← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 83 OF 89

Sashe 83

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Wanda baba ya kira a waya ne yake ta faman magana a cikin wayan sai da baba ya tsnkayi muryan kamar daga sama mutumin na fadin hello hello ya karba shi da sauri tare da fadin. Hello mr Josua mun tashi lafiya ya iyalinka mutumin ya karba wa baba don wayan a handfree take a lokacin kowa najin mutumin a lokacin. Baba yace mr Josua dama akan maganan kudin yaran nan ne don Allah nawa ne kudin karshe da aka turo masu nan mutumin ya shiga yin bayani dala dala a waya yadda kudin suke a yadda zamu fahinta. Yana gama bayani yace ihope ba wani matsala aka samu ba dai ko baba yace yarinya tace abinda ta gani matar nan ta nuna mata miliyan goma sha shidda ne . Jesus mutumin ya furta da karfi lokaci guda tare da fafin ai duka kudin ma idan an hada bai kai haka ba sai kace kudin wani IG ko commitioner. Nan dai ya kara bayani baba yai mai godiya ya kashe wayan tare da fadin idan ma baku yarda ba ga nomban mutumin zaku iya kiranshi kuji karin bayani a gurin shi. Sai baffa yace ta yaya zataga abu a rubuce yanzu kuma ace ba hakana bane ? Innalillahi inji baba kabir Baffa nine kuma zan cuta maku yau kan kudin ku yace baba ba hakana bane don za a iya canza digit din kudin su rage babu abin da ba a iyawa gaskiya. Hawaye ke zuba daga idon baba kabiru na bacin rai kan maganan da mukayi yanzu a gaban kowa yace cikin wani murya mai ban tausayi ga mai saurare. Josua ko zaka iya hada ni da wanan matar da ta bamu takardu muka cika ranan Josua yace kwarai kuwa tana nan office din ta ai bara nakai mata wayan. Dan shiru ya biyo baya kafin ya kai ma matar wayan ta dauka muna ji ta dauka baba ya fara tambayan ta da fadin ko zaki duba muna takardan mu ji nawa muka saka hannu a kai. Ta duba tace miliyan shidda ne kamar yadda baba ya fada muna din nayi caraf nace ba naka sha shidda a waje farin rubutun kudin ba ? Dariya mai ban haushi sosai matar ta kwashe dashi sosai muna jin ta a waya tare da fadin amma ke kina da abin dariya fa. Luckly muna da komai anan a cikin computer mu muna reconding idan zaku iya zuwa kuzo ku duba da kan ku wanan lamban da kike magana. Shine serial nomba na kudin ku nan ta kara karanto min shi wanda shi din ne na gani a can sai nace bashine kika ce min kudin namu ba. Tace ke mahaukaciyar ina ne da za a baku wanan kudi haka mai uban yawa kiyi abu na masu hankali mana. Zaku iya zuwa ku duba komai na nan wurin mu a rubuce cikin computer mu kuzo ku duba shaaa ta katse wayan. Muryan baba musa ne ke fadin assha wanan hali a ina kuka samay shi ne haka kan kudi ku rufe ido kuciwa kowa mutunci wanan bawan Allah idan baku gode mashi ba bai kamata ku nuna mashi haka a fili ba. Baffa yace baba ba hakana bane shi sharian kudi idan yazo ds kowa kana iya yin sa ai mu abinda ta fada muna ne ta gani muka sa rai. Baba kabiru dai bai iya fadin komai ba lokacin sai hawayen da yake sharewa baba yushau yana bashi hakkuri kan maganan. Nan dai baba musa ya zage mu tas yasa mu bawa baba kabir di hakkuri wanda har muka gama ya kasa furta komai gare mu. Haka muka fito rai a bace don kudin ba suyi muna dadi ba kamar wa yanda suka sai da wani abu a kasuwa ba mahaifan su ne suka rasu ba. Gidana muka nufa da kudin kai tsaye inda muka samu Jamil yana jiran mu a kage dashi kamar yai tsuntsuwa ya bimu gidan baba din inda ake rabon kudin. Muna shiga yana ganin mi rai a bace yake fadin yaya akayi baffa ya ce kai rabu da mashiririciya kawai taje ta sa mutane a ciki kawai ashe ba haka na bane abin. Nan ya tare shi da fadin kai abi abin nan a hankali zaku gane gaskiya fa ba abinda ba a iyawa yanzu wallahi. Kana ganin ba hadin baki akayi a rage kudin ba a baku abinda bashi bane wai ma nawa ne suka baku wai ? Baffa yaja tsuki ya mike ba tare da ya fada mai komai ba ya fice daga gidan . Kallon mamaki Jamil ya bishi dashi har ya fice nan dai ya sakani gaba na fara mai bayanin shiririta cikin rashin fahinta. Yace kai ina ba za a yarda ba wallahi zanbi in gani har sai na gano gaskiyar wanan maganan sai kudin nan sun fito wallahi. Yace bari in nemi layin baba hamza wani dan uwan mahaifin mu dake aikin yan sanda shima a sokoto ne ya mike ya fita. Don zuwa nema layin