Sashe 19
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read
makara da yawa saboda suna daukan mataki sosai. Bayan tafiyana da sati daya Allah ya karbi ran mama ta tafi da cikin dake jikin ta su umma sun ga tashi hankali don mahaifin mu ya birkice masu shima gaba daya don mutuwan ya taba shi sosai. Abin mamaki a ranan ne kuma mahaifiyar Jamil ta rasu a can gida sai waya suka samu Allah yayi mata rasuwa itama da yammacin ranan a gida don ita ma tayi dan jiya sai dai ba a sa ran rashinta ba don zazzabi ne tayi na dan kwanaki yazo da ajali. Ina school ban san wainar da ake toyawa a gida don nasa ran mama taji sauki har su umma kila sun koma gida a lokacin. Ashe mama bata duniya ta tafi gurin da ba a dawo sai rabon a hadu gobe kiyama idan da rabon haduwa din gare mu Allah yasa mu cika dakyau da imanin ubangijin mu a ran mu Amin. Nasan wanan shafin zai taba zukatan makaranta da dama don akwai zafi irin wanan mutuwan ka rasa mahaifiya a lokacin da kafi kowa bukatan ta a duniya. Mama ta tafi tabar baba da nauyin rikon iyalin data bari shine kalman da mahaifin mu ke fada ko wani lokaci yana kuka da hawayen shi na rashinta a tare damu. Har sunje gida anyi zaman makoki sun kwana biyu a gida suka dawo duk banda labari saboda makaranta da ya boyeni a lokacin. Mahaifina ya kawo min ziyar sai dai duk da karancin shekaruna naga sauyi a tare dashi don ya ramay yayi baki sosai babu walwala a tare dashi. Cikin farin ciki da kaguwa na tambaye shi mahaifiyar mu yace taji sauki sosai tana gaishe ni umma fa na tambaya sun koma ne baba ? Yace umma nanan zaune gida zata kwana biyu a wurin mu kafin ta koma sai dai maman mu ta tafi gida a can zata haihu yace dani. Ina ta murna maman mu zata haihu ya bani abinda zai bani ya tafi bai dade a gurina ba kamar yana sauri ashe kuka ne yazo mashi a lokacin. Ina ta fadama abokaina mahaifiyata zata haihu zan gyaiyace buki suna ban address din su tare da layin wayan su idan ta haihu in fada masu. Har akai hutu baba yazo da kanshi ya dauke ni na isa gida da murna na ko zan samu mama ta haihu a lokacin. Sai dai ba mama a gidan sai umma da kanne na a gidan suma yanayin su ba dadi a yadda na samay su sai umma ce mai karfin halin taro na da zuwa. Ni a zatona tunda nace umma mama har yanzu tana gida bata haihu ba naga bata dawo ba sai cewa tayi da sauran lokaci zata dade a can kafin ta dawo. Na dauka idan ta haihy zamu tafi gida ayi bukin suna damu acan tana ganin ina murna ta shige daki tana kuka tunda nace Allah yasa mama ta haifi mace wanan karon. Maimakon in ga murna da doki a fuskan kanne na sai bata rai danaga sunayi idan na shiga daki su biyo ni sai umma ta kwala muna kira dole mu fito daga dakin. Ashe umma bata son su fada min halin da ake cikine sai washe garine bayan mun karya naga mahaifina bai fita aiki ba sai na dauka yana up ne aikin dare zai fita. Kira ya kwala min ina daki ina gyara na fito da sauri yake ce min tare da nuna min wuri in zauna bayan na samu wuri na zauna ne ya kira sunana. Na dago kai a hankali na amsa mashi da na,am baba yace magana zamuyi dake ina son ki fahince don ke musulmane ko. Na daga mashi kai a hankali yace kin san rayuwan mu a gurin Allah yake ko nace eh baba ya ce dakyau yace kin san ko yanzu ko anjima Allah zai iya kiranmu mu koma gare shi ko ? Sai lokacin na fara jin tashin hankali yana ziyara na don ban son ai min maganan mutuwa ko kadan sai naga umma tana share hawaye da gefen hijjab din ta. Baba yace kin san kin wuce kin bar mahaifiyar ki bata da lafiya ko da sauri na dago ina fadin eh baba nasani yace to hadiza hakkuri zamuyi don Allah daya bamu ita ya karbi abinshi . Baba nace da karfi sai kuma na koma fadin inna lillahi wa,inna alaihim rajiun sai naje su a gurin na somay masu ban san inda nake ba don halin da na shiga. Sai farfadowa nayi na ganni a hannun umma tana shafa min ruwa a fuskana budan baki na nace mama da karfi tayi saurin rufe min baki da hannun ta. Baba bai iya fadin komai ba don shima kuka yakeyi a lokacin ga kanne na da suke kuka wiwi a kaina suma. Umma rana naga taushi a gurin ta don ita ta koma tana lalashi kamar yadda mama zatayi min ta koma min makwafin mahaifiya a gareni. Banci ban sha don damuwan da nake ciki bazan iya fada ma mai karatu ba sai wanda ya taba shiga irin halin da nake ciki a lokacin yasan irin rayuwan dana riska a lokacin. Baba yana lalashin mu yana nan nan damu baya son yaga ran mu ya baci ko kadan sai dai duk wanan ban gani nidai muradina mahaifiyar mu ta dawo gare mu. Da kyat suka shawo kaina na fara dan walwala da kannena da nasiha da fada da komai hankalina ya fara kwantawa. Sai daga bayane nake jin labarin mutuwan mahaifiyar Jamil wurin kanne na na tausaya muna sosai dani dashi don irin halin da muka riski kan mu a ciki na rashin magaifiya da mukayi. A cikin wanan yanayi na bakin ciki ne hutun mu ya kare haka aka mayar dani school ba tare da na gama warwarewa ba. Wanan time din na dai koma school din ne ba don zan aiwatar da komai ba na fannin karatuna haka din ne kuwa don tunanen mahaifiyata ya hananu shakat a raina. Sannu a hankali na fara sakewa ina dan walwala a makaranta duk da ba wani yi nake kamar a baya don ba zan iya shafe rashin mahaifiya a zuciyana ba.