Sashe 64
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read
dani don yaci kudina. Ya ko ci don nan ya kawo min kabali da ba,di bamu da kaza ya kamata mu sai kaza na amfanin mu shi nashi bana lalurar gida bane sai nawa idan sun zo ake sakawa a gaba a cinye anga banza. Niko ban gane shi ba har yanzu ina dauka sona yake tsakani da Allah sai nake sakar mashi komai idan yai min dadin bakin su na maza. Na ramay na lalace ni ragga diyana ragga duk mun bi mun kanjamay don wahala gashi dan aikin da nake kuri dashi an dakatar da yin shi yanzu. Sai abin ya taru yai min yawa sosai a kaina dole naje gida wurin anty don ta taimaka min tasa baki ga kanne na su bani dan wani abu in sai ko kura na ruwa dan kwabo ya dinga shigo min. Da kyat da boni anty ta yarda zata sa mun baki gare su duk ko da tasan abune mai wuya a banbare su kudin da nake so. Amma haka ta daure zatayi masu magana idan sun shigo shikan baffa tana tun karan shi da zancen yace ba zai bayar ba. Sai dan karamin mu ne da anty ta titsiye yace zai bani dubu goma tace bai yi ba don Allah su tausaya min idan basu koyi bani ba yanzu yaushe zasu koya. Haka dai har ta ciwo kanshi yace zai bani sha biyar lokacin daidai kudin baron ke nan nayi ta murna da ta fada min. Inda ta zaunar da kanne na tayi masu nasiha sosai mai ratsa jiki duniya ke nan wace Jamil ya cusa muna ra,ayi mu guje ta itace kuma yau na komawa ta taimake ni. Ba tare da tayi duban baya ba ga komai ta tausaya wa hali da nake ciki tasa ai min wani abu a tallafa ma rayuwana don Allah. Baron ruwan da na saye baiyi wani tasiri ba duka duka baifi wata ba na kadar dashi na fara sana,an kayan mata da dan kudin. Wai ni a gani na zaifi sana,an ruwa kawo min kudi a cikin lokaci kwana biyu muka turmushe kudin babu ko labarin su kuma. A cikin haka ne su maman Ahmed yan hayan gidan mu suka tashi don zaman mu yaki dadi dasu ga matsin jamil akan shi fa sai dai su bar muna gida. Do sune ke zugani ina wani abin don shi bai kaunar yaga nayi wayau a rayuwan shi yafi son ya gannin ko yaushe kamar wawiya yana juyani yadda yake so. Tashin su ba a dade ba aka sa wata amarya a dakin da suka tashi ciki amaryan matar abokin Jamil ne yasa muke kuma dan shiri da ita. Wanda hakan yasa na dan samu sauki wasu abubuwa a gidan yanzu don yana ganin yadda abokin nasa ke kula da matar shi. Sai dai abinda ba halin mutum ba bai iyayin kamar kowa don bai saba yin hakan ba tun farko ina dai zama zamana hakkuri dashi. Shiko yana holewar shi waje da matan banza yau ma kamar kullun na tashi babu ko sisi a hannuna ga yara na har sun fara min kukan yunwa. Na rasa yadda zanyi dasu a daki can dai dabara ya fado min wanka nayiwa yaran babu ko sabulu na shirya su muka nufi gidan mu dasu. Bayan mun gaisa ake tambayana inda na fito da sanyin safiyan nan nake cewa gida ganin yanayi na baisa sun matsa da dogon bincike a kaina ba sai abin karyawa aka gabatar min dashi. Na dan tsaya basarwa mama ta matsamin akan in dai karya din don ban samu anty a gida ba lokacin tana gurin aiki sai mama ne a gida kawai. Nan dai na fara labarta mata halin da muke ciki a gidan ina kuka tace in daina kuka nawa kaddaran auren ke nan yazo min a haka. Hadiza kina da hankali da ilimin ki zaki zauna kullun miji yana cutan ki kin kasa wayau ki fahinci abinda yake nufi dake. Fada sossi mama tayi min ban iya magana ba sai kukan da nakeyi har barci ya daukeni a gurin ban koma gida ba anan naci na safe dana rana har anty ta dawo daga aiki ta samay ni a gidan. Kallo daya taimin ta gane halin da nake ciki bayan ta idar da sallah la,asar ta fito ta samay mu nan dai ta shiga min nasiha inda duk laifin a kaina ta dora inda ta kare da fadin idan naga dama in koma in kara bashi kudin don yanzu ba abinda ma yarage ai. Na samu ta hada min abubuwa na koma gids na girka muna abinda zamuci da dare dani da yaya na sai gashi ya shigo dauke da dan leda a hannun shi. Lemon sha ne ya zauna ya bare ya min mikawa yayan shi bari ya shiga shan abinci sai da ya gama yayi gyatsa yana kaiwa kwance saman kujera ya mimike sallah na idar idar na jawo kullan abinci ina zubawa don in ci yace ina kika samu abinda kikai abinci ? Ban saurare shi ba saboda haushin shi da nakd ji a raina yaya nami zai fita tun safe bai damu da yasan iyalin shi sunci ko basu ci ba.