← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 46 OF 89

Sashe 46

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

Abin sai kaman za a kama sai kuma aji shiru duk dai wani abinda suka bukata na riga dana gabatar masu dashi ko akan takardan nashi. Ya kare da fadin Allah dai ya jikan wani yai masa rahama muka ce amin don ni nama manta rabon da inwa mahaifina addua irin haka yanzu idan ba raina ne ya baci zan tuna dasu ba. Nan dai mukai wa baba sallama muka fito tare da yiwa sauran mutanen gida sallama ganin tare da shi muke yasa yau ban samu rakiyan yan gidan namu ba har gida. Tsuki yai ta ja har muka kawo gida yana dura ma wanda bai sani ba zagi wai sallon suci kudine yasa suka rike kudin har wanan lokacin ace mutum ya mutu har kusan shekara biyar kudin shi bai fito ba. Ni dai ina jin sa sai jefi jefi nake saka mai baki a zancen nasa sai kawai kwana biyu angulu ta koma gidan ta na tsamiya ya tayar da halin shi na yawon dare da yakeyi sosai. Nan dai nayi ta zaman hakkuri ban faye damuwa da halinsa ba sosai a cikin haka maganan kanwata da wanan mai nemanta usman magana tayi karfi sosai akai masu baiko a tsakanin su. Don yafi jamil dina hali ta ko ina bama za a hadasu ba kuma ya dan girmay ma Jamil din ga shekaru shi karatun shi yasa ma gaba sosai don gidan su suna karatu har nisa . Ba irin Jamil ba da yasa karyan duniya a gaba kuma a haka nake son abina kamar in hade shi ba dama wani dan gidan mu ya fadi maganan shi a gaba na koda kuwa mahaifan mu ne. Sai dadin hira yasa na kwashe na fada mashi abinda kace mai wani fa mai miji don a yadda mukai alkawari a tsakanin mu sai nake ganin ni kadai zai zauna dani har tsufa mutu ka raba takalmin kaza. Sai ya dibi kwanaki baya garin yana gurin yawon shi na banza zai dawo ga matsin daga wurun iyayyen shi dana fara fuskanta yanzu daga gare su tunda suka lura komai ya kare min danazo dashi daga gidan mu sai dan kamay kamay da nakeyi. Ina ganin yadda mata sa,anni na suke kwaliya gwanin ban sha,awa dasu niko babu hali sai kamay kamay idan buki ya kamani dole in tafi. Wani lokaci ina ji ina gani zanki zuwa bukin dangi daya dace ace na tafi don nasan yarda zan fito tsumai tsumai a gurin ina labe labe . Kowa tausayina yake ji ga abin magana ba halin a fada min gaskiya in kwashe in fada mashi ya tsiri yin gaba da mutum take zai nuna masu hakan. Shiya kowa ya kawo ido ya sa min dashi ana kallona don karya fure take bata yaya ni duk wanan bai damuna tunda dai muna zaune lafiya da mijina komai yayi. Idan yan uwana sun zo suna ban sha,awa yadda suke fita tsab dasu har ana kwatance dasu a gari saboda iya kwaliyan su da fita niko ganinan kullun a rabe a gida. Sai wani hali da yazo min yanzu dashi na ganin ya rabani da kowa daga cikin kawayena da mukayi makaranta a tare muna dan hurda dasu. Sai ya nuna min shifa bai son suna zuwa min gida duk yadda zanyi in kore su dole inyi don dai kawai a zauna lafiya dashi. A kwai wata kawata da tazo min muna zaune muna hira ya shigo suka gaisa dashi bayan ya shige ne take fadin hadiza dama mijin ki ke nan nace ina dariya kin san shi ne ? Tace uhumm gani nayi dai kamar na sanshi a wani guri ashe a unguwar su yana neman wata yarinya anan ta sanshi sai dai bata fada min ba sai bayan ta wuce ne ya hau fada dani. Wai shi bai son kwashe kwashen irin kawayen ga yan iska ya fa santa ba yarinyar kwarai bane sosai don haka kada ya kara ganin mu a tare kiri kiri ya hana wanan hurdan sai daga baya nake jin labari a gurin kawayen mu a inda ya santa yana gudun ta fada min komai inji. Sai dai abinda na kula dashi yana matukar son yaga kawaye yan karya sun zo min nan zai fara rawan jiki ya fita ya sayo kayan sha ya kawo muna. A zauna dashi ana hira da wasa da dariya har su wuce sai hakan ya fara kulle min kai don na rasa gane gabas din shi shida yace bai son kawaye sai inga idan wasu sunzo min yana rawan jiki wanan ke nan. Ina ji ina gani banda halin shan abu mai sayi a dakina sai na saya ga cikin dake gare ni yana sani shan abu mai sanyi sosai. Sai dai ban samu wani lokaci kuma banda canjin da zan saye a tare dani ga fridge dina Jamil ya hada dashi ya fitar yace wai karamine aka saya min. Haka yasa yanzun nake kama kama da wahalan sayen abin sanyi in jika makoshina dashi ko tausayin halin da nake ciki baiji ko kadan. A cikin haka har watan haihuwana ya kama inda na koma gida don haka aladan gidan mu yake haihuwan fari a koma gida a haihu a can. Shi da kanshi ya matsa min tun watan bai tsaya ba yake damuna wai yaushe ne zan koma gida ne har mahaifin shi ya kama mashi shima yana fafin haka kamar sun gaji dani a gidan ni da gidana. Haka dai na koma gida wurin haihuwa inda na dauki wasu satituka ban haihu ba ina zaune a gidan mu sai ya ga dama yake zuwa dubani a cikin sati sau daya. A cewan shi wa kada ace yayi rashin kunya idan yana zuwa nan ko yana sheke ayyan shine a gari kawai da yab mata tunda shi dan karyane.
Chapter 46 · 0% Book details