Sashe 45
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Ina zaune ina kare mai kallo yana shirin fita da yamma don duk yamma haka yake wanan al,adan ya tsala ado a jikin shi ga kamshin turare mai tsada yana tashi. Sai daya gama shirin shi yana batun fita nace gida nake son zuwa in duba su yau kamar baiji abinda na fada ba ya kara dauko kwalban turaren shi ya kara fesa ma jikin shi yadda yake so. Bakajini bane na fadi daga inda nake zaune ina kallon shi cikin tagumi yace najiki mana sai dai ban san abinda zaki je yi gidan bane. Zuwa zanyi in gaida su kawai don nasan in ka fita ba lalai ne ka dawo da wuri ba yace ni na rasa ma may zance maki hadiza . Wai da kike dadin zaki ki duba su ina ko dazun naga shigowan Baffa gidan nan shekaran jiya kuma summaiya sun zo nan gurin ki. Nace su kadai ne a gidan halan yace ke kika damu dasu su basu damu dake ba ni dai da zaki bi shawarana ki hade kan uan uwanki kuzama tsintsiya daya madaurin ku daya ku hudu da zai fi maki alheri. Nace ban gane may kake nufi ba har yanzu yace eh bazaki gane ba muddin baki kwantar da hankalin ki yanzu kin fahinci magana na ba. Don yawan zuwa gidan nan da kike yi ko wani lokaci yana daya daga cikin daman da zasu samu su cinye maku kudin ku idan ya fito nan gaba. Wani kallo na watsa mashi tare da fadin kudin ina baba kabiru ne mai muna fafutukan fito dashi yace ko yanayi ai da wata manufa yake yin su don shima ya debi rabon shi daga ciki. Kara mai kallon mamaki nayi don jin furucin shi akan baba kabiru din yace yes waye bai san da dukiyan ku yake tunkaho ba a garin nan. Sai ku da har gobe baku wayau da zaku gane hakan sai idan sun gama maku barna zaki dawo kina fadin dama na fada maki kinki ji a baya. Ni fa ban fahinci inda maganan nan naka ya dosa ba har yanzu zama yayi a kusa dani don ya fahinci banda saurin zurmawa idan ya tsarani da magana. Yace ni abinda naga yafi maku shine kiyi kokari ku hade kai da yan uwan ki tun yanzu ta inda bakin ku zaizo daya a kasa gane tsakanin ku. Nace ai muna hakan ko yanzu wani shu,umin kallo yayi min tare da fadin ke har yanzu dai yarinya ce hadiza ana gabas kina yamma ni zan fita idan na samu lokaci zan maki bayani a tsanake. Daga haka yasa takalman shi ya fita kallon inda yaci abinci nayi naga ledan kazan daya shigo dashi da rana yaci yashe saman dan table din da muke cin abinci a falon namu. Naja tsuki tare da mikewa ina duba ledan kazan na samu ya rage dan guntu a ciki zama nayi na karasa cinye sauran tare da sude kasusuwan da bai karasa cinye tsokan su ba na gama na kwashe kayan na fita dasu. Gyaran daki nayi na fita gurin girki na don kada yamma yayi min don nasa a raina yau zan shiga gidan mu da dare. Da sallama na na shiga gidan namu inda na samu yan gidan mu a dakunan su suna kallo da murnan ganina kowa ya tare ni muka shiga gaisawa dasu. Sai da nabi da kunan matan baba na gaidasu na dawo dakin yan matan gidan mu na zauna muna hira sai tsokanana sukeyi wai ciki yasani muni. Anty ne ta shigo dakin ta zauna don ganina a cikin dakin tana fadin wai ke haka zaki haihu daki ba komai a cikin sa har yanzu hadiza. Ko kun gyara dakin naku ne yanzu muzo musha kallo mu kan tana fadi a cikin zolayata don takanyi wasa damu wani lokaci. Fadin haka yasa kanwata fadin wanan shegen macuci ai itace ya samu har ta yarda da hakan idan da nice wallahi sai ya fito min da kudin kayana wallahi. Take na daure fuska don jin ashar din data dura ma Jamil dina alhalin yanzu ya gama maganan alheri a kan mu. Sai anty ne tace kuna zagar mata miji a gaban ta yanzu kuna samun sabani a gidan nan bandai sake fuska ba har lokacin har ta gama dan hiran da mukeyi sama sama da ita a dakin ta fita. Can takira yarta dake dakin tare damu tayi mata wani abu lokacin na samu fadin yanzun ke da kanki kikewa Jamil haka idan wani yai min ashe ba zakiji haushin sa ba summaiya. Tace wallahi halin mijin nan naki yana ban haushi anty dubi yarda kika koma don Allah kamar wata bakauya dake don babu mai kallon ki ya dauka wai kin yi karatun boko. Nace to ki matsa kowa bada yadda Allah ke masa tsarin rayuwan sa ba ko kin naso ne in dawo wanan gidan ne kuma mu kama ganin laifin juna daku. Nan dai na nuna mata bacin raina akan abinda tayi min din har sai