mu duk abinda akewa yarinya idan ta haihu baba yayi min shi inda kuma baya su cincin da sauran kayan ciye ciye ya sa min turmi goma kamar yadda yayiwa yar gurin shi data haihu bai bambamta mu ba ko kadan. Harda set din jakkuna masu saukin kudi kuda biyu inda anty ma ta garje ta saka min kaya masu tsada nawa dana baby kowa sai yabawa yake da kayan. Yan uwa sun min fada sosai akan kayan kada in fara inbar kayan nan su lalace don ban san ciwon kaina ba suke fada duk wanda yayi min fada abinda yake fadi ke nan . Don na tashi da turakay har arba,in da wani abu ga wanan haihuwan yan uwa sun min kokari sosai ga haihuwan nan har sai da na rasa bakin godiya. Bayan an watse ne anty ta sa dani da kanne na mu zauna a ware masu tsada daga cikin kayan a jesu daban haka mukayi inda masu kyau da kudi sosai na samu sun kai guda goma sha takwas . Sauran duk suma duk atamfa ne sai dai ba masu tsada sosai ba irin da ake kaiwa buki inda duk na baba kabir da yai min manya ne. Dangi ko turmi dadaya sukai min don sunga baba kabiru yana tsaye da al,amarin mu sai suka sake mai komai kamar dukkan su ba yan uwan mahaifina bane fa baki dayan su. Don ni har abinda suke muna din yana matukar bani mamaki sosai sai kuma inyi tunane koshi baba kabir din don dukiyan mu yana hannun shi ne yake min haka din. Bayan kamar sati ne anty tace a dauko kayan nan akai dinkin su don in samu tufafin yin goyo don goyo sai da zani saboda goyo yana cin zani sosai. Banki ta nata ba duk da ina son in ba Jamil shawara akan hakan sai dai ba fuskan yin hakan a gare ni don na fahinci anty da serious take maganan ta. Ina kallo aka kira tela yazo har gida ya karbi dinkin kayan inda anty ta biya rabi ta sa mu kuma mu biya rabi din fitan rabin daga gurin jamil yayi wuya ashe don ina gida ne ya kyale ni. Nayi kiba sosai don jwgon yayi min kyau saboda ina samun hutu da kulawa sosai a zaman da nakeyi a gidan mu din. A kwana a tashi har mukai arba,in da kyat da boni don jamil duk ya matsu mu dawo kamar abin arziki har nima na fara kasa hakkuri da zaman gidan. Haka muka ga munyi arba,in a dadafe a gidan mahaifan nawa da zamu koma ne baba yayi muna sayayyan buhuhunan abinci gero masara shinkafa da su mangyda da kayan miya. Aka tarkata ni aka mayar dani gidan Jamil din dani da yar goyo na koda muka koma mun samu dakin kaca kaca ba gyara ko ina dole suka dan kama min muka dan gyara hakana kafin su tafi. Sarakuwa na sai murna take a gaban iyayyena da suka rakoni ta karbi yarinyar ta goyata tun suna gidan basu tafi ba kamar abin arziki. Jamil na gurin yawon shi koda muka dawo sai dare sosai ya dawo gidan yana fadin ashe da gaske yau zaku dawo din ? Kallon shi nayi da mamakin abinda yace din nace ba an aiko gidan mu a gyara min daki kafin in dawo yace shi ba wanda ya fada mai. Ya shiga daki ya na kallon kayan da muka dawo dashi ya wani ya tsune baki zai juya nake ce mai buhuhunan abinci suna sashen baba an aje da cewa mahaifin shi. Ya juyo da sauri cikin washe baki yana fadin har da abinci nace eh buhu uku ne sai kayan miya da sauran tarkace ya juya da sauri zuwa ganin kayan dana fada mai. Sai can gashi ya dawo yana washe baki tare da fadin shi baba bai san bamu cin masara bane da gero nace gero ai don kunu aka kawo min shi masara kuma don