← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU. 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Ranan dai ban iya aikata komai ba a gidan ko abinci ban dafa ba duk jikina ya mutu ina jiran shigowan jamil din gidan inji inda kayana suke. Wanda nasaye da hakkina na rufa mai asiri dashi na dawo yanzu ban samay su dakin ba kuma ai dole hankalina ya tashi sosai fiye da tsamani. Kamar yasan ina jiran shi sai ranan kuma bai shigo gida da wuri ba sai can cikin dare sosai ya dawo lokacin har barci ya fara sata na a inda nake zaune a falo. Jin karan bude kofan shi na mike zubur dani yace may ye haka ban bari ya rufe baki ba nace Jamil ina kayana suke don babu komai a cikin akwatunan ga baki daya dana bude. Yace cikin dakewa wasu kaya kuma nace kayan sunana da muka saye yace suna ciki mana ina ruwana da kayan ki tunda muka saya. Nace abar maganan wasa ina kayana suke yace wai bai sani ba yana kokarin shigewa daki na mike da sauri nasha gaban shi ido rufe na kara tambayan shi. Yace wai kina haukane ko may ko kin mai dani barawo ne da zaki tsare ni kina tambayana kayan ki ko kinga ina zama a gidan ne ni ? Hannu na dora a kai na fara zunduma mashi ihu a dakin ina fadin wallahi ban yarda ba don babu wanda zai shigo min daki bai bar alama ba. Ganin zan tayar da mutane gidan yasa yace ki bari zan maki bayani da safe don Allah yana fadin haka ya shige daki ya kwanta abinshi . Haka na kwana ina juyi duk tunane ya hanani barcin kirki washe gari ma da wuri na tashi don kada barci ya dauke ni ya gudu. Ina cikin aiki ya fito na bar abinda nakeyi nace Jamil ina sauraren ka yayi kamar bai jini ba yana kokarin ficewa dakin. Nayi sauylrin tarewa ina fadin wallahi ba inda zaka sai ka fada min ko inyi karan ka ya wani juyowa yana fadin ni zakiyi kara akan kayan ki hadiza ? Nace wallahi kuwa idan baka fada min inda kakai min kayana ba yau a gidan nan ganin da gaske nakeyi yasa shi fadin suna wurin dinki. Cikin zaro ido nace duka kake nufin kakai dinki turmi talatin da wani abu , yace bake kika ce a dinka ba shiyasa na kai dinki duka. Wani wawan ajiyan zuciya na sauke ina fadi yanzun naji magana dai sai dai har yanzu zuciyana bai yarda cewa duka kakai din ki ba gaskiya. Yace yanzu dai na gane abin hannun ki ya fara rufe maki ido da har kike son tayar min da hankali akan zanuwan banza naki ki jawo min mutane. Nace ai dole don kudin nan kaima kasan ban ci komai a cikin su ba don may ko ba zan tayar da hankalina ba akan su. Kowa ya sai abin kwarai da kudin shi sai nice zan banzatar da kudina a sakani a baki gashi dama mutane na fadin nice banda arziki cikin mu da an bani kudi ka cinye. Yace inji uban wa ke fadin haka ya wani gayayyako ni yana fadan karya har ya samu ya fice daga gidan dama abinda yake so ke nan ya samu hanya ya sulale ya fice. Ashe shi wayau shi daya kwashe kayan ace sata aka shigo akai min da bana nan shine hikima shi na turani gidan su in yi kwanaki acan. Sai kuma wani abinda ban sani ba mai ban mamaki da daure kai da lamarin Jamil shine ashe wai hayan kaya nan sukayo dashi da Ruth a shago. Sukayi alkawarin zai dawo masu dashi da zaran an gama suna danawa da na baby din ga baki daya har akwatinan gaba daya na hayane. To ina yakai min kudin da ya karbe a hannu na din daya karba wanda yasa na sayar da filin mu a wani gari daya matsa muna sai da muka sayar. Duk abinda nakeyi yin shi kawai nakeyi hankalina bai kwanta da zancen kayan ba don tun ranan da mukai maganan ya shiga wani tsare gida yana daure fuskan shi gare ni. Kyale shi nayi sau da aka cika sati biyu na kara tuntubanshi kan zancen dinki yace yaji kawai ya fita bayan kwana biyu mm a sake tambayan shi kuma. Ranan dai fada mukayi dashi sosai kan kayan inda nasha kuka na sosai don na fahinci babu dai kayan kwana kwana kawai yake min kan kayan. Washe gari tun da safe na shirya sai gidan mu gurin iyayyena inda na samu dama irin ranan da suke jira gare ni ke nan yazo. Sai da suka gama saurare na suka dora a inda na tsaya baba bai gida a lokacin sai da ya dawo ne anty ke fada mashi ina nan na zo gida mun samu rikici da Jamil. Yasa a kirani nazo ina kuka nake fada mai komai har na gama murmushi baba yayi tare da fadin ni dama ban shirya ma zuwan irin ranan