← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 56 OF 89

Sashe 56

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Ko dana koma gida na samu ya karasa min aikina kamar yadda yace zai mun din don har Amira na samu ya kimtsa min ita don bai bari na tafi da ita ba. Ina shigo jikin shi har rawa yake wurin tambayana to yaya zancen kudin ne komay ake neman mu dashi kudin dake a jikina na fitar ina nuna mai take ya washe baki yana fadin alhamdullahi. Allah ya rufa muna asiri dama ko barcin kirki ban samun yi kan rashin samun mafita da banyi ba yanzu kin ga Allah ya rufa muna asiri. Nan ya shiga lissafin irin karyan da zamuyi idan na haihu yake fadin in kawo kudin tun yanzu yakai na mai shagon da yake sayayya da na haihu daukowa kawai zamuyi a gurin shi. Ina kallo ya lissafa kudin da yake so ya kuma fitar da wanda zamu sai abinci har na suna idan na haihu din da za,a dafa gurin taron suna. Da kyat da boni na samu yabar min wanda zan dan rika a hannu na don lalurori irin na mata sai cewa yayi dani ba ga baba kabiru nan ba yasa zai min idan na haihu. Ni don sanin yadda muke da mutanen gidan mu yanzu sama sama yasa hankali bai kwanta da zasu yi min ba idan na haihu din ganin na na matsa mai ya firar da dubu talatin ya bani a cikin dubu dari tara da kyat ya mika min a hannu na wai sakaci gare ni kada in aje a wurina a kwashe. Nasan abin da yakewa shine ganin haihuwana na farko an min abinda ma bai zata zasuyi min ba ga kuma kanwa ta data haihu itama an mata sha tara na arziki ya gani. Ban san baida kunya ba sai da ya miko min kudin yana wani shan toka a fuskan shi tare da fadin ni ke nan naga kudi na daure fuska may zanyi dasu bayan baba kabiru yana muna komai idan mun haihu mafarin in koyi kashin kudi ke nan jifa. Baba kabiru da ya gama zagi yana batawa a gurin mu ne yake kuma tunanen zai muna abin arziki yanzu saboda son banza daya iya a rayuwan shi. Ni gani wawiya ta karshe ban koyi tunanen irin sakin da yake min ba a lokacin ni dai bukatana da tunane na dani kadai zai zauna ba wata mace da zaice zai kara aure nan gaba. Don sam bani irin wanan tunane a raina saboda son shi daya rufe min idanuwana a lokacin har mutane na fadin wai ko asiri yai min ne haka wana abin ga kowa don sanin halina an kawo ido ansa min dashi banda makwabi a rayuwa na. Don kowa yasan da ya fada min gaskiya zan kwashe in fada mai ya dora gaba da mutum har illa masha Allah. Yanzun kan muna da abinci ga kudi don shi Jamil mutum ne da bai ci ko wani irin nau,in abincin daya danganci tuwo a rayuwan shi sai dai dan taliya makaroni shimkafa da miya ko tea kamar ba haihuwa kauye ba shi. Sai daga kai nake wa mutanen gidan mu don komai ina dashi yanzu ban dan murya gun kowa don neman wani abu don tunda anty tai min fadan haka ga yan hayan gidana na daina tambayan su wani abu. Da yake ni sakarai ce sai wanan samun yasa ina daga masu kai har suka fahinci hakan gare ni kowa ya jaye min daga harkana sai ni dashi da yan uwan shi muke bushashan mu a gidan. Daka ji sallama yan uwanshi ne ba dai nawa ba yanzu zan hada masu delicious ko a sawo masu kayan sanyi susha su wuni suna cin dadi a gurin mu. Sati kaman uku da haka na haihu na kara haihuwar diya mace ba laifi don yan uwa da matan baba suna asibiti a tare damu har na haihu aka dawo dani gida. Tun yanda suka ga ni kaina da Jamil din muna masu kowa ya dauke kafan shi a gidan tun ranan matar mahaifin shi ce tazo ta zauna damu na satin da akeyi inda Jamil sai dadi yake cika mu dashi. Niko ban tunanen komai a raina don sai fadin ake yarinya tazo da goshin ta don muna cikin wadata inji yan uwan shi suke fadin haka gare mu. Ban wani damuwa ba na rashi ganin dangina basu tsayawa a gurina ni tunda ga dangi jamil sun tsaya min akan komai ai ya waddatar dani nake gani don haka ne ban nemi shawaran kowa ba. Da anty ta kara shigowa duba mu take kebewa dani irin yadda akeyi din nan tana tambayana mai muka shirya ma bukin don sunji shiru ban tuntube su ba har yanzu. Sai budan baki nayi nace kada su damu ai mun gama shirin komai da zamuyi tace kai madalla Allah ya raya muna bata dade ba ta fita . Sam ban kawo magana na wani katobara bane a lokacin don haka na shiga harkokina ba wani damuwa don ina