← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 49 OF 89

Sashe 49

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 3 min read

a gurin ta na dan wani lokaci. Wanan bai sa na canza daga abinda nake mata ba a matsayin ta na sarakuwa na a gurin su ina bata girman ta sosai da yin aikin dana san nawa ne inyi. Ranan dai ban san ko may ya hadasu fada ba da Jamil ya shigo yana jan tsaki har ya gaji ya kai ga fadin anzo an zauna zaman sa wa mutane ido ana faman takura muna. Wallahi daga yau idan tayi maki ki dinga ramawa ninace nasan bacin ran abinda tayi mai ne yasa ya fadi haka sai ban bi ta kan shi ba kan maganan tsakanin shi ne da ita wanan. Neman matan shi yanzu zanga zanga ne ya kara turani zuwa kauye wai inkai yarinya su gani don wasu da yawa basu santa ba tun kan ya karasa nake ce mai ni dai gaskiya idan yasan zanje ya barni can ne ba zan tafi ba. Wai ashe yaji haushin maganan sai gashi ya kaini kara wurin mahaifin shi ya kirani yai min fada sosai har yana fadin waini yanzu ya gane ina gudun zuwa kauyen mu ne don ina ganin nafisu. Mahaifin nasa yasa alla dole in shirya babu ko wani tsaraba dana tanadar masu na tafi kauye ganin gida tsomai tsomai dani ba laifi tunda nima garina ne yan uwa kuma suna jin tausayina ga maraici ga rashin dace da miji na gari da banyi a cewan su. Wanda ni hakan yana matukar ban haushi sosai don ni banga laifin Jamil ba ai ba gare shine rashi ya yanke cibi ba don ni dauka nake karfi ne baida yasa bai min abinda ya dace yayi na zaman shi miji a gare ni. Abinda ta dawo dani gari wanan karon bayan na shafe sati hudu da kwanaki masu kyau nayi baki duk na fige idan ka ganni bazakace na taba yin boko ba a rayuwana. Zancen kudin mu ne da ya taso yasa baba kabir aikwa in zo zamu tafi abuja muyi wani sgning a can shine dalilin dawowa na dawuri da bansan ranan dawowa na ba gidan. Ko da na dawo na samay su a cikin jin dadi don mahaifin shi ya samu kudin aikin shi da yai retaya ya fito sai dadi suke ci a gidan babu kama hannun yaro. Atm din shi ma yana a hannun Jamil ashe idan tsohon yace ya ciro mai dubu biyar sai yaje ya cire dubu hamsin ko arba,in yasha garalin shi dashi. Na dawo muna shirin zuwa abuja da baba kabir da kani na Baffa ne suka tashi da rikici a gidan da tsohon nashi ya tura wani kanin Jamil din ya ciro mai kudi aka samu saura dubu goma kacal a banki. Wanan abin ne ya kawo rikici tsakanin shi da mahaifin nasa sukai fada sosao ranan da dan son nasa haushin wanan abinda yaji yace duk zugin matar shi ce . Don itace mai zugashi a kanshi don ta tsane shi saboda ba ita ta haife shi ba niko ala dole sai naji zafin abin na shigar ma mijina fada. Har muka tafi abuja ban magana na kirki da ita ba wani abu bani hannu kawai muka sa a takarda muka juyo zuwa gida. Ina shigowa na samu Jamil ya gyara min daki ranan bai fita ko ina ba don dama muna ta wayan dashi ganin muna tare dasu baba ne yasa bai tambaye ni tun ina can ba zancen kudin namu. Ina dawowa ya tare ni da murnan shi har da karbar min jakka na ya karbi yarinya yayi mata wanka ya shirya ta sai da zzamu kwanta yake tambayana nayi mai bayani. Tsoki yaja ya bani baya bai kara magana sai safe ya tashi a cikin daure fuskan daya saba bai dade a gidan ba ya fice gaba daya.
Chapter 49 · 0% Book details