Sashe 54
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gobe na Allah ne abinda muke jira tsawon shekaru sai gashi Allah ya nufa sun shigo gare mu nan hankali mutane ya dawo gare mu. Don suji yaya za ai rabon wanan kudin namu an kasa kudin gida uku muka fara samun kashin farko ranan jamil shi da kan shi ya shirya min yarinya don inyi sauri mu hadu a gidan baba kabiru inda aka bukaci muje har. Har kusa da gidan ya rakani yana fadin idan kinji ki maida hankali ki saurara da kyau don kada a samu matsala nace insha Allahu mukai sallama na yaju ya koma gida yana jiran dawowa na daga gidan mu din. Na samu su baba musa da baba yushau sun shigo garin inda na karasa ciki da sallama na ina gaida mutanen gidan namu da kwana. Aka ce ni ake jira in karasa ciki kafin yar uwata tazo an bude gurin da sallama tare da addua kamar yadda musulmai keyi idan sun hadu a gurin yin abu mai muhinmanci. Baba musa da yake babba ne ya fara magana yace to Alhamdullahi yau dai Allah ya nufa wanan kudin da aka dade ana jira sun fara shigowa gare mu. Sai dai zamu so muyi rabo kamar yadda addini ya umurta da ayi yadaiyi yan bayanan shi tare da fadin zasu cire kason umma mahaifiyar su a rabawa magadan ta kamar yadda addini yace. Nan kanina ya gyara zaman shi da kyau ya kuma dora da fadin zamu cirewa shi Alhaji kabiru kuma kudin shi daya sa na jigila tare da yin wahala kafin kudin nan su fito gare mu. Sai baba kabiru din yace ba zai karbi kudin duka ba tunda kudin namu bai gama shigowa ba lokacin tare da fadin zai kuma karbi iya wahalan shi rabine. Nan sukayi komai kamar yadda ya dace ayi kan tafarkin addinin musulunci aka fitarwa maza da kason su sai mu mata mu biyu . Ganin duk mun bata rai tunda baba musa ya fara magana yasa baba kabiru yin gyaran murya a gurin yace idan mun ga rabon da sukayi bai gamshe mu ba zasu iya kiran malamai ko alkalai suzo su raba muna da kansu idan haka zai gamsar damu din. Dakatar da rabon kudin baba musa yayi a lokacin da yaji abinda baba kabiru din ke fadi yace assha daga cikin mu nan wa zai cuce su suke gani idan mu masu hali ne ai ko kallon kudin nan da yake gadon mahaifiyar mu ne ba zamuyi ba. Nan dai muka dan fara kamay kamay alaman nuna haba dai baba aka raba kowa ya dunkule nasa muka fito idanuwan mu mirsisi nayi sallama da mutanen gidan mu muka bar gidan. Gaba dayan mu gidana muka hade dukkan mu nan kanina ya fara fada akan abinda su baba sukai mu nan dai kowan mu ya shiga fadan albarkacin bakin shi kan su baba din. Sai baffa ke fadin shi baba kabiru ne yafi bashi mamaki da wai ya karbi kudin da don yayi wahala ya nema muna hakkin ga gwaunati. Lokacin ko yana UG two ne baba ne mai daukan nauyin karatun shi a makarantar ga diyan shi a zaune bai kai su ba su amma duk wanan bamu gani ko kadan mu kudin mu dai muka sani mu. Sai Jamil da na samu yana dakon dawowa tun fitana yace yanzu kun fara gane mai nake fada maku din ke nan yanzu shi baiji kunyan fadin wai a bashi wanan kudin ba don Allah. Mun dai fadi magana a gurin duk wanda yazo muna a baki fadi mukeyi a lokacin don ran mu daya baci kan dan abinda iyayye mu suka dauka wanda iya hakkin su ne suka dauka. Nan mijin sumaiya yazo shima ya dan dora nasa zancen akarshe a ka yanke shawara Baffa kanina zai rubutawa baba takarda kan abinda sukai muna karshe su sumaiya suka dauki kudin su mukai sallama bayan mun cire wanda zamu rabawa dangin mu kaf daga cikin kudaden da kyat don kowa na fadin kudin sunyi yawa abinda nace a ware din abawa yan uwa da suka wahala damu. Daga cikin mu dan karamin mu ne kawai bai magana karshe ma da yaga irin shawaran da mazajen mu ke badawa yayi yawa ya mike tsam abinshi yace damu sai da safe. Nan na gano baya tare damu aiko muka haushi da fada shida bai ce damu komai ba ta fita abinshi yana fadin kudai bi sannu don kudi karewa zaiyi ya barmu da iyayyen mu daga haka ya fice abin shi ya barmu. Ina mamaki yanzu kwarai da kanwata tafini