Sashe 24
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Bamu dade da dawowa daga gida ba sati daya na kara na koma school don na samu baba ya gama min shirin komawa makaranta. Nan na bar kanne na da gwagon mu da muka zo da ita na barsu ban gama fahintar yadda rayuwan ta yake da yadda zata zauna tare da yan uwana. Don hankalina sam bai kwanta da yanayi wanan matar ba don ina ganin zatayi fada don haka zata kwasa da kanne na a gida dana barsu tare. Ban yi wani nisan zango ba mahaifina yakawo min ziyar sai dai na kula ya danyi rama kadan da baki wanda na dauka duk yana cikin damuwa rashin mahaifiyar mu da yanayin da yake ganin mu a ciki na ban tausayi. Ga maganan auren shi tun bayan rasuwan mahaifiyar mu bamu kara jin magana ba a gidan itama kanta ta rage kiran shi kamar baya can. Ashe rikici suka yi da ita wai ba zata zauna ta dubu yaran shi ba shikuma ya yace ba zai iya rabuwa da yaran shi ba gaskiya. Shine rikicin da sukeyi a tsakanin su har ya kawo tsaikon auren mukaji shiru zuwa wanan lokacin don mun ki jinin matar tundai kauna ta summaiya bata kaunan ai maganan karin auren baba a gaban ta ko kadan. Yanzu zata kama zagi tana aibanta matar har wace ta hada auren zata zage ko a gaban waye duk da ba wani shekuru ke gare ta ba amma akwaita da tsananin kishin tsiya. Ita a dole tana taya mahaifiyar mu kishi tana fadin ai da baba baiyi zancen auren ta ba lafiya kalau maman mu ke haihuwanta. Wanan ke nan wanan time din mun dawo gida na samu kanne na sun rama sunyi baki raina ya baci da ganin hakan ko ban tambaya ba nasan zaman su da gwagon namu ne babu dadi. Mun samu kebewa da sune suke fada min ciwo sukai tayi har da kwanciya asibiti nayi masu sannu baba ma yai min bayanin irun ciwon da sukayi a bayana din sosai. Abin farko dana fara kula dashi wanan gwagon tamu sam jinin mu baizo daya da ita ba idan ina falo tana daki idan kuma daki nake ita tana falo don a dakin mu ta sauka. Ranan cikin dare ina barci na falka na ganta tsirara tsaye da wani kwarya a kaina wani irin ihu na yanka gashi mahaifin mu baya gida yana aikin dare ne ranan. Ihu na ne ya tayar da yan uwana a tsorace duk da basu san may ya faru ba suma suka shiga tsoron a lokacin. Ban iya fada ma kowa abinda ya faru ba ranan sai dai muna yar tsama da wanan matar da aka kira da gwagon mu mai zama damu. Sai ta so ta dora min tsangwama tana fadawa mahaifi mu wai ina mata rashin kunya nan zai kamani ya zage ni fes a kanta. Abinda bamu sani ba ashe matar manyace aka dauko aka kawota zama damu abuja cikin rashin sani wanan yawan ciwon da yan uwana ke fama dashi duk itace ummul,abasin ciwon su. Kwatsam sai ga umma ta dira abuja kamar daga sama tana zuwa matar tasha jinin jikin ta nan umma ta shiga yadda magana kamar haka. Mugu sai dai ya harari kayana ya barshi, idan yace zai taba kayana sai dai su tafi tare da maishi banci dan kowa ba babu mai zuwa ya taba min nawa. Idan mutum yace shi takaman shi sheri ne ya zo karshen sheri a rayuwan shi don asirin shi ya kusa tonowa a garin nan ire iren maganganun da umma kan zauna a falo tana sakewa ke nan. Idan baba yana gida zai tambayi umma wai da ita da waye take wanan magana haka sai tace mai ya barta ta fadi ai mashi yasan kanshi. Ranan dai gwagon ta tayar da hankali wai zata koma gida tunda umma tazo dama don babu kowa tare da mune baba kabiru ya roketa tazo. Batai wani kwanaki ba ta tafi ta barmu bayan baba yayi mata goma sha tara na arziki tana ta godiya aka sakata a mota da zai kaita jahan mu. Ranan ne umma ta zauna da baba tana fada mashi mugun halin gwagon namu da taji daga baya wanda hakan ne ya tayar mata hankali ta biyo mu. Mahaifin mu dariya yayi yana fadin may yasa kuke yarda da irin maganganun nan don Allah wanan duk camfine wallahi. Nan nake fada masu yadda na ganta ranan da bamu kara shiri da ita ba har ta tafi ke nan umma tace kaji ba aniyar kura ta bita ba a cikin kayana ba kan. Na koma school na bar gwagon mu a nan inda wanan zuwa da yar gurin baba musa tazo sai da mahaifina ya nuna rashin yardan shi akan zuwan da tayi da yarinyar da farko. Don shi bai ra,ayin rike dan wani a rayuwan shi yasa nashi ma bai yarda yan uwa suka dauka ba ina makaranta ne ciwo ya kama mahaifin mu lokacin mahaifitar mu tana da shekara biyu da rasuwa ke nan. Sai dai bai kwanta ba tsatsaye yake jiya muna samun hutun makaranta