Sashe 16
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 6 min read
sosai da ganin tsaraban zuwan da mahaifin mu yayi gaida umma ne yayi shawaran sayen fili don yai gina a garin da baba kabiru yake don nan ne local govenment din mu. Bai dawo ba sai da yaga komai ya kan kama na ginan ya dawo yabar baba kabiru da sauran aikin ginan gidan yadda yake son a tsara mashi ginan gidan. Akan ginan ne baba kabiru ya shigo Abuja wurin mahaifina munyi murna da ganin shi sai dai haduwan su baida dadi don bai koma ba sai da suka samu sabani sosai akan ginan da mahaifin mu. Don yace shi bai gane kan ginan ba don ba haka akai mashi lissafin komai ba kafin ya dawo wanan maganan ne ya tunzura baba kabiru din yai fushi ya fada ma mahaifin bakaken maganganu shima. Sai dai kafin ya dawo sai da mama tasan yadda tayi ta shirya tsakanin su dashi har ya hakkura ya karbi aikin akan zaici gaba da kula mashi da aikin a can. Washe gari ya juya ya koma sai da yai muna alheri sosai kafin ya tafi din muna ta murna da hakan shiyasa muke son zuwan shi ga kifi da sauran abin marmari dayazo muna dashi na tsaraba. Hutun mu ya kare na koma makaranta cike da kewan yan uwana dana bari a gida don sune abokan hiran nawa a gida tunda ba kawaye nakeyi ba ni. Karatuna ba wani matsala don baba yana alfahari dani sosai don bani cin na kasa da uku duk hutu don hakane ma nake samun kyauta daga gurin mahaifin namu. Matsalata daya da baba yawan ce mun banda wayo da yakeyi ko yaushe alhalin niko naga ina da wayau ai amma daga baba har mama abinda suke ce min ke nan danayi dan abu kadan yanzu zansha fada sosai a gurin su. Umma tazo ta kwana biyu a gurin mu lokacin na dawo gida na samay ta haka muka zauna a cikin tsangwama irin nata . Tsangwaman ta akainane da kanina baffa da yanzu ya tasa bai son zaman gida ko yaushe suna kwasa da baba akan fitan da yakeyi waje. Haka yasa itama zuwan ta ta karbe korafin da ta fita yanzu zata haushi da masifa ta bal,balleshi da masifa wai idan ya fita wanan garin da babu kai ba a gane gabas din shi don yawa. Ranan tare da da kanne na muka je bukin wani birthday sai ba a fara program din da wuri ba har muka kai dare muna can wurin wasan. Mahaifin mu ya dawo gida ya samu bamu nan nan ya hau mahaifiyar mu da fada don birthday din dan kawar tane muka je dan da kyat ya yarda mu tafi don umma ta saka baki yasa ya yarda muje din. Ya fita ya bimu a can ya samay mu ana sallaman mu don komawa gida sai gashi tun a gaban mai bukin ya fara bal,balan mu da fada tana bashi hakkuri. A mota ma mun shs fada sosai a furin shi inda duk laifin ani ya dora min don nice babba a cikin mu muna shigowa gidan umma ce ta tare ni da wani fadan kuma again har yafi na baba ma fadan nata. A cikin fadan take fadin da wanan wautar har kike son wanan yaron mai shegen wayau din da son banza da sauri baba yake tambayan ta wani yaro kuma umma. Ita hadiza din har take soyayya ban sani ba ni wai ma wani yaro ne take so din tace rabu da yar nema mara wayau kawai bata san sherin mutanen garin nan bane. Allah ya rufa muna asiri ya rabaku dasu kike son wanan dan banzan yaeon ya hure maki kunne wa yanda ke cikin garin ma mai suka zama har yanzu. Wani kallo nayi mata ta watso min dakuwa da hannun ta na noke kaina da sauri tace don na zage shi zaki min kallon banza ko ke gaki issasa ko ? Baba ya sake tambayan wani yaro ne wai take magana a kanshi tace bar yar nema ai na balbale ta babanta yushau kuma yaje yai mai iyaka da ita har gidan su. Don ubanshi yazo ya ban hakkuri har gida don yasan halina sarai ba kyalesu zanyi ba wurin mahaifiyana ya juya yana mata kallon tuhuma. Tayi saurin fadin ga umma nan ka tambaye ta idan da masaniyana haka ya faru din ta yi saurin kare kanta daga masifan shi. Kutawa yayi ya shige daki na koma na rakube a guri daya ina ganin kamar zai dauki matakine a kaina ranan. Umma duk abinta Allah yayi ta mace mai rikon ibada sosai dama ance mutum dan tara ne bai cika goma ba gata da yawan saka ma diyan ta albarka. Bata da sakaci da ibadan ta don ko yaushe a cikin lazimi take tana zikiri da sauran abin ibada daya dace mutum yayi a ganuwan shekaran shi ta karshe. Tun wanan ranan nake dari dari da mahaifina don ban san irin matakin da zai dauka a kaina kan maganan daya ji daga bakin umma din ba. Sai dai shiru har hutun mu ya kare muka koma makaranta na barsu a gida daya kaini tun a mota yake min fada mai kama da nasiha akan in mayar da hankalina ga karatuna sosai. Idan na gama zai kaini inyi kararun likita nan gaba kada in sa wasa in bata kurciyana ga banza har sai da nayi hawaye ba tare da ya sani ba. Lokacin vistinga da yayi ina saka idon zuwan yan gidan mu sai naga sabanin hakan sai babane yazo shi kadai wai sun tafi gida su. Banji dadin hakan ba amma sai na dake ina addu,an Allah ya dawo dasu lafiya ba karamin sayayya baba yai min ba a lokacin. Nasan duk cikin tsigar lalashine yasa yai min sayayya haka mai yawa bai jima a gurina ba ya wuce sai dana koma hostel ne nayi kukan tafiyan da sukayi wanan karon ba tare dani ba gida don ban san lokacin da zan tafi ba kuma. Mun dan jima wanan karon don candy da zamuyi na jinor waec sai da muka gama na dawo gida da kaina don yanzu ina da wayo na zan iya kai kaina gida da school din. Nayi murna da na samu sun dawo gida suna ta ban labarin gida da wuraren da sukaje ina son in tambaye su labarin Jamil babu daman in tambaya don mama dake falon tare damu. Da dare na ina shirin kwanciya baffa ya ban takarda wai inji Jamil yace ya kawo min tare da fadin bai bari kowa ya ga takardan ba ya boye min. Naji dadi sosai ga labarin shi da yake ban yace yanzu yana final year ne a inda yake karatun shi. Sai dana gama komai mun shige na fito da takardan na karanta gaisuwa ne tare da jaddada min irin kaunar da yake min din naji dadi sosai har cikin raina na samu wuri na boye takarda. Duk da takardan ya dade a wurin baffa kafin in dawo gida amma bai hana shi kamshin turaren daya zuba a jikin takardan ba daya rubuta. Na mayar da takardan abin dabe min kewa do duk dare idan zan kwanta zan dauko in karanta in mayar in nuke a inda nake adanawa kada wani ya gani a cikin iyayyena. Haka rayuwa ya dinga gudana muna jin dadi sosai a gurin mahaifan mu don duk wani abinjin dadi suna muna shi na nuna so da kauna gare mu.