Sashe 42
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
A fanin girki ba iyawa nayi sosai ba ranan da suka sakar min girki da kaina don farkon zuwa uwar miji ke girkawa sai dana cika wata daya a gidan tace in karbi girki in dinga yi. Ranan tabara zalla a gurina don tun a gida muke kwasan rikici da anty akan girki sai kanwa tace mai yin girki da duk wani aiki daya shafi kitchen a gida don ni ba iyawa nayi ba ko nayi girki bai dadi. Anty kance dani sai nayi aure zan san illan yin hakan da nakeyi don cutar kaina nakeyi ince wai ban iya girki ba ni sai gashi yau maganan ta ya zama gaskiya a gare ni. Idea yazo min bayan na soya makarde na zunbuda maggi star ina jin uban mijina har da santin girkin yakeyi da aka kai mashi nace a raina nagode ma kafanin maggi star don sun fitar dani wanan kunyan. Tuwo dai ne ban iyaba ba musanman na gari ga uban mijina bai cin shinkafa da dare sai tuwo yake so ko wani abu mai nauyi haka. Sau biyu ina tuka tuwo yana ruwa ya sake don yadda nakeyi ashe ba haka akeyi ba don sai na kwaba garin da zantuka da ruwa nake tuka shi ban kuma bari talgi ya nuna nake tukawa sai tuwan ya sake baya kwana da safe ya sake sai dai a zubar. A nan muka fara samun matsala dasu sai uban mijin nawa ya hau zage zage ina ji shi har dakina yana fada akan ban iya tuka tuwo ba kamana. Dole uwar mijin nawa ta shiga koya min yadda zan tuka tuwon don barnan da nake ja masu din na hasaran garin kamar yadda sukace inayi masu. Shi dai zancen kayana yabi ruwa ke nan don babu halin in magana akan shi yanzu fada da gaba zai shiga tsakanina da Jamil din. Ina jin sarakuwa tana gulma da matan hayan gidan mu wai ban iya komai ba sai aukin kwanciya da miji suna min dariya. Ta dauka barci nake nan suka saka faifaina sukaci har suka gaji ina ji su ban kuma fito ba daga dakin har suka watse a gurin haka yasa na dauki niyar gyarawa da kaina. Da yamma na fito zan dora girki tace in jirata idan ruwa ya tafasa tazo ta duba min ruwa na tafasa nayi yadda ta koya min sai Allah ya taimake ni nayi a cikin sa,a don tuwon ya tuku da kyau baiyi ruwa ba. Ina gamawa na ta fito da taji shiru ta samu har na tuka tuwon har ta hau fada wai don may ban kirata tazo ta duba min ba. Shiko surkina da muke cewa malam yana ji ya fara fada tana bude tukunya taga tuwon yana tafasa ya tuku da kyau bata dai yi magana ba sai tabe baki da tayi ta juya ta tafi. Sauran yan hayan gidan sun kafa kujerun su a tsakar gida suna jiran suji yadda zamu kwashe da ita da ta fito sai sukaji ba ai magana ba haka yasa suka fara tashi daya bayan daya suna shigewa dakunan su mai zuwa yin aikin gabata kuma ta shiga yi. A kwaini da nauyin aiki idan na fara aiki daya sai ya kaini wani lokaci ban karasa ba yanzun ma wanke wanke na tattaro zanyi sarakuwa na tana fitowa ta hau fada wai wanke wanken da yakakata inyi da farko shije sai yanzu zanyi in sa masu abinci karnin kwano yana tashi zuciyar su ya kama tashi idan sun ci abincin. Na dai gama na kife ba tare dana ce da ita kanzil ba ga uban mijina daga daki yana karba mata don shi mutum ne da baya fita ko ina iyakan shi gida kullun sai dai akwashi da son cin dadi sosai. Don gaskiya fannin abinci baida wasa ko kadan muna cin mai lafiya mu sha mai lafiya sai mun koshi zaman nawa dasu dai da dadine ba dadi gamu nan dai ne zaune. Don ma ban cika shiga shirgin su ba idan na gama aiki ina cikin dakina sai ko idan yan uwa suka zo gurina zakaji murya na a gidan. Daga cikin matan hayan gida akwai wata jamila da jinin mu ya dan zo daya da ita itace ke fada min wata rana da muka dan kebe a gurin wanke wanke take ce min. Wanan sarakuwan bata son ki hadiza suruka haka komai kakeyi idon ta yana sama ni dai da nice ke bazan bari tasan komai nawa ba gaskiya ko dai don ba itace ta haifi mijin ki ba yasa take maki haka ne. Ni dai murmushi nayi mata tare da fadin kin san zama da manya sai hakkuri tunda suna koya muna gyara ne ai ban yarda na fadi wani maganan da zata kaini gaba ba a gaban ta. Fadin haka da wanan matar tayi yasa na shiga rufe sirina ga kowa dama shi kan shi Jamil din haka yake so bai son ina hurda da kowa bama a gidan kawai ba harda yan uwa na ga baki daya. Niko ina da dabi,an in nayi bako sai na cika mashi