← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 6 OF 89

Sashe 6

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read

take shiga banan take fita ba. Mama dai bata tanka mata ba don ba sa,an yin ta bane koma sa,antane ita fitina ba abin yin ta bane da mutane shiyasa umma ke jin dadin kara cusguna mata duk cikjn sarakan nata. Don rashin hayaniyar ta da umma ke kira da duk munafunci ne hakan don ta yi gadon kili bibi daga wurin uwarta wai da haka uwarta ta watsa gidan dan uwanta. Duk da karancin shekaruna ina jin zafin irin abinda umma takewa mahaifiyata a gidan don abin yana ci mun rai kun san diya mace da tausayin uwar ta. Baba kabiru ya dawo gida da yarinya yana fadin kyanda ne ke damun ta an bata allurai da sauran maganunuwa umma dake dakin ta tayo zubur ta fito daga dakin ta tana fadin . Ba kaji ba gurin yayeyayen ta ta kwaso ma ya wanan bala,in yanzun ta bar mutane da wahala kashin kudi kai baba kabiru ya girgiza ya mikawa mama yar tare da mata bayanin maganin da yadda zasu yi amfani dashi. Mama tayi mai godiya ta karbi yar yana fadin Allah ya bata lafiya ya fita a tsakar gida ya tsaya suna magana da umma dake ta fada da mama. Yace umma ina saude ke zuwa kullun saude na gidan nan ba kamar sauran matan gidan nan take ba da ke yawan fita unguwa koda yaushe. Baku bari a fadi ai shiyasa take jin dadin maku makircin ta don kuna karba yanzu wanan kudin da kaje ka kaso wa yar nan da na gargajiya kazo aikai mata ai da kun amfana da kudin. Ranan dai umma tayi jinini sosai kan kai shamsiya chamest din da baba kabiru yayi kamar a aljihunta yayi wanan lalurar. Jikin yarinyar ya matsa sosai ana magani kamar ba ayi sai da takaisu ga kwanciya asibiti kafin ta samu sauki aka sallamo ta sai da umma tayi ta jininin kwanciya asibitin nan har ta gaji. Wai ni da wani zamu ji da fitinan umma ko da ciwon shamsiya mama nake kallo dake kwala tana shafa ma shamsiya magani. Ban san lokacin dana bude baki nace kai umma fada fada wallahi da sauri mama ta dago kai da fuskan ta dake shabe shabe da hawaye tace kul kul na kara jin wanan maganan a bakin ki. Da sauri na ja bakina nayi shiru don tsoron fushin mama a kaina na fice daga dakin simi simi dani zuwa waje na rakube don tsoro. Da kyar Allah ya taimaka shamsiya ta fara mayar da jikin ta a hankali sauki ya fara samuwa wa yar kanwa ta har ina daukan ta muna dan fita mama ta samu tayi aikin da zatayi. Zuwa makarantar kauye sai a hankali don sai munga daman zuwa muke zuwa idan kuma bamu ra,ayi umma tace a barmu karatun ya mace ai ba dole bane sai mace tayi karatun zamani. Nafi kowa son zuwa makaranta don haka tsana na da take ya karu a wurin ta sosai har da mahaifina data haifa takan hada tayi masu gori idan bakin halin nata ya tashi. Kowa a gari yasan halin umma da fitina don haka mutane ke kiyayan ta sai wanda Allah ya nufa ya fada tarkon ta ranan zai sheda fitinan ta. Tana matukar son matar baba kabiru da yaran shi duk daba wani dadin take samu ko biyaya a gurin matar ta baba kabiru ba. Yau mama wanki take yi don rashin lafiyan shamsiya ya hanata tayi muna wanki kwana biyu haka yasa mama tayi ranan kare girkin ta da ta saba gamawa a cikin lokaci. Umma na tashi daga barcin da ta dan yi na rana wanda a saman gira take yin shi don ko kaza ta gitta ko dogon motsi ta sani balle wani yazo yana magana da mahaifiya ta sai tace gulmanta suke yi. Ta fito daga daki tana gyara daurin dan kwalin kanta takai duban ta gurin girkin mama din tace wai ni ba a aiko min da abinci na bane yau ko ban samu bane don banda hakki a ciki. Mama ta dago daga duken da take tana fadin umma ban karasa bane yau wankin kayan yaran nan daya taru nake yi kwana biyu ban samu yin wanki ba don jikin shamsiyan. A,a dai inji umma don dai ba uwarki nake ba yasa zaki barni da yunwa har wanan lokaci da kinsan darajana da mutunci na ai ba zaki maida hankali gurin wankin kayan diyan ki ba ki barni da yunwa. Murya a sanyaye mamatace