Sashe 60
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read
a raina tunda yace mahaifin shine ya aike shi saya na dauka bai da shine yasa bai sayo muna ba. Ban tsinke ba sai da sallah ya kwaso min gwanjon kaya da ta zauna ta gyara masu dinki dagani har yara ta bashi ya kawo muna wai kayan sallah mu ke nan. Da farko har ina munna na shirya zuwa gaida mutanen gidan mu anty na kallo na naga bacin rai karara a fuskan ta sai wata kanwata take ce min. Ke ko anty harda sallah baku gyara kowa na zuwa acan acan dashi ke sai ki zo muna haka ba dadin gani dake har yar ki don tunda yan kayan yarinyar da anty ta saya muna masu tsada na haihuwa sukayi mata kadan yanzu na koma mata yan kamay kamay. Don ban iya saya mata don banda shi gaba ban dashi baya sai dan abin da ya kawo muna muyi amfani dashi. Raina bace nace wa kanwar tawa wanan da na saka kika raina shine ya saya muna shi na sallahn mu ke nan daya sawo muna. Wanan ai mama ta mutu ne gwanjon lace din lagos aka gyara wani irin bacin rai naji da suke maganan nan dai na rufe ido naci masu mutunci yinin da banyi ba ke nan na fito na koma gida na cike da bacin rai. Tun da na tun karo gaban unguwar mu naga mutane suna kallo na haka na dage kai na wuce ban tsaya gaida kowa ba. Wai ashe sun shige ke nan dashi da ita na biyo gurin shine idon da mutane suka saka muna don gudun kada tsotsayi ya hada mu dasu a hanyan. Ba wanda ya iya fada min hakan sai wata tobashiyan shi data zo muna yawon sallah take tsokana na da fadin yanzu shi kuma mijin ki har lalacewan shi ya kai shi ga bin arna arniyar ma wace ta haifeshi. Har ya fito kerare yabi hanya da ita da uban ranan nan kowa yana kallon su bai ko jin kunyan idon mutane da nauyin su. Wani iri naji a raina yake na kama mata har dai na samu ta wuce bata gaji da zubawa ba raina yanaz bace. Fitan ta na shirya sai gidan da mahaifin shi yake naje da kuka na nakai masu maganan da nake ji a unguwa yana cewa karya da kazafi ake mashi. Sai da mahaifin nasa ya gama saurare na yace min ke kin tabbatar da hakan ko kin gane su da idanuwan ki haka dai yayi min magana ta baibai ta yadda ban gane komai da nake fadan akai. Abinda ban sani ba ashe tsohon yasan da wanan zancen har kayan sallah ta dinka mai da kayan azumi shine rashin kama min da bai yi din ba dana zo da zancen. Sai daga baya duk nake jiyo hakan a wurin mutane sai dai nasa a raina cewa tunda yace naga hakan da idanuna na hake sai na kama su din da idona. In da na na bar zancen a raina ba tare da na shedawa kowa zancen ba na koma normal life dina shima ya dauka na bar wanan zancen ne yaci gaba da harkokin shi kamar yadda yakeyi a baya. Har akai shagalin sallah aka gama ban kara fita ko ina da sunan zuwa unguwa ba ina gidana kumshe sai wanda ya tuna dani yazo gurina dubani a cikin yan uwa. Matsalan dake damun yan uwa na dani shine yarda da wanan zuwaira din danayi hundred pacent a raina don duk shawarana yana gurin ta duk da na girmay ta nisa ba kusa ba kuwa. Don ko sa,an kanwa ta summaiya batayi ba ga haihuwa amma haka muke mu,amula da ita duk shawarana yana gurinta wanda ni ban ganin laifin hakan da mukeyi da ita. Wanda hakan shi Jamil din ya kidanya min yana so dani adole in kirata da anty kuma mu kama mu,amula da juna kamar yan uwa. Ashe ban sani ba kuma yadda muke haka ya dauki wanan farkan tashi yakai gurin su suna mu,amula da ita tana masu abin arziki