umma tace tunda yaji sauki gida zatazo damu mu kwana biyu. Mun dawo gidane muka barshi can sai kuma ya samu sauyin wurin aiki ya koma Niger state da aikin shi satin mu uku da zuwa gida ke nan ya samu wanan sauyin. Lokacin ne abubuwa suka taru sukai mai yawa dole yazo yayi reporting don kada ya samu matsala satin shi biyu a minna har ya samu gida inda zai zauna da iyalin shi sai kuma ciwo ya dawo mashi sabo. Da yan wuein aikin sukaga ba zasu iya ba aka tada mota a kawo shi gida wurin iyalin shi da yamma lis suka iso wurin baba kabiru dashi. Hankalin baba kabiru ya tashi sosai yadda yaga dan uwan shi ya koma a lokaci guda ciwon dai baiyi kama dana asibiti ba sam. Haka dai suka dauke shi zuwa asibiti suna hadawa dana gargajiya da farkon zuwan shi yana magana don har yana ma baba kabiru bayanin yadda yake jin jikin nasa a lokacin. Nan dai baba kabiru ya gane abin kamar sammune akai mashi hankali ta kara tashi sosai umma ta samu labarin ciwon nasa inda hankalin ta yayi matukar tashi da zancen. Washe gari ta shirya sai birni inda baba yake kwance a asibiti jikin ba sauki addua,a tayi mai ta dawo gida da yamma lis babu wani walwala a tare da ita ko kadan. Mun taru a dakin ta don son jin yaya jikin mahaifin namu da ta baro a can sai cewa tayi yace a gaida mu ya samu sauki sosai da taje . Munyi ta murnan jin hakan dama da zata tafi munce zamu tace mu bari idan ta dawo sai mu shirya mu zo mu duba shi da jiki don haka muka kasa kunnuwan mu don muji tace ga ranan da zamu mu duba mahaifin mu din kafin ya koma. Tunda tace damu ya samu lafiya ko banza mun san idan mun samu ganin shi zamu samu kudin kashi a gurin shi wanan shine burin yan kannena a lokacin sai lissafin abinda zasu saye da kudin sukeyi. Kwatsam muka wayi gari da mumunan labari kuma Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa washe garin da dawowan umma daga wurin shi din . Ganin mutanen gidan mu nata kokekoke idan an ganmu sai a kama yan kamay kamay don kada mu gane nice na fara fahintar abinda ke wakana a gidan namu. Inda na tsura umma da taron mutane a dakin ta masu zuwa ta,aziya suna fadin ashe ba nisa tsakanin shi da matar shi don yanzu da rasuwanta shekara biyu ke nan tsakanin su. Duk da hankali bai gama shigana ba lokacin hakan bai hanani fahintar maganan da sukeyi ba ihun da na yanka daga inda nake ne ina fadin wayo baba, ya fargar dasu ina wurin tsaye . Kafin su taso zuwa inda nake na zube a somay kasa take sukayo kaina gaba dayan su sai fadin suke basu san da labarin rasuwan nasa bane dama ? Umma fadi take may zan gani haka kuma Allah ka dubeni da ido rahaman ka ya Allah tana fadi a cikin wani irin yanayi na tashin hankali ganin ana zuba min ruwa ban farfado ba yasa take wanan maganan hankali a tashe. Kururuwan da sukeyi ne ya dawo da hankalin mazan dake waje a cikin gidan hankali a tashe suka shigo don ganin abinda ke faruwa. Can kuma kanina wani ya tare shi yana fadin Allah sarki ashe kuma mahaifin ku shima ya rasu bayan mahaifiyar ku din. Da ya fara ihu daga van bai tsaya sauraren maganan shi ba yayo gida yana yanka ihu a cikin tashin hankali sai ya samu kuma ana fama danibin farfado daga suman da nayi. Daidai lokacin da ya shigone aka samu nayi dogon ajiyan zuciya sai fadi suke barka ta farfado yayo kaina yana kuka tare da fadin hadiza mun shiga uku ance baban mu ya rasu yau. Rungumay juna mukayi gaba dayan mu muna sake wani irin kuka na maraici a tsakanin mu da yan uwana duk tsawan da suke muna bama jin su a lokacin. Don haka dole aka kyale mu don abin kuka ya samay mu a lokacin ba mai iya hana mu yin kukan don suma kukan sukeyi a lokacin. Ranan dai muna a cikin tashin hankali da ba zan iya muku bayanin shi ba saboda halin da muke ciki ba wanda yai zancen cin abincin da ake kawo muna a ranan . Washegari ne baba kabiru ya iso da yan kayan da baban mu yayi jinya a wurin tare da yan kudaden da ya bari wanan ya kara tayar muna da hankali muka tabbatar da mahaifin namu ya rasu kuwa. Muna manne dashi yana kokarin ganin mun da sake sai magana yake bamu don mu dan sake jikin mu dasu. Sai dai ina nikan kamar kara tunzura ni ma sukeyi don ban iya ci ban iya sha a lokacin sai aikin kukan da nakeyi don tashin hankalin da nake ciki don na fi sauran fahintar halin da muka shiga a yanzu na rashin iyayyen mu din. Sai da baba kabiru ya nuna min bacin