umma kiyi hakkuri iccen ne baya kamu sosai taja tsuki tace haka kuke ai matan yanzu da shegen kiuya gurin aiki. Kwala min kira tayi in zo in karbo mata goro wurin mai tiredan unguwar mu inda take saya sai da tayi min kashedi tare da dangwara ta mika min kudin goron. Illar ya jani ina fita na hadu da kawata hafsa an aketa tace in rakata idan mun dawo sai mu sayo goron mu kaiwa umma har naso na kiya don tuna halin umma . Sai dai jin gidan da zata yasa nace muje in rakata din don ina son zuwa gidan kanwar mahaufiyar hafsa gida ne daya fi ko wani gida a gari kkyau gashi idan munje bamu fitowa sai ta bamu wani abu da bazamu manta mun je gidan ba. Mun zauna harda cin abincin mu hankali a kwance kamar ba nice masifafiyar kakan mu ta aika ba tare da jan kunne kada in dade gurin aiken nata sai gashi duk gidajen dake makwabtaka damu umma ta shiga nema na ance ban shigo ba. Sai da muka gama kwadiyan mu muka tun karo gidane na tuna da zancen aiken umma gabana ne ya fadi na lalaba aljihuna naji gudin suna nan inda na aje su kudin da aka bamu ne na kara na sai mata goro manya guda uku na tunkaro gida da murna na. Ina sallama ta lalayo min wani uban ashar sai da na girgiza tazo kamani na gudu ta buge baba kabiru dake dakin shi ya fito yana asha subbanallahi umma ya akayi haka ya faru kuma. Ta mike da kyar tana fadin banda yar banzan nan da na aika tun dazun ta sayo min goro nan da shagon awali mai tireda ta tafi gantalin ta sai yanzu na ganta. Juyowa yayi gare ni inda nake tsaye ina kyarma cikin sanyin murya yace hadizatul kubura ina kika je da umma ta aike ki ne tun dazun. Dan kwala na fara kiu,kiu da idona ina kyarma a cikin inda inda nake fadin hafsa ne tace in rakata gidan mai kare an aike ta tana jin tsoro shine muka je tare. Baba yace watau kice baki jin tsoron karen ko hadizatu nayi narai narai da manyan idanuwana yace kinci abinci kai na gyada mai yayin da umna ke fadin ina fa taci tun kan muguwar uwata ta kare muna girki na aike ta fa. Haba umma may ye laifin saude a wanan magana don da zaki tona zuciyar saude da kinga rashin jin dadin abin da yarinyar nan tayi yanzu. Kiyi hakkuri umma tunda bata taba aikata hakan ba yau ne ta fara don Allah kiyi hakkuri kada ki dake ta. Wani kallo tayi wa baba din dake magana a cikin tsigan lalashi tace gidan uban wa kika ci abinci bakin ki haka duk maiko. Na dukar da kaina kasa ta kara daga murya tana tambayana da karfi da sauri na dan girgiza tare da fadin can ina nunawa da hannu. Oh kin fara yawon kwadayi gidajen mutane ki nuna wa duniya ubanki ya watsar daku a gari kuna gararanba kai kai haba umma wanan maganan haka ina yafito maki kuma haka ,? Dan naki ne yaje yawon gararanba ya watsar da iyalin shi da yawon gararan ba yake zai dawo muna da abin arziki idan ya tashi dawo haka. Umma idan wani ya fadi haka yaya zaki ji a matsayinki na mahaifiyar mu duk gari an san ida yake ansan kuma aikin da yakeyi a can. Jikin ta ne yai sanyi don itama din dai tuntuben harshe tayi wanan maganan ya fito saboda masifan ta har ta kai ga fadin hakan. Ta kama kamay kamay tana fadin bafa haka nake nufi ba yaya zan wa dana wanan kalamin da ita dai nake da wanan mai manyan udanuwan nake magana tana nunani inda nake tsaye. Ina aiken da tayi maki baba yake tambayana ledan dana dunkule na saka a aljihuna na ciro na mika mai ya karba ya mika mata ta karba tare da kutawa tana fadin yau kin kuru wallahi. Tana magana tana kallon goron nace na hada da kudin da hajiya ta bamu na sayo maki duka rufa min baki tace cikin tsawa na dan kara ja da baya. Umma har yanzu fadan bai kare bane duk da kudin da ta samo wurin rakiyan aiken ta nayi da zata ce ta cika min. Juyawa baba yayi gurina yana fadin ke kuma daga yau idan kin kara wuce wurin da aka aike ki sai na yanke maki kaunan ki gidan nan da sauri na daga kaina alaman naji ina kyarma yace shige shiyan ku maza sai da yaga na shige wurin mu ya ja ya wuce.
Chapter 6 · 0% Book details