Sashe 25
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read
rashi sosai ga rashin kin cin komai da nakeyi ne yasa na dan daure nasha kunu a gaban shi kadan. Muna manne da umma wace yanzu nauyin mu ya koma kanta muna ganin ta komai namu a duniya duk da mahaifiyar maman mu tana nan da ranta a duniya. Sai dai ba sabawa mukayi sosai da ita ba don mun fi sabawa da umma don da ita muke zaune akoda yaushe. Wanan mutuwan ya tayar da hankalin mutane sosai a kauyen mu don yanzu ne mahaifin mu yake a ganuwan samun arzikin shi sosai a duniya. Sai kuma Allah yai nasa ikon akan shi ya raba mu dasu a daidai lokacin da mukafi kowa bukatan su daga shi har mahaifiyar mu a duniya. Kwanan baba kabiru uku bayan sadakan uku ne ya kebe damu yake fada muna shi zai koma zai tafi ya tattara kayan mu dake can abuja. Don yanzu zaman mu ya dawo nan ke nan da sauri nace baba karatun mu fa yace zamu duba wanan idan mun dawo sai mu san abinda za ayi akai. Abinda nake so daku shi ku kwantar da hankalin ku ku natsu ku rage wanan damuwan da kukeyi alabashin hakan zai sa muma hankalin mu ya kwanta mu samu natsuwan yin abinda ya dace a kan ku. Ya bar muna wanan kudin da yazo dashi yace muyi amfani dashi kafin ya dawo mukai mashi godiya ya tafi bayan ya gana da umma da yan uwan shi. A kwana na uku ne mukaga su baba yushau da baba musa sun shirya ashe tare zasu tafi abujan don ganin abinda mahaifin mu ya bari a can din. Har lokacin gani nake a raina kamar zamu koma Abuja ne ba a nan zamu zauna ba ban da wani sukuni a tare dani idan kaji muryana sai idan yan kannena ke wani abinda bai dace ba na tsawa ta masu. A rana ta bakwai da rasuwan mahaifin mu ina kwance saman gadon karfen umma dake dakin don yanzu gaba daya a dakinta na tare din tsoron dakin mu nake ji gaba daya. Yaro yazo yace wai Jamil yana sallama dani kamar banji yaron ba sai umma ne ta bashi amsa da fadin wanan mai bakin nacin kaje kace dashi ba zata zo ba. Summaiya ce tace haba umma ki bari taje su gaisa mana kila gaisuwa yazo yai muna kuma kin kore shi da fadan kin nan. Dakuwa ta sakar ma summaiya da hannun ta tana fadin ungo naki ni kike fadawa wai gaisuwa yazo yai maku kunfini rashi ne ni da dana ne ta rasu kuma nayi hakkuri da rashin shi. Sai mikewa nayi daga inda nake kwance ba tare danayi mata magana ba zan fita tace wai fitan zakiyi ko baya na hana. Umma ba dadewa zanyi ba gaisawa kawai zamuyi dashi in dawo na bata amsa na fice ban tsaya jin abinda zata fada min ba. Na samu ya juya zai tafi na kirashi ina fadin gani ya juyo fuskan shi ba yabo ba fallasa a cikin shi bayan mun gaisa ne suke fadin ashe kuma baba lokaci yayi. Idanuwana suka kawo hawaye nace muma haka wanan zancen yazo muna ashe iyakar mu dashi ke nan daya rakomu shiga mota da zamu zo nan. Sai hakkuri do mutum baya wuce lokacin shi kece babba idan yan uqan ki suna ganin ki a cikin damuwa suma ba zasu sake ba yace. Duk maganan da take kaina yana kasa ina hawaye a lokacin don ban iya kara furta komai saboda tunanen mahaifina da nakeyi a lokacin. Abokin nasa ne yace yanzu komawa zakuyi abujan ko may ake ciki tunda ance kuna da gida a can ai nace cikin muryan kuka ban sani ba sai dai babu alaman zamu koma can din . Don naji su baba kabiru sun tafi hada kayan mu dake can yanzun haka suna can basu dawo ba tun shekaran jiya suka tafi. Ajiyan zuciya naji jamil din ya sauke tare da fadin nima tunanen da nakeyi ke nan idan kun koma can dawa zaku zauna acan yanzu kuma. Muryan umma ne ta fito da tocilan ta tana haska muna tare da fadin kaikan wanan yaron idan kana maita sai ka cinye yan gaein nan a baki dayan su. Ke kuma munafuka maza ki shige tun ban bata maki rai ba a furin nan yanzu simi simi na wuce ta tare da fadin sai da safe ku na gode na barsu da ita a gurin. Bata shigo ba sai data dan dade dasu ban san dai yadda suka kwashe da ita ba don ko da ta shigo har na kwanta abina ta karashi fadan ta kala bance mata bani dai.