wanda ni nawa sun gama dashi ko an taru an cinye duka an barni da tunane. A cikin haka baba kabiru ya samo min aiki sure p da aka bude maimakon in bada nomber wayana sai Jamil yace in bada nasa don ni a lokacin banda waya a hannu na dole idan kudin sunzo zasu fada a wurin shi iyakata account dana bude da kaina kawai amma dole sai yaga alert ga wayan shi. Fitowan farko aka bamu na wata uku a jere tunda ya like min sai da aka ga bayan kudin dan abinda zance na tsira dashi shine kawai kudin da ya sai muna abinci dashi na gida naci wanan ne kawai ba zan ratse ban ci ba daga cikin kudin. Yanzu abin da dama sosai a tsakanin mu tunda ina samun yan kudade suna shigo min ta hannu na sai dai duk da hakan sunane don zaice nasa albashi yayi wani lalura dashi nawa zamuyi dan amfanin gida dashi saboda rashin tausayi. Don yasan da zaran ya bata rai hankalina tashi yakeyi sosai sai na bashi ATM ya ciro su za a zauna lafiya tsakanina dashi. Ga ido da yan gidan mu suka saka mi da yawan tambaya may nakeyi da kudina ne basu ga wani canji gurina ba ko a dakina da jikina. Duk da kowa ya san shine may karbe kudin yana min wayau don shikan wallahi yayi kiban shi bulbul dashi ga sutura kamar zai kashe shi na alfara da yake sakawa jikin shi sai kamshi idan yabar guri da zai bar mutane suna shaka. Na koma bagidajiyan dole saboda aure zaka rantse ban taba shiga boko nasan duniya ba idan ka ganni a cikin hakan na samu ciki na biyu a gidan shi. Kanwata ta haihu bayan ta share shekara a dakin ta ba haihuwa anyi shagalin suna lafiya mijin ta yai mata sha tara na arziki duk da naji yan gidan mu suna fadin itama da kudin ta mijin ta yake mata abu sai dai yafi nawa. Don su ana gani a jikin su da dakin su komai nasu acan acan yake ba kamar mu da muke a tauye ba nida yar diyata a gidan mijina. Rufin asirina guda shine aikin da baba ya samo min wanda bai hana inga laifin baba din a idona ba duk wanan abinda yake min duk da shima yana da nasa diyan da ya haifa suna bukatan haka a gare shi kuma. Amma ya rike mu fam yayi watsi da duk abinda mutane ke fadi a gamay dashi ya yi watsi da maganan kowa kan mu ya rungumay mu tsakani da Allah. Sai dai zugin Jamil a kanshi yana aiki a kaina don duk wanan kokarin da yake muna sai jamil din yace wai bai da hali bai taimaka muna don bai bamu kudi . Ko yace wai sun haye muna kudin gadon mu sun barmu muna wahala sun saka muna ido don basu suka haife mu ba idan da badon yana gudu mutane su gane ya cinye muna kudi ba ba abinda zai sa ma ya kula damu. Ire iren wanan maganan da yakeyi tun bai tasiri a zuciyar mu har ya fara nan zamu taru a gidana da yan uwan haihuwana mu kulla mu warware a tsakanin mu. Gashi kamar kudin uban shi ko da mahaifin shi ne ya mutu iya abinda zai iya ke nan a kan kudin mu gashi ban taba jin yana ma mahaifa addu,a ba a gaba na koda na rana daya ne. Karamin mu ne da aka samu kudin nan anty tasa ya sai tabarmi da butoci ya baya a masallatai sadaka mukan ta bimu har ta gaji bamu sai komai mun bada sadaka ba. Ni ina ma naga kudin tunda banda ta cewa alan kudin sai yadda akayi dani dasu yanzun ko ancinye an koma jin haushina. Ni dai ga wautana burina shine a zauna lafiya a tsakani na dashi na dauka yi hakan shine zai kara sa muna yarda da kauna a tsakani mu dashi. Ashe van san ba duka maza ne suka san hakan ba a rayuwan su don ba zance ba za, a rasa wanda keda rikon amana ba sam.