nan bane a rayuwana. Ko ban san wanda na nace sai na aura din bane wai dama sin san abinda zai je ya dawo ke nan sai dai a lokacin da suke kokarin nuna min hakan ganin su nake a matsayin makiyana a gare ni. Ina kuka nace baba nayi nadaman auren Jamil a rayuwana don ya gama dani gaba daya a rayuwana wallahi. Baba yace hakuri zanyi in koma don ga zuria a tsakanin mu yanzu sai dai in koma inyi hakuri da halin mijina don su ba zasu taba kashe min aure ba in dawo ina kuka dasu daga baya. Naji haushin wanan maganan na baba gaskiya sai nake ganin don mahaifan mu basu da rai ne sukai min hakan. Kwanana uku a gida kafin Jamil yazo da yannan shi maza inda suja samu baba ya aika a kirani da su anty muka samay su a falon shi. Baba ya bukaci in fadi magana na nan dai na shiga jero magana yan uwan shi sai assha suke fadi tare da fadin su basu san komai ba a kan wanan abinda na fadi jamil din yana min. Ranan dai ya jishi ba dadi do a gurin yaso yai ma anty da ta zake tana kokarin kwatar min incina a gurin shi don shi baba yana sakaya wani abu don shima nashi ne. Nan dai anty tayi mashi tas ta zage shi sosai saida ya raina kan shi sosai a lokacin suka dai ba da hakkuri tace zai karbo dinkin idan tellan daya kaiwa ya dawo. Aka ba da hakkuri ban koma ranan ba sai washe gari inda anty ta saka ai min kitson kaina da kumshi ta bani kaya masu yawa . Irin su zanuwan gada da kayan aiki da tufafi masu yawa da dare suka mayar dani dakina mun samu bai gidan har suka tafi bai dawo ba. Sai dare can ya dawo bai kwanta ba yai min dadin bakin shi daya iya yana fadin ya dauka ni mai rufa mai asiri ne ba zanje gidan mu da wanan maganan ba. Lokacin ne yake ban hakkuri kan kayan nan dai babu su inyi hakkuri idan ya samu hali zai saya min wasu da yardan Allah ya kare cikin dadin baki da bani hakkuri. Haka na hakkura na shanye zancen kayan a raina na dogara ga dan albashin dake zuwa min wanda yanzu munyi wata uku ba a bamu ko sisi ba na aikin mu. Haka nake ta faman kama kama ina juya rayuwa a yadda yazo mi din sai daga baya nake jin gaskiyan maganan a makwabtan mu . Wurin wanan kawar tawa take fada min yadda zancen yake inda take fada min itama a gidan da taje kitso don kawar matar ce bata san suna tare ba take bata labari na. Inda take fadin maza suna cuta wallahi don abinda akai min din ko da bata sanni ba na bata tausayi sosai raina naji ya baci sosai kafin ta gama bani labarin a gidan ta. Inda nayi mata sallama na fito ban zamay ko don ko gida ban shiga ba sai gidan da mahaifin shi yake na samay su da kuka ina fada masu abinda naji a gari dan su yayi min don ni yanzu kunyan in koma gida da wanan maganan nakeji. Budan bakin mahaifin nasa sai fafin yayi ina da aiki idan zanyi amfani da jita jita a rayuwana su masu fadin haka kyashine da hassadan dan shi yasa suke kulla mai sheri. Don kawai su bata wa dan baidai goyi bayana ta ko ina na fito sai ya tare dan nasa ya kare shi haka na taso da bacin raina na dawo gida naci kuka na ba wanda zan fada ma wanan zancen na takaici ya saurare ni. Haka ya dawo gida ya samay ni yana wani cika yana batsewa don ma kada inga fuskan yi mai magana ban kula yadda ya dawo min ba. Na shiga fada mai duk wani kalma daya zo min a baki akan indan har maganan dabaji gaskiya ne na roki Allah ya dubi maraicina ya saka min a gare shi shi da Ruth da duk wani wanda ke da hannu a cikin cutana din da sukayi. Ruth kan itama bai barta ba don tatsanta yake sosai yayi mata alkawarin zai aure ta idan ta musulunta duk da kusan haihuwan shi da tayi . Amma haka munafukin yayi mata alkawarin aure a tsakanin su take bude mai bakin aljihun ta yake shagali shi dashi don iya yaudaran shi da karyan shi. Da farko yaje gun Ruth ne ya tatsi banza ya gudu sai ya hadu da yar duniya dama tana neman wanda zata kama sai ta daure shi har kafa baida daman dogon motsi ya gudu gareta. Don ta dade da asirice shi yaje cin banza banza ta ciyo shi ga masifana a gida da nake aza mai tunda nasan bai rabu da ruth din ba na sashi gaba da fitina. Har ya fito fili ya nuna min ban isa in rabashi da ita ba wallahi haka muke zaune bani na samu kaina ba dashi sai da kudin da muke bin gwaunati ya fito na wata hudu sannan ya nemi shiri
Chapter 63 · 0% Book details