← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 30 OF 89

Sashe 30

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Tunda na gama karatuna ina gida zaune sai dai ina gamawa summaiya tace ba zata koma boarding ba ita ma sai dai tayi jeka ka dawo a gida. Son da baba kabiru ke muna ne yasa bai mata fadan haka ba ya nema mata makarantar jeka ka dawo ta fara zuwa anan cikin garin. Gashi mun dinke sosai da jamil don yanzu shima a cikin gari yake zama gidan wani abokin aikin mahaifin shi don ya samu saukin kebewan mu a ko wani lokaci ya bukata. Da damana yayi zai koma gida ne muka kitsa akan nima in koma kauye na kwana biyu na yarda da hakan bayan tafiyan shi nima na tsiri son zuwa gida wurin umma kamar yadda nace a gida. Baba bai hanani ba don saukin kai irin nasa nan na shirya nayiwa kauye diran ba zata da farkon zuwa na naji rashin dadin garin don da yan uwana muka saba zuwa wanan karon kuma ni kadaice nazo. Sai daga baya na dan fara sake jikina a lokacin duk wata sa,a ta acikin dangin mu tayi aure nima don karatun da nake ne ba ai min ba na sani. Sannu a hankali na fara sajewa da su nan na yanke shawara na fara sana,a don kudin kashin da ke kokarin yi min tsaye a garin . Da taimakon yar mahaifiyar mu na samu jarin dana fara sana,a dashi a garin inda naje birni na saro kuloli da sauran kaya na bukatan mata. Sai dana kwana biyu a gurin yan uwana sai dai ban yarda na zo da kayan gidan baba kabiru an gani ba don kada yayi min fada kan hakan na gama masu kwana biyu tare da gama sayen duk wani abinda nake bukata na juya zuwa gida. Sai dai da farko naji kunyan yin talla don bantaba ba a rayuwana sai gani dauke da kaya buuuu a kaina ina shiga gidajen kauyokan mu dama ke waye ina tallatawa. Allah a cikin ikon sa yasa ma sana,an tawa albarka sai gashi dan lokaci kadan nayi suna sosai don bayan kuloli har turamay nake sayarwa kuma. Cikin dan lokaci kan kani nayi arziki da bai faduwa da wanan sana,an da nakeyi inda baba kabiru ya samu labari ya zo takanas ta kano har kauyen ya gana da umma akan barina da sukayi ina wanan ssna,an kamar mara gata a gari. Sai umma tace ni naga zan iya banda rashin gata abinda na zabawa kaina ke nan bai min magana ba ya koma da bacin rai don mahaifiyar su, ta hanashi yi min fada. Kudi na hada yakai dubu dari biyu jamil yazo gurina muna hira nake bashi labari yake fadin sai in samu wani sana an in dora a kai da riban nawa. Ya dan jima gurina muna hira daya koma gida ya kasa zaune ya kasa kwance yana tunanen wanan kudin dana bashi labarin na mallaka a yanzu. Washe gari bayan la,asar na dawo daga talla sai gashi nayi mamakin zuwan shi don ba lokacin zuwan shi bane kenan. Bayan mun gaisa ne yake fadin dama wani shawarane yazo min dashi shine dalilin ganin shi da nayi a wanan lokacin. Nace wani shawara ke nan yace eh gani yayi yanzu dai shi baida wani sana,an da yake yi mai zai hana shima ya fara sana,a da zaiyi saurin kawo muna kudi don mu samu mu fara shirin auren mu nan da dan lokaci kadan. Don ni gashi sana,an ya karbeni da farawa na tara wanan uban kudin idan mun hada hannu sai abin yayi auki mu kashe mu birne ba wanda yasan tsakanin mu. Nace ba tare da nayi wani tunane ba kana ganin haka zai fi muna yace kwarai kuwa don karuwan mune gaba daya. Nace yanzu kai may kake ganin zakayi wanda zamu samu karuwa haka da sauri ya gyara tsayuwa da kyau yace dani shawaran dana yanke shine in dinga shiga birni ina sayo mai na fetur da gas ina shigowa dashi nan kinga babu mai wanan sana,an ai anan ko ga kuma masaya na dayawa . Nace wanan shawaran yayi daidai gaskiya kaga a dan lokaci kankani zamu samu mu hada abinda muke so ke na yace shi ya gani shima. Batare da jin wani darrr ba nace ya je da dare idan yazo zan fito mai da kudin don yanzu idon mutane yayi yawa a kan mu. Ya gama min dadin bakin shi daya iya ya na shiga gida don jamil a gurin iya dadin baki baida tsara a kauyen mu nan da jin dadi na na shiga gida. Sai ga umma na gyaran gurin da take kiyon awakanta ta dago tana fadin yanzu muka gama maganan ki da babakin yushau nake fada mai riban da kika samu da sana,an ki . Shine ya kawo shawaran mai zai hana a sayo maki shanu a turke maki har lokacin da dabbobi zasuyi tsada a sayar nace ya bari ki shigo muyi shawara dake. Fuska na bata tare da