← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 53 OF 89

Sashe 53

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read

Tun daga wanan ranan abubuwa suka kara jagulai muna don sai yayi min kamar basu haduwa da matar ashe sallon tako suka canza min don kada in gane suna tare da ita.
Da zaran ya fita da safe yana gurin ta sai in yamma tayi zai dawo yayi wanka ya kara fita baya wuce sha daya zai dawo gida ya kwanta sai kuma gobe indan ya fita kuma.
Cikin jikina yana ta kara girma a lokacin ga ba komai a hannun mu sai tunanen fitar da kai kunya da nake faman yi inda shima a bangaren shi haka din ne ke gudana wurin shi.
Bai aje ba baiba wani ajiya ba sai ranan naga bai fita ba kamar yadda ya saba fita yawon shi na banza din har na gama abinda nakeyi na samay shi muka zauna muna hira dashi.
Yake ce min wai yaya zancen filin mu na wani gari da mahaifin mu ya saya nace filin na nan baba yana kula muna dashi sai nan gaba za ai shawaran abinda za a yi da fili.
Yace to may zai hana a sayar da fili in samu abinda zanyi na haihuwa da kudin shi yana ganin shine mafita a gare mu tunda dai naga shi baida shi ai.
Nace wai wai nifa tsoro nake ji da kunya in tunkari baba da wanan zancen haka gaskiya a dai canza dabara zai fi nake gani.
Da yake sarkin iya tsari ne nan ya zauna ya tsara min yadda zamuyi yace ai sai na fara neman hadin kan yan uwana tukun mun daidaita zan tukari baba da zancen fili.
Haka dai na gaiyaci yan uwana kan suzo akwai maganan da zamuyi dasu a gidana ranan kaza da yake mukan hadu ba wanda ya sani mu dan tatauna dasu.
Da farko sunki ban hadin kai kamar yadda naso sai daga baya ne da na sa masu kuka jikin su yayi sanyi suka yarda a sayar da filin don na fada masu abinda nake son inyi da kudin filin.
Tunda wancan mai yawan baida ranan fitowa gare mu yanzu abinka ga dan uwa duk sai suka tausaya min suka fara fadin suma suna da abinda zasuyi idan kudin sun samu.
Nan muka aje ranan da zamu samu baba kabiru da zancen filin kowa ya koma inda ya fito sai ranan da zamuje wa baba kabiru da zancen kuma.
Jamil ya dawo yana tambaya na yadda mukayi dasu nace sun yarda nan ya hau yin dadin baki irin nasa har da fadin yadda kudin filin zai kai idan mun sayar din.
Ya shiga tsara abinda zai saye na suna da wanda ni zanyi tun lokacin da yaji yan uwana sun yarda don ni yanzu ina kallon shi ya daina harkan bariki gani kadai ya dogara a gidan.
Bukin yar uwanshi za ayi a kauye ya shiga min shiri wai yana son in fito wurin bukin dani da Amira yai muna dinki fita buki kala biyu duk da bamasu tsada bane niko sai rawan kai nake zan fasa taro da kayan idan naje.
Ina ruwan dan baka saba ba nake ganin ai ba wanda zai kaini fita a gutin yadda yake dada kayan a gabana da yadda zasuyi min kyau.
Mun samu baba da zancen fili baba yayi mamaki kwarai may zamuyi da kudi haka mukace muna dai son a sayar a bamu kudin mu ne lalura zamuyi.
Yace mu bari zai tuntubi yan uwan shi idan sun yanke shawara zamuji daga baya abinda suka yanke.
Kwana biyu na wuce wurin buki a kauye wanan karon ban dade kamar yadda yake turani in dade ba saboda zancen kudin da yasa ma rai din ya matsa akan in dawo.
Tun da na dawo ya sani gaba haka nikuma na sa yan uwana a gaba muka tayarwa baba hankali akan fili baba musa yace wa baba kabiru a sayar kawai tunda matsin yayi yawa yaran nan idan ba munyi da gaske ba suna da ja sosai damu nan gaba.
Haka dole aka sa fili kasuwa kan sayarwa shiko gogan kulun ya dawo tambaya yake yaya babu wani magana a bangaren babane har yanzu.
Idan nace a,a sai yace ya gane mutanen nan cutan mu suke son yi idan ba haka ba fili ne za a ce yayi wuyan sayarwa a gari kaza.
Shi idan basu samu mai saya ba shi zaije ya samo wanda zaisai fili a bamu kudin mu don ga lokaci yana karasowa na haihuwa na ni bani tunanen hakan shi idan na haihu baida yadda zaiyi gaskiya.
