← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 21 OF 89

Sashe 21

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Wanan time din haka na kare shi babu dadin rayuwa a tare dani don sam hankali baya ga karatu don tunanen mahaifiya na da yai min yawa a raina. Na dawo gida na samu har lokacin umma tana gidan zaune da kanne na kamar kada in dawo sai umma ta tayar da hankalinta akan tana son zuwa gida ta duba su can. Wanan abin ya daga hankalin mahaifin mu sosai da ya rasa yadda zaiyi damu gashi hutu akeyi sai ya shirya har damu zata tafi muyi hutu a can. Da yake dogon zango ne muka fara murna zamu gida muga yan uwan mu sai dai ina gani kamar idan munje zanga mama acan a raina. Mun zama yan matasa yanzu don haka muka fito fes damu a gurin baba kabiru muka fara yadda zango da muka iso zamu dan kwana biyu a gurin shi kafin mu karasa gida. Matan shi suka shiga ina aka saka damu suna yi muna kokari mun fi sakewa da matar shi ta biyu a gurin ta muka sauka inda umma ta sauka gurin uwargidan shi. Bamu da wani damuwa dan zaman sati dayan da mukayi da iyalin shi sai dawainiya yake damu yana nuna diyan dan uwan shi ne mu tankar diyan cikin shi muma muke a gurin shi. Muka kare sati dayan mu muka wuce kauyen mu, yan uwa na ganin mu sai sharan hawaye sukeyi don tunawa da mahaifiyar mu da sukayi. Muma dai kukan muka dauka tundai ni dake da wayau a cikin mu nafi kowa shiga tashin hankali sai da kyat da fada da komai umma ta samu na dakatar da kukan da nake yi. Washe gari da rana muka shirya zuwa gidan kakannin mu na fanin mahaifiyar mu kai mata ziyara don muna jin dadin kasancewa da ita fiye da umma da take mahaifiyar mahaifinmu. A can ma mun taba kukan saidai da ta rarashe mu mukai hakkuri duk firan mu na ranan kan ciwon mama ne da yadda muke maraicin ta. Sai dare muka koma gida bayan tayi muna abinci mun ci mun dawo umma ta cika fam kan dadewan namu da mukayi a gidan kakan mu mahaifiyar maman mu din. Ba wanda ya tanka ta muka shige dakin mahaifiyar mu inda anan muka sauka tunda muka iso don dakin umma ba fili kaya sunyi yawa. Ina kokarin cire kayan jikina ne hafsa ta shigo tana rada min Jamil yana waje yana son ganina nace hafsa kin san ba abinda zai yuyu bane don yanzu umma ta gama muna fada munyi dare a gidan Auta don haka ake kiran kakan namu dashi. Kije kice yayi hakkuri tunda muna nan watarana zamu hadu ai wanan ranan bamu hadu ba dashi haka ya juya ya tafi . Ba tare da ya ganni ba sai dai banji dadin hakan ba don mun dade bamu hadu ba dashi ba zance ga ranan da muka hadu dashi last ba. Gama shiri nayi na samu wuri na kwanta har na fara barci nake jin umma tana kwala min kira daga kofan dakin ta na amsa a sanyaye tare da mikewa zuwa wurin ta ina fadin umma gani. Bazaku ci abinci bane har wanan lokacin baku dauka ba nace umma a koshe muke don mun ci abinci a gidan Auta kafin mu dawo gida. Salati ta saka tare da fadin yaran nan kun iya sai da hali yanzun zuwa kukayi kuka nuna mata muna barin ku da yunwa ko may ? Da sauri na dago ina girgiza kai tare da fadin ba hakana bane umma ba wanda ya nuna hakan a cikin mu wallahi rufa min baki munafukan banza kawai. Gobe in Allah ya kaimu zanje gidan inji abinda yasa ta girka maku abinci a gidan ta kallon mamaki nayiwa umma din kamar ta manta da Auta ma kakan mu ne kamar yadda take kakan mu itama. Nidai naja kafana na barta nan tana surfa muna zagi dani da kanne na akan zuwa gidan kakan mu ta uwa da mukayi muka kai dare. Washegari tun fitowan mu dakin na gaida umma ban kara fitowa ba ina dakin mama ina aikin tunane rayuwan mun yadda muka koma abin tausayi duk da dai bamu da tausayi don mahaifin mu yana tsaye a kan mu. Dama yan uwan shi kowa na nuna kulawan shi akan mu a matsayin su na yan uwan mahaifin mu din a gare mu. Saidai mu bamu ganin hakan da suke muna dan abu kadan zamu dauka don mahaifiyar mu bata da raine ake muna wani abin da bai dace ba. Yinin ranan haka nayi shi a dakin ba wani walwala a tare dani sai ma gyaran dakin da na tsiri yi tankar mahaifiyar mu tana nan a cikin sa ne kamar yadda naga tana yi idan munzo tare da ita garin. Sai yama lis na watsa ruwa a jikina kofan umma na dawo na zauna muna hira da yan uwana a gurin ta fito daga daki tana fadin kin ga dama kin fito ke nan don maganan