tuwo. Yace ba za mu sha kunnu a gidan nan ba don kin san bamu sha kunu ya fice yana murna ya dawo da leda a hannun shi kaza ce da zafin ta tare da abinsha ya shigo dashi. Mukaci muka kwanta tunda safe washe gari ya tashi ya fita sai gashi ya dawo da wani mutum a bayan shi ya sallama muna sai gani nayi kawai Jamil yana cicibo buhuhunan nan yana fita dasu waje gurin mutumin . Can sai gashi ya shigo yana washe baki yana murna da farin ciki sosai a fili na dauka zai ban wani abu a cikin kudi sai gani nayi ya soke abinshi ya fita. Ban kara ganin shi ba sai daren sosai ya shigo gidan yana wani daure fuskan shi ni dai ban tanka mashi ba na kama lamarin gabana. Ya gaji ya bari ya dawo ya sake da kanshi yana wani haba haba dani, niko kaina sai wani dadi nake ji a raina wai ni miji yana so na . Da rana tsaka sai gashi ya dawo a cikin fara,an shi yana kwala min kira nazo da sauri ina karbawa na amsa mai yana tsaye tsakiyan falon mu na samay shi yace dauko min kayan sunan nan naki in duba akwai abinda nake so a ciki. Kallon shi nayi galala nace wasu kaya ke nan yace cikin canza fuska turamay da kika samu da suna mana . Gaba nane naji ya buga gashi ban gama sululin wasu turamay na diyar kanwar mahaifiyar mu da ta kawo min dinkin su har na koma gida ban samu dinkawa ba na barsu a dakin namu. Ina gidan baba kabir ne ta aiko a karbar mata dinkin sai lokacin na tuna da turamay na tura summaiya kanwa ta ta kwaso min a dakina. Sai gata ta dawo tana fada min bata gansu ba a inda na aje su hankalina ya daga da yazo na tambaye shi sai cewa yayi shi bai gansu ba a dakin tun tafiya na. Wanan abin kusan yaso ya hada mu fada har da sister din mahaifiyar mu uwar yarinyar gashi ita kadai ce ta rage muna uwa da muke ganin dakin su daya da mahaifiyar mu. Amma ta rufe idon ta kan yar tace sai na biya turamay nan ni kuma na kasa dauka daga cikin turamay na in bata sai yanzu kuma shi gashi ya dawo min da zancen kayan dana samu din da haihuwa. Bai tsaya jin abinda zance ba ya fada daki ya fito da akwatunan zuwa falo ya fara budan su sai naga ya dago da sauri yana kallona tare da tambayana ina turamay suke ? Nace ai na fada ma mun kai dinkin su tun kan in dawo gidan ko sharan yan gidan mune hakan don sunce banda tufafi goyo kuma tufafi yake so sai. A hasale yace inji uban wa yace ki dinke wanan kayan masu uban yawa da tsada ki sa ma jikin ki kin ko san kudin kayan nan sai kallon shi nake a cikin mamaki na kasa magana ban iya furta mai komai ba. Ina kallo ya tattara sauran turamay bayan ya zabi guda biyar ya fita dasu da haka sai da ya jide kayan nan kaf ya fita dasu ya sayar. Idan nayi magana sai ya hauni da cin mutunci kamar zai duke ni idan mahaifin shi yaji mu sai yace idan ban rufawa mijina asiri ba wa zan rufawa duniyan nan. Haka dai rayuwan yake tafiya muna tun dawowana daga gidan na samu uwar mijina da muke zama da ita ta canza min sosai har gara lokacin da ban haihu ba din da dan dama. Yanzu ba nasiha a tsakanina da ita ga gori da take min akan gida dan abu kadan zatace idan don gidane nake son raina ta sai a fada masu kudin haya su biya ko su fita su bamu gidan mu. Ina dai hakkuri ban tanka ta duk fadan da zatayi har ta kare bana kulata sam sai idan ta huce ne zata dan dauki diyata ta dan wuni