fadin kash umma baki fada min wanan maganan da wuri ba yanzu fitan nan da nayi har na bada sakon a saro min kaya don ni ba zan samu zuwa ba wanan satin da kaina. Kuma gashi har mai sakon ya wuce ko fuska ta sauya tare da fadin Allah yasa haka shine alheri nace amin nayi saurin wuce guri don naga kamar bata yarda da magana ba a lokacin. Don idan zan sari kaya da kaina nake zuwa in sari duk abinda nake so in dawo don ko gidan baba kabiru sai inyi shiga goma ban leka su ba duk ko da cewa tan uwana suna gidan. Sai idan naga dama nakan dan leka su a gurguje in fito duk zuwa da zanyi sai anty tayi min korafin yadda na mayar da kaina wata gaja saboda da neman duniya ina karamar yarinya dani haka. Takan ce arziki na Allah ne ko nayi ko banyi ba idan lokacin arzikina yazo Allah zai bani ne gama mu da kudin mahaifin mu ake saka ran fitowan shi a ko wani lokaci zamu iya samun abin mu. Wanan fadan da takan min nakan ji zafin shi don ina fanin tana min hassada ga samun da taga inayi ne a yanzu ga zugin Jamil dake shiga kaina kan in raba yan uwana da can din ma gurin su anty din. Ga maganganun da wasu dangin mu yan hana ruwa gudu da sukan min kan dukiyan mahaifin mu wai su baba kabiru sun karbe sun cinye su da iyalin su. Maganan yanzu da nasan kudi sosai ya zauna min a raina sai nake ganin haka din ne don su ko yaushe yanzu a cikin wadatata suke don basu rashi sam. Dare yayi jamil yazo na fito da kudin zuwa gurin shi muna gaisawa yake fadin to yaya ina can ina Allah Allah kar gimbiyar tawa ta canza shawara don nasan idan umma ta sani zancen ta baci. Nayi murmushi tare da fadin ina zan bari umma ta san wanan zancen kaiko sai dai ina shiga dazun ta tare ni da zancen wai in kawo kudin a sawo min saniya da kudin. Da sauri yace sa may injin baki bata ba dai nace gasu tare dani yanzun haka ban yarda na bata ba don karya nayi mata kan cewa nabada sakon su a saro min kaya ai. Yayi wani irin shu,umin dariya tare da fadin da kyau ta wurina ita umma may tasani kan kudi yanzu su burin su ke nan idan mutum ya dan samu kudi ace wai yasai abin kiwo dashi. Nace ai ni ba zan yarda da wanan shawaran nata ba ga kudi ina ganin inda zamu samu karuwa wani zancen kiwo ake yanzu kuma da za a zo a girke a gida karshen tama ba wani riba a ciki. Na kawo kudin dana kulle a cikin bakin leda na mika mai yana rawan jiki ya karba tare da fadin gobe asubanci zanyi don in samu in dawo da wuri kin ga har rumfa na kafa dazun bayan rabuwan mu dake inda zan fara sana,an tawa. Bai dade ba yace zai tafi don ya samu barci issashe don asubancin da zaiyi a gobe din mukayi sallama dashi ya tafi na koma ciki cike da murnan wanan shawaran da jamil din ya kawo muna. Don ina ganin zai ma fini samun riba a yadda ake cinikin man fetur da gas a kauyu kan mu don masu noman rani dake amfani da injin da sauran abubuwan bukata don rashin wutan lantarki da muke dashi a garin. Washe gari sabo da murna ban fita talla ba barci na nayi sosai a gida sai zuwa sha daya da umma ta jini shiru ne ta leko dakin mu tana fadin. Yar kabiru yau nace ba fita tallan kayan ne ko hutu kikeyi ne haka na bude idona da kyar tare da fadin umma yau hutu nake yi don ba wasu kaya da yawa a tare dani sosai. Takai dubanta gurin da nake aje kayan tana fadin lalaikan kaya sun fada sosai wallahi kila zuwa gobe sakon ki ya iso ai kinga sai ki fita da tushe. Sai zuwa a zahar na fito na debi ruwa na watsa ma jikina na nemi abinda zanci don tun safe ban ci wani abin kirki a cikina ba don dauki da nakeyi jira kawai nakeyi inji ance ga jamil can ya bude rumfar shi ai. Sai dai har yamma banji komai ba yasa na dan fito na fita nabi ta wurin har lijacin ba jamil babu labarin shi a garin sai zuwa gab da magariba ne nake jin labari wai an tare jamil a hanya ko may ko may ban karasa jin maganan ba don faduwan da gabana yayi a lokacin. Fita nayi a gagauce don in tabbatar da zancen da nake ji nan nake ganin mutane gungu gungu kin san abu ga kauye basu iya samun magana ba. Yana kuka shabe shabe wai an tare shi a hanyan shi na zuwa birni sayan mai an kwace kudin an mashi dukan tsiya ko mashin din don sunga tsofo ne suka barshi dashi don ko sun dauka basu dauki komai ba don wahalanta. Jikina yayi sanyi nadai gode ma Allah da suka barmin shi da rai suka
Chapter 30 · 0% Book details