da nayi maki jiya kike fan fushi haka yau. Nace ba haka na bane aikin dakin mu nayi don yayi kura da yawa sosai ta tace ke dai kika sani idan kin sa kanki a damuwa haka ma yan uwan ki ba zasu sake ba don basu ga kina walwala ba . Shiru nayi ina fadin a raina walwala ai ya kare a gurin mu umma tunda mun rasa mahaufiyar mu ko a duniya. Maganan ta ne ya dawo dani ga tunanen da nakeyi tana fadin idan ba zamu iyacin abincin da akayi ba a gidan mu dafa taliya muci da dare. Don mahaifin mu bai barmu munzo hakana ba garin sai da ya sawo muna duk wani cimar daya san muna amfani dashi a can muka zo dashi gida. Tambayan kanne na nayi idan zasu ci da sauri suka amsa min haka yasa na tashi don in dafa muna taliyan tunda suna son ci na sani dolene kawai yasa suke cin abincin gari. Mungama muka taru a gurin umma din nan mukaci taliyan sai dai itako kallo bai ishe ta ba tuwon ta da aka kawo muna taci. Bamu wani dade ba muka kwanta don dare yayi a lokacin sai dai ni ba barci ne nayi ba na dai kwanta ne ina tunanen duniya a lokacin. Tunda muka zo ko hanya bai hadani da jamilu ba har yakai satin mu daya da zuwa garin duk ko shima yana cikin garin a lokacin. Yau ya kama kasuwan kauyen mu ne kowa sai hada hadan sana,ar shi yakeyi don fita dashi gurin yan kasuwa in ka debe mu da bamu komai sai dai mu wanke mu saka don yanayin mu daya dan banbanta dana yan gari. Sai dai duk da haka ba,a barmu a baya ba don muma munyi kwalliya mun saka kaya masu kyau don muna da muradin shiga kasuwan mu dan zagaya. Saboda akwai kudi a hannun mu bayan wanda baba ya ba umma don lalurar mu na yau da kullun da wani matsala daka taso a gare mu a gidan. Kamar yadda tsoho keda naci a kudi haka ma yaro yake da kunata akan kudi don su sauran basu san baba ya bamu kudin ba a hannu na. Mun gama shiri muka sallami umma don abokai na da suka shigo don mu fita sai dai ni abinda ke ban mamaki shi su hafsa kawana ba karatun sukeyi ba kuma su ba aure sukayi ba har yanzu. Mun fita mun dan zaga abin marmari na sayo muna da kannen na don mun dade bamu ci ba a can mun juyo zamu dawo gidane muka hade da su jamil da kungiyar su. Ashe sun saka ido a kan mu suga fitowan mu take dan leken asirin su ya sheda masu mun fito garin muna zagawa a kasuwan sai gasu sun sha kwaliyan su zakace ba yan kauye bane su. Kallon juna mukayi na sada kaina kasa don kunya su a dole ga samarin da suka ga yan mata suka zo da guntun turancin su don su burge mu saboda mun fito birni musan sun iya turanci. Da sumaiya kawanta suke turancin sai kanne na maza da muke tare suke buga turanci dasu suna jin dadin yadda yaran ke amsa su. Na dago yana fadin baby ya kike ne kwana biyu bamu hadu ba ya mukaji da hakkurin rashin mama kuma sai lokacin naji wani iri a raina. Don haka nake da an min maganan mama hankalina sai ya tashi sosai mutuwan ya dawo min sabo a raina. Mun dan dade a gurin tsaye dasu suka rokeni da dare in basu lokaci su samay ni a gida mu kara gaisawa don nan ido yayi muna yawa akan mu. Na matsu in bar gurin haka yasa mukai sallama dasu muka wuce zuwa gida inda kannena maza suka bisu kamar yadda suka bukata suyi. Yalon da muka sayo kasuwa ne nake wankewa a bakin kwatan shiyan umma kanne na suka shigo da leda shake da abin motsa baki suna fadin cikin murna Jamil ne ya saya masu. Ina kokarin fadin su rage murya kada umma ta jiyo su sai ko gata tafito but daga dakin tana fada cikin hasala wani jamilun din badai na gidan babbaku ba danayi mashi iyaka daku ? Wanan yaron kamar jikan mayu da bakin naci haka na fada mai na mashi iyaka daku a garin nan Baffa kanina yace umma mu hadiza ne da za a hanamu fita gurin shi. Dakuwa tayi mai da hannu tana zagin shi tace dama zubin arnan da gare ka dan nema mara kunya ya juya zuwa dakin mu yana bata rai da zagin da tayi mashi din. Ko kafin in zo dakin na samu ya fitar da kayan yana ci fada na fara mai don may suka karbo mai kayan shi yanzu gashi sun sa umma fada damu haka. Yace idan ke baki ci ki barmu muci ai ba rokon shi mukayi ba ko tun ina jin haushi har na dauki gwangwanin maltina daya na bude ina kurbawa. Daidai lokacin umma ta dago labulen dakin tana fadin watau ma bakuji maganata ba ko in kuce kwadai ne ai wurin shi zaku mutu. An fada maku kauye ana haka
Chapter 21 · 0% Book details