ciki ya koshi sosai kafin ya tafi sai hakan ya shiga bata ma uwar mijina rai kuma. Sai ta tsiru da dabian idan na gama girki itace wai zata raba wai ina sa masu nama kadan da kashi mijin ta bai iya ci wanda nake sa mashi din. Wanan dalilin yasa idan na gama girki sai in dauki tukunyar in kai mata itace zata raba ta diban muna namu sai dai arziki na daya Jamil ba mai zama gida bane yana cin abinci sai yamma yakan shigo ya dauki wanka ya fita kuma. Haka yasa abincin ke isana har in samu in ba yan kanne na dake zuwa wani lokaci wurina ga shi ta dauko min idan nayi baki zata shigo ta zauna a falona har sai hakin sun tafi zata bar dakin nawa. Wanan halin da take min yana damuna sosai sai dai banda halin yin magana don a cewan ta tana kulawa ne da bakin nawa ai ya kawo hakan . Wata rana yar shi ta haihu da dare da ya dawo gida yake ce min ina turamay nan da aka bani na aure nace suna cikin akwati yace in dauko mai turmi daya zai ara ne yaba yar uwar shi idan ya samu hali sai ya sai min wani. Da saurina na shiga daki na dauko mai wanda ban faye so ba daga ciki na kawo mai ya fita dakin dashi zuwa wurin iyayyen shi ya kai musu nashi gudun mawan na haihuwa da akai masu din suka shiga saka mai albarka. Tun ranan ban kara jin zancen turumin a bakin shi ba haka yai ta min wayo yana karbe turamen nan ban dinka ko daya ba daga cikin su saukina ma ina da kayan da baba yai min tun a gida dashi da anty amarya nayi fitan buki dashi. Ga matan hayan gidan ina gani da sallah tazo mazajen su suna saya masu kayan sallah niko ba wanda yai maganan nawa inda nasan da sanin iyayyen shi turamay na da yake karbewa a gidan sai banji sun min maganan dinki kayana ba sam ko tashin zancen babu a bakin su. Ashe ni ban sani ba idan ya fita da turmin sarakuwa ja da muke tare yake ba ta kadar mai dasu gidan dillalai abasu kudin suyi abinda suke so dashi. Hakanayi sallah da dan kamay kamay don babu tufafin kwarai a gare ni da zanyi firan sallah dashi haka dai wanan ya wuce kanne na sun zo suke min hira irin kayan da mijin yar uwana ya dinka mata yar wirin baba kabiru dake aure a kusa damu don babu da nisa sosai kusan duk unguwa daya muke har iyayuen namu sai dai akwai dan tazara damu dasu amma duk unguwa daya ne gidajen mu. Da sallah kan muci mun sha shi shan minerals a gurin mu ba wani aiki bane don duk dare yana shigowa da dan ledan shi gidan damu da iyayyen shi. Munje gidan gaida iyayyena da sallah mun fara shiga wurin iyayyena mata muka gaisa dasu ina kallon irin kallon da anty ke min sai dai batayi magana ba bayan kallon akai muna iso gurin baba kabiru. Mu kaje gaidashi a falon shi yayi murna da ganin mu ya tambayi iyayyen mu muka ce suna lafiya har zamu daga sai yake ce min dama yana son ganin mu. Muka koma muka zauna muna sauraren shi yace dani dama maganan aiki ne ya samu a lokal goverment yake son ji wa zai bawa aikin cikin mu niko mijina zai bawa aikin ? Har bakina na rawa don ban bari yakai aya ba nace abawa Jamil yace kina ganin haka yayi maki kada daga baya inzo inji wani magana nace na amince baba a bashi. Haka yasa aka buga offer na aiki da sunan Jamil din ya fara amsan albashin shi yan gidan mu kaf sun nuna min bakin ciki akan hakan danayi kowa sai fadan albarkacin bakin shi yakeyi kan hakan. Niko saima takaicin su da nake ji don may zasu hana in bawa mijina aikin da muka samu ni a ganina hakan zai kara muna dankon soyayya a tsakanin mu tunda har na sadaukar mai da aikin dana samu nawa. Idan wata yayi ya karbi kudin shi ban sani sai dai inga ya dinka sutura ya sai turare da sauran abubuwan bukatan shi da dan cafenen kwana biyu da yake sayowa muci. Gani ragga ya fara yi min sallama a jikina a lokacin sai dai ban daukan hakan wani abu don nasan ba karfi ne ga mijin nawa ba mahaifin shi kuma yayi ritaya yanzu daga aikin asibitin da yake na kauye mafarin tattarowan shi ke na ya dawo birni da zama a cewan shi. Sai dai shi yana kula iyalin shi don yana masu sutura sosai yana kuma basu suna ci da babban sallah yazo an kawo turamay a gidan uban mijin nawa yayiwa matan shi sayayya sosai lokacin ne na samu ya laba dani yake fadin in boye kada sauran sarakan shi su san da ya sai min zani din . Ina ta murna yace in kai a dinka min