ganin ai muna dashi. Summaiy kanwata ce tazo tana tambayana nake fada mata yadda mukayi da anty tace kai amma ke anty hadiza wai wata irin wawiyace haka don Allah. Anty ce zaki fadawa kun kun gama shirin komai da mijin ki kina ganin ke yanzu baki da bukatan komai a wuri su ke nan ? Nace may zamu bukata tunda muna da kudi a hannun mu yanzu tace to shike nan ita yanzu gida zata taji irin shirin da akeyi a gida don tasan yau ya kamata ace anyi su cicin da sauran su. Nace sai ta dawo ta fita zuwa gidan mu niko ban wani damuwa ba a raina don nasan zamu burge kowa da wanan haihuwa ko suyi ko kada suyi ban damu ba ni. Da ta shiga gida sai ganin gidan tayi wayau ba kowa anty ma tana dakin ta tana barcin ta a lokacin don tana up a wurin aiki. Bayan sun gaisa ne take tambayan ta ko akwai wani abinda za a yi a gidan sai take cewa ai mai haihuwa tace ta hutar damu don sun gama shirin komai. Tace a ina ta shirya anty har gashi gobe suna ni banga wani shiri da takeyi ba tace summaiya kin san shirin da sukayi ita da mijin ta ne ki sa masu ido aga ni mana. Abinka da dan uwa sai hankalin ta bai kwanta ba ta kara dawowa gidana tana fadin ita fa taje gidan mu bata ga wani shiri da akeyi ba a can yanzu idan mutane sun taru mai zan raba masu na buki ? Nan dai dabara ya fado min nace buta zan sayo sai alale da taliya da zan dafa kuma da dambu . Tace duk a ina za ai maki wanan aikin to nace a gidan yaya sani wanan Jamil din nan da suke kamar abokai wanda ya tilasta min kiran matan shi da anty. Wani tsoki taja tana fadin yanzu ke a can za ai maki aiki sai kace wace bata da gata a gari gaskiya bai kamata mu nuna wa baba kabiru da matan shi haka ba anty. Fada mukayi da ita sosai a gurin don ta fahinci ina haka ne don gyarawa Jamil dina rai kawai ban damu da abinda dangi zasu fada ba a kaina. Nan na fitar da kudi cikin wanda ya dan rage min na bashi ya sawo min buta sai gashi da kananin butoci kuma dozen uku ni da na bashi kudin dozen biyar yana fadin. Wai ya samu sun tashi shine ya sawo min wa yan nan nace ai ba zasu isheni ba yake fadin wai har wasu mutane zasu zo da zan saye da yawa don barnan kudi kawai. Dinki kala uku yai min duk a cikin kudina shiko ya dinka sun kai kala goma sha kamar shine mai haihuwan da zai fita bani ba. Washe gari a gidan su aka yanka katon ragon da ya sayo aka gyara sai dan hanjin da aka aiko min dashi wai sun raba a can suma zasuyi amdani dashi ne. Sannu sannu gida ya fara cika da mutanen arziki yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa min suna gashi ba a kawo min abinda zan ba su ba. Yan uwana da suka zo tayani aikin suna daga gidan mu sai tambayana sukeyi mai zasu yi nake cewa ba wani aiki a can gidan su Jamil ake abinci. Koda za a kawo min sai ga taliya wani iri dashi ba mai kuma dan kadan kasan kula sai dana dafe kaina don takaici da bakin ciki ga alale shima kamar hakan aka kawo min din. Haka na aka raba ma wa yanda ke gidan a lokacin aka barni ina kamay kamay idan mutane sunzo mi don ba abinda zan basu anan. Yan uwana suka kwasa suka wuce gidan mu don a can suna nasu dahuwan don dangin mu da suka zo daga wurare anan suka sauka. Dama kuma a ka,ida hakan yake ga al,adan bahaushe yan uwan mai haihuwa zasu taru ne a gidan mahaifanta har zuwa wani lokaci kafin su zo gidan ta da dan abinda suka tanada don ta. Sai da sukaci suka sha a can suka dauko dan turamay dana samu wanan karon turmi hudu ne kawai daga gidan mu sai buhu biyu na abinci gero da masara da baba kabiru ya saka min. Aka nufo gidana dashi tun da naga haka naji raina ya baci dasu a zuciyata fadi nake aiko in haka ne zasu sha kunya don ni dama a shirye nake abina don haka. Nan gidan su Jamil suka shigo da akwatinan daya gabatar masu a ranan don ba wanda yai tsammanin haka daga gare mu. Sai wani washe baki nakeyi ina sallo ni adole mun faso gari muma sai fadi mutane ke yi basu taba ganin itin set din akwatinan ba a gurin. Da aka bude kuma sai da kowa ya kama baki don kyawon kayan dake cikin akwatinan danawa dana baby duk abin kallo ne a gurin. Aka kwasa zuwa gidan mahaifana kamar yadda akeyi a wuri mu sukai ta sa albarka suna fafin yarinya tazo da goshin ta inda yarinya taci sunan mahaifiyar
Chapter 56 · 0% Book details