baba namu dake sokoto ya fita bai dade ba ya dawo yana fadin na samo layin baba hamza barj in kira baffa yazo muji yadda za a yi. Ya zauna yana kiran layin baffa din har ya katse bai dauka ba ya ha tsuki ya kasa hakkuri ya kira layi wanan baban namu na sokoto can ya dauka. Kun san mutanen yanzu sai a hankali maimakon ya gyara zancen sai cewa yayi da Jamil tunda ta fadi haka ta ganine. Ni yanzu abinda zanyi shine zan nemo maku wayan wanan da aka saka gaba wurin fitowan kudin ku don muji gaskiyan maganan. Idan ya kama kuzo ne sai ku shirya kuzo ku samay ni nan sokoto muje office din da ake abin muji komai. Basu kashe waya ba suka shiga zagin su baba ina jin ban iya daukan matakain komai ba akai don nima a lokacin na hau sosai dasu a raina. Nan dai muka bar zancen iba batun tashi in fita naji yace to yaya ake ciki ne wai banji kince dani komai ba har yanzu mana ? Dakatawa nayi nace kamar na may fa yace a dake ba a baki kudin bane ko may nace ambani mana amma duka suna gurin baffa ai bai ba kowa nasa ba tukun. Kamar ya suna gurin Baffa kudin ke baki da laluran yi da kudine da zai rike maki kudi ko rainin wayau ne kuma yin hakan ? Nace suna dai guri shi ya rike baice dani komai ba har yanzu gaskiya yaja wani guntun tsuki ya mike yana fadin an sa muna da lalurar kudi zai wani rike kudi a hannun shi. Ko ya fiki sanin duniya ne da zai wani rike kudi a hannun shi yana karami gare ku kuma nidai tunda na fadi hakan ban kara mai magana ba. Sai dai nasan da wuya kudin nan su shiga hannun shi yadda aka saba don Baffa yasha alwashin shi zai rike namu din gaba daya dani da kanwata . Washe gari da muka tashi da wuri ranan Jamil din ya tashi yana tambayana ko baffa yazo a daren jiya wuri na ?. Nace tun fitan nan da yayi ba sake shigowa ba har yanzu ya ja tsukin da ya saba ja din kamar ko yaushe. Kafin karfe biya ya tambaye ni sau ba adadi ko Baffa din ya shigo nace bai shigo sai ya ja tsuki ya fita. Yinin ranan nan ya zauna a kofan gidan yana hira a camban yan unguwar wanda nasan zaman jiran Baffa yake ya bullo. Sai yamma lis Baffa din yazo gidan yana hango shi da kyat ya daure ya jira karasowan shi inda inda ya dan tsaya na wani lokaci har ya dan bada time kada aga gazawan shi. Tunda baffa din ya shigo muka gaisa nake tambayan shi ko yaga Jamil din a waje yake tambayan may zan mai idan na ganshi. Nake fadin kai yake jiran zuwan ka tundazun ai yaja tsuki yaci gaba da min bayanin abinda suka tsara da sauran yan uwana. Kan mu mata zamu bada dubu ashiri su maza dubu hamsin a rabawa yan uwa na birni dana kauye mazajen mu kuma dubu hamsim daga cikin kudaden mu . Sauran zai aje muna a gurin shi ya duba abinda ya dace asai muna dashi don gudun tabarbarewan kidin a hannun mu. Ban kai ga magana ba Jamil din ya shigo gidan yana fadin Baffa ka shigo ai dazun na kira layin ka bai shiga ba tunda safe nake gwada layin naka. Yace eh barci nake da safe na kashe wayana ne Jamil yace dama akan maganan kiran baba hamza ne don na samu layin nasa har na kirashi nayi mai bayani . Amma yace hakan ba gaskiya bane don hakama ba zai yuyuba tunda tagani a rubuce lalai an rage kudin nan ne anbi wani hanya dasu. Tsuki Baffa yaja tare da fadin kai wanan maganan a barshi kawai, don Allah, ba kamshin gaskiya ga maganan ta ko kadan . Jamil yace a, ba hakana bane kada kayi mamakin sai azo abincika kaga kudin sun fito daga baya don sun mayar da ita mace ce kawai wallahi ya kawo haka. Ni tun farko ban so aje da ita wanan tafiyan ba ita kadai haka, na riga da munyi magana da mutanen sun ce muna iya bi hakkin mu. Wani kallon kai din Baffa yaiwa Jamil tare da fadin da kudin wa zakuyi wanan hidiman haka yana fadin haka ya fice yana dariya. Ina zaune ina sauraren su, nan dai ya bi Baffa din zuwa waje sin dade suna magana dashi koda ya dawo naga fuskanshi a daure . Sai dai yana ga bakan shi na son abi kidinkidin din kudin da yake tunanen an lake muna a sokoto. Yana wanan maganan sai dai hankalin shi yana gun kaso na da baiji labarin shi ba har lokacin don haka a cikin dare ina barci ya tutseni ta hanyar tayar dani daga barci. Sai na fada mai ina kudina suke akan may ba a bani ba yadda aka saba bani nawa a hannu na da farko wanan karon aka hana min. Nace suna gun baffa
Chapter 83 · 0% Book details