da ta bani hakkuri na sauka nace da ita ta samu lokaci ina son ganin ta ita kadai idan zata zo kuma ta zare jiki tazo ita kadai tace min taji. Ina shirin komawa baba ya dawo do yayi tafi ashe kwana biyu bai gidan yana dawowa muka fita muka gaida shi yake fadin a,a hadiza kin shigo ne ? To ya kuke ya mijin naki na amsa da suna lafiya suna gaida ku baba yace lafiya dai ko nace lafiya baba na daizo gaida ku ne kwana biyu ban shigo ba na duba ku. Yace cikin nuna jin dadin shi ga hakan mun ko gode naji dadin hakan sosai adaita hakkuri don Allah komai na duniya sai da hakkuri ake cin riba nace na gode baba daga inda nake tsugune. Har na mike ya sake fadin ina ganin kwanan nan zancen kudin ku zai tashi don munyi magana da wanan mutumin dake muna hanya kudin su fito a cikin jin dadi nace Allah ya nufa baba na kara mai godiya. Na fito ban dade kwarai ba don daren da yayi na yi masu sallama na nufi gida sai da yan gidan mu suka rakani har gida muna hira suka juya suka dawo gida. Har lokacin na sami Jamil bai dawo gida ba nima ban sa rai da zai dawo haka da wuri ba don sai dare yayi sosai yake shigowa gidan. Washe gari ya gama barcin shi karfe goma da wasu mintina ya bukaci ruwan wanka na kai mashi bandaki kafin ya fito na aje mai abin karyawan shi ko a inda na saba aje mai ina gyaran gida ne ya kwala min kira. Nazo yake fadin wa zai sha maki kunu haka babu sugar ko kosai nace yau baba bai sawo muna kosai bane kuma sugar ya kare tun jiya na fada maka. Ya ja tsaki tare da rufe kwanon kunun ya dan mayar da kan shi saman kujera fuska a daure nace jiya naje gida baba yana gaida kai ya mace wai kudin mu ya kusa fitowa. Wani irun dagowa yayi daga yadda yake kwance yana fadin saboda Allah nace wallahi ko jiya baba yake fada mi hakan da naje yace ashe mun kusa warkewa ke nan nace insha Allahu. Nan ya fara sake min hira a ciki sakin fuska inda yake shiga ba nan yake fita ba jin dadin hira yau yasa na sako mai zancen da anty tayi min. Take ya bata rai ya fara fada yana fadin ina ruwan ta da rayuwan mu ne nifa kwata kwata wanan matar batai min ba a rayuwana nasan duk wani cin amana da baba keyi da zuginta ne yakeyin shi. Nace niko banga hakan ba gaskiya don bata saka kanta a cikin maganan mu yace ke may kika sani so take kowa ya koma yadda take wai ita ta waye din nan . Ranan kan hirane zamzam dashi ba wani nuna bacin rai a tare dashi fitan da baiyi ba ke nan har mahaifin shi yana tambaya ko lafiya yake gida har yanzu. Yace lafiya yana dai hutawa ne a gida yau tun wanan ranan muke zamzam dashi kanwata tazo na danyi mata nasiha kamar yadda Jamil din ya lurar da mu muyi din. Bata ki ba sai dai cewan da tayi amma kada mu nuna yadda har za a fahince mu a gida tun daga wanan ranan muka dinke tam dani da yan uwana da muka fito ciki daya. Babu mai gane jan mu komai namu a hade mukeyin sa a gidan ga summaiya Allah ya dora ma anty sonta a rayuwan ta komai ta samu ko zatayi sai tace summaiya dai har yan uwanta suna sata gaba akan hakan da take nuna ma diyan cikin ta bata damu dasu ba sam. Bayan kamar sati uku dayaji shiru shi da kansa yace mu shirya muje mu gaida mutanen gidan namu nayi mamakin haka sai dai naja bakina nayi shiru tunda gidan mu zamu tafi. Mun samu baba a gidan ya tare mu a cikin fara,an nan nasa suka dan taba hira da Jamil din ina gefe ina jin su sai dan zungura na Jamil keyi akan inyi maganan kudin mu mana a gurin baba don ya gama kitsa min abinda zance tun a gida gamay da kudin da mukaji shiru. Can nace baba har yanzu dai wanan mutumin bai kira ba ko cikin mamakin wani mutumi nake nufi baba ya tambaye ni nace wanan mutumin da zancen kudin mu ke gurin shi baba. Baba yace wallahi har yanzu banji wani abu a guri sa ba amma dai barin kira shi muji yanzu komay ake ciki akan zancen nan ya daga waya tana ringing gab da ta katse ya dauka. Suka gaisa a cikin harshen turanci suke magana baba yace yaji shiru yace eh kasan abin da wuya amma dai insha Allahu ana sa ran fitowan shi a cikin wanan shekara din sai dai kasan ba duka yake fitowa ba za a kasa shi kamar kashi uku ne haka. Baba yace haka abin yake yace yadda tsarin namu yake ke nan ai dama sukayi sallama bayan baba yayi mashi godiya ya katse layin tare da dubo mu yace kunji ko.