← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 52 OF 89

Sashe 52

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ganin rashin dawowa gidan shi da wuri yana ci mun rai ga kuma abinda mahaifin shi yace da nakai kara yasa na sa ido gare shi.
Yau ma da yamma yai wanka ya shirya ina zaune ina kallon shi yana ta faman feshe feshen jikin shi da turare har ya gama zai fita nake tambayan shi kudin cefane .
Ko kallon banza ban samu ba a wurin shi yasa kai ya fice daga gidan wana abin ya karas min jin haushi da takaici ranan dai sai garin rogo muka sha nida diyana ga ciki a jikina kuma.
Ina zaune ina kallo na dubi agogon dakin lokaci ya nuna sha biyu da rabi na dare tashi nayi na goya yar diyata a baya na sa hijjab dina.
Banji tsoron dare ba haka na fice tunda gidan namu a bakin titin unguwan mu yake nasan ba zan rasa mutaje ba a lokacin a waje.
Gidan hanyan da Ruth take na nufa don ba wani nisane a tsakanin mu ba don dama matan unguwan mu sun min kwatancen gidan har dakin da take zaune a ciki.
Ina shiga dakuna ne birjit sai kida ke tashi da kallo a wasu dakunan na gida dagani kasan gidan da kabila suke zaune ne a cikin sa.
Dakin na dosa inda cool music ke tashi ciki a hankali ban tsaya wata wata ba nayi nocking din kofan dakin da karfi ina duka iya karfina .
Muryan Jamil ne daga ciki yake fadin who is there ?
Na kara nockin iya karfina sai naji muryan ta tana fadin iam coming dan wani lokaci aka bude kofan tana dare da dan karamin towel iya cinyanta tayi daura gaba dashi.
Budan kofan mukai arba da ita da sauri ta koma tayiwa kofan key yadda ba zan iya shiga ciki ba nan take na dinga dukan kofan ina zagi sukaki budewa daga ita har shi.
Dukan kofan da nake da zagi ne ya jawo hankalin mazauna gidan suka fara fotowa daya bayan daua daga dakunan su suna tambaya lafiya.
Sai zagi nake ina fadin husband snercher shame for you ina mata ihu idona ya rufe sai kallo na mutanen gidan keyi sin kasa min magana.
Sai wani iyamiri daga shi sai dan gajeren wando ga katon ciki ne yazo wuri yana fadin madam kiyi hakkuri ki koma gida basu kyauta maki ba gaskiya amma kiyi hakkuri don Allah.
Kin ga nan gidan haya ne yaran mu sunyi barci zaki iya tayar dasu daga barci gashi gobe suna da school yana kokarin jan hannu na na fisge hannun nawa daga rikon da yake son yi min.
Na kokarin shi kaini wajen gidan ganin naki kula shi ya hada hannayen shi biyu guri daya yana fadin don Allah kiyi hakkuri ki koma gida ki jira mijin ki ya dawo sai kuyi ta can dashi tunda sunki bude kofan gidan.
Kallon shi nayi ido jawur sai ya kara hada hannayen shi wuri daya tare da fadin don Allah a cikin hausan shi da bai zauna ba sosai a bakin shi.
Ganin yana ta hada ni da Allah gasu su kuma sunki bude kofan yasa na juya na fara tafiya na fito daga gidan mutumin yana biye dani a baya yana bani hakkuri.
Yace mun san basu kyauta ba muma muna magana don abin nasu yayi yawa sosai har muna tunanen yana da mata kuwa akace muna kece matar shi ai.
Kiyi ma mijin ki nan fada sosai don Allah ko mu a gurin mu wanan abin kunya ne haka da sukeyi har sai da ya fitar dani a lungin gidan da sai yanzu nake jin tsoron wurin mutumin ya koma gida.
Ni kuma na wuce zuwa gidana hankali a tashe kowa yayi barci a gidan haka na zauna kamar manya ina dakon jiran shi ya dawo.
Karfe daya da wani abu ya shigo gidan yana wani muzurai da shan kamshi a fuskan shi yana shigowa na dora mugu azzalumi macuci ma,hainci kawai fita min daga daki kada ka goga min zunibin da ka kwaso a daki.
Wani kallo ya watsa min yana kokarin shiga dakin na tare kofan da sauri ya bangaje ni na fadi ta bayana sai da kashina ya amsa min don yadda naje baya din.
Ya shige abinshi na tashi da kyat na bishi ciki rikici sosai mukayi dashi har da saki ya bani a cikin daren nan kafin gari ya waye don ya zagu sosai a wurina.
Da asuban farko ya fita gidan ashe gurin mahaifin shi yaje ya fada mai abinda ya faru a tsakanin mu inda ya nuna mai rashin gaskiyan shi kan abinda yayi min din .
Ina zaune inda na idar da sallah sai lokacin nake jin ciwo a kwankwaso na a inda na buge din daya ture ni da dare yake min ciwo sai sallaman su naji har da matar baban shi sun shigo.
Ban daga ba daga inda nake zaune anan suka samay ni muka gaisa dasu sai gashi ya shigo falon yana muzurai da idanuwan shi.
Nan mahaifin ya fara bayani ya nuna ma kowan mu kuskuren shi ni dai laifina wai don may ban jirashi gida ba har ya dawo muyi abinda zamuyi dashi na bishi can.
Budan bakina nace baba kai kace min na sheda abinda ake fadi din ne a kansu, baba danaje fa matar daga ita sai towel ta fito min dashi a gaba.
Yace bake kika je mata gida ba koma yaya kika samay ta aike kika jawa kanki mugun gani na dauka wani fada sosai mahaifin nasa zai mashi sai ji nayi yana mashi fada akan sakin da yai min kawai.
Inda ya kare zancen shi da fadin mu ruwa kan mu asiri mu boye maganan kada in bari gidan mu suji zancen sakin nan don nasan ba aure na da Jamil din suke so ba.
Chapter 52 · 0% Book details