Nikuma jin hakan sai na kara hasa ma yan uwana wuta muka matsama baba kan zancen fili mudai a sayar ko nawa ne a bamu kudin mu shine burin mu.
Baba yace indon ta nasa ne a bari nan gaba fili zaifi kudi sosai don yanzu ba lokacin kudi bane ga mutane don damanane yanzu .
Mukace mu dai a sayar duk wanan abin mu uku ne masu hasasa wutan komai shi karamin mu baya cewa komai sai yadda mukayi dashi.
Da yake yana jin maganan mu shi dai bai cewa damu komai sai yace duk yadda muka yanke yayi mai don ko kudin farko da aka raba nasa Baffa ne ya kalalamay yaki bashi wai don kada ya halaka kudin.
Ko dubu daya yake so dole sai baffa ya sani zai cire ga account din shi don Atm da komai nasa yana hannun baffa don bamu yarda da iyayyen mu ba saboda zugan su Jamil dake aiki a kan mu lokacin.
Wani tsana da kiyayya ne ya fara shigowa tsakanin mu da yan uwan mu da farko muke daukan kan mu duk abu daya yanzu irin abinda suka ga muna nuna ma mahaisu sai tsana da rashin yarda ya fara shiga tsakanin mu dasu.
Babu magana mai dadi haka ma su anty duk sun tsamay hannun su ga zancen mu yanzu a hankade suke kallon mu idan munje gidan.
Haka yasa muma mukai shawaran daina zuwa gidan wurin su sai an dauki lokaci mai tsawo bamu taka gidaba da sunan zuwa gaida baba.
Don shi baba kabir mutum ne mai wuyan sha,ani baka gane bacin ranshi a lokaci daya don bai nuna muna komai dake faruwa a tsakanin mu dashi sai dai su iyalin nasa.
Anty ma tun abinda mukayi wa iyayyen mu maza muka rasa gane kanta ta daina muna komai sosai da take muna a baya yanzu ta rungumi diyan ta kawai.
Duk da tana dan iya kokari wurin nuna muna ba komai amma mun ja baya ga al,amarin ta sosai yanzu haka dai ake zaman kadaran kadaham damu dasu.
Ranan dai na samu baba da kuka ina fada mai ina cikin matukar bukatan kudi ne don haka don Allah a sayar da filin nan ko nawa ya samu.
Ba a fi sati ba aka sayar da filin namu ina kwance gida baba ya aiko inzo yana neman mu Jamil yana jin haka yai zubur ya fito daga daki yana fadawa dan aiken yaje yace gani nan zuwa.
Bayan fitan dan aiken yake fadin in tafi zai karasa min aiki na kafin in dawo don haka na shirya a gurguje na nufi gidan namu wurin kiran da baba kabiru ke muna.
Ban dade da isa ba yan uwana suka hallara a gurin nan dai baba yai muna jawabin yadda filin ya kama inda za, a fitar da gadon mahaifiyar su sai a raba muna sauran.
Idan akwai mu abinda muke ma bakin ciki shine ace za a raba gado a warewa mahaifiyar mahaifan mu gado tunda yanzun bata darai ai.
Gani muke kuma da yadda Jamil ya lurar damu ai zalunci ne da ha,inci ake muna a hakan da komai za a ce wai a cire kason mahaifiyar su duk da bata raye wai a raba da ita don dai kawai su samu kason wani abu daga ciki.
Yau ma kaman kullun bayan sun gama muna jawabi sai kanina baffa yace shi yana da magana wai duk da hajiya umma bata raye, may kesa ake cire mata nata kason ko yaushe idan anzo rabo.
Kai baba kabiru ya girgiza yana murmushi yace yanzu kai baffa waye bare a cikin uban nan, nan naka , sai baba musa ya dakatar dashi da fadin ba wanan ba don na gane dan kason mahaifiyar mu da muke ci daga cikin arzikin su suke wa bakin ciki don yau kun fito fili kun baiyana muna manufa ku akan abinda kuke nufi.
Baba kabiru ranshi ya baci sosai damu bai iya magana a gurin ba saboda bacin rai sai na koma tun a wurin ina jin nauyi da kunyan kanmu sosai na abinda mukaiwa baba kabiru da yan uwanshi sai dai murna da dokin samun kudi a lokacin bai bari mun rokeshi gafara ba.
Kamar yadda muka saba idan mun saba mashi muke bashi hakkuri ya huce damu sai yau bamu samu yin haka gare shi ba don doukin samu kudi da mukeyi.
Chapter 53 · 0% Book details