zakewa akan zancen kudin nan sosai sai daga baya na gane sherin mijin ta ne ya yi mata famfon shedan a zuciya itama ta kumbura fam da iyayyen namu. Tsakani da Jamil yanzu ko nan wani irin ladabi ya taso ga Jamil din gare ni sai nan nan yake yi dani da yar diyata na zama wata hajiya a guri shi da baya son ko kuda ya tabani a lokacin aka bude wani shafin sabon soyyaya sosai a tsakanin mu. Tun cikin dare muka fara kasafin kudin da abinda zamu saya da kudaden namu inda yasa na ware ma mahaifan shi nasu kason daga cikin kudin. Ni yar Dadi aure sai nace ya rike kudin a hannun shi gaba daya duk abinda za a yi sai ayi nan muka shiga facaka da kudi ba wanan, ba wancan, duk kuma yan uwan shi don ni nawa yan uwan ba wanda yazo kaman an tsayar dasu a lokacin daga zuwa gurina. Baka jin komai sai kamshin a shiyan mu na soyeye da dafe dafen kayan dani idan mun shige daki yana gida kowa yazo gurina ban fitowa sai dai mutum yayi sallama ya gaji ya tafi don bai bari in fito gurin mai shi. Ni da kaina naje gidan mu tare da kudin damu ka warewa yan uwan mu dubu sittin kacal da kyat da boni daga cikin kudaden namu. Banyi mamakin ganin canjin fuska ga kowa na gidan ba sai dai lokacin nima kaina na hayaki sai ban damu ba ashe da safe Jamil ya bayar da wanan takardan daya ce zai rubutawa baba kabir din. Shine sauyin fuskan dana gani a wurin yan gidan namu a lokacin jin sallama na yasa baba kabir fitowa ya kirani zuwa falon shi. Inda ya fara magana bayan kara gaisawan da mukayi yana fadin nasan da sanin ki jamil ya rubuto min takarda akan zancen kudin ku don haka na aika kowa yazo don kuji komai da kunnuwan ku. Ba a dauki lokaci ba naga su baba musa sun iso gidan kowa ranshi a bace damu yake lokacin sumaiya ma ta iso daga gidan mijin ta don unguwan su nada dan nisa da namu. Ran baba musa ya baci sosai nan sukai muna dala dala karshe suka nuna muna bacin ransu kan sun gane mazajen mu ne suka shiga cikin maganan kudin. Baba yusha,u yace yanzu kuko nauyi da kunyan wanan bawan Allah baku ji yadda kuka rufe ido kukai mai kan abin duniya shifa kudin gado sai wanda Allah ya nufa ya more zai more mai a duniya. Zaku iya rama mai irin dawai niyar da yayi dakune koma ince yakeyi dakune a duniya nan don dai mu kun san ba hali muke dashi ba da zamuyi maku. Cikin fushi baba kabiru yace in don kudin hakkina ne dana karba ya tashi ya mike ya dauko kudin yana fadin gasu na yafe ku kara da naku. Tunda kuna ganin na cuce ku ne na zallunce ku kuka na fara yi don nice babba kafin in magana kanin mu karami daddy ya mike yana fadin baba wallahi ni kan bada ni akai wanan shawaran ba ban ma san suyi wanan shawaran ba yana fadin haka ta mike ya fice daga fallon namu. Kuka nima nake ina nema gafaran baba kabir don hankalina ta tashi matuka yadda naga yana kuka akan mu sai abin ya daga min hankali sosai. Karshe dai muka bashi hakkuri muka fito rayu kan mu babu dadi kan rabon kudin inda kanina baffa da summaiya suka kyankyashe idanuwan su mirsisi basu kunyan kowa. Mun ba anty wani abu ba wani mai yawa bane don mun san ta wahala da rayuwan mu dubu ashirin muka bata baba ma haka sai uwar gidan ra goma da amaryan ta. Tace mu barshi ita kan ba zata karbi kudin mu ba gaskiya da kyat na samu na bar mata kudin a dakin ta na fito na tafi inda yaran baba kabir kaf suke muna kallon banza don mun taba masu mahaifin su. Sai gashi bayan sati biyu banda ko sisi a hannu na dama wurin shi koda na lalabo sai cewa yayi ai kudi sun kare babu komai a hannun shi kuma. Raina yayi matukar baci sosai da jin hakan ba yadda zanyi dole na kyale shi don banda yadda zanyi dashi kan hakan . Sai lokacin angulu ta fara komawa gidan ta na tsamiya kuma ya fara tayar da halin shi shikan ya samu ya yi dinkuna na alfarma daga cikin kudaden sosai ya sayi duk wani abinda yake da gurin saye din kafin kudin su shigo a hannun mu. Dan haka baida sauran takaici kuma yanzu nikan ko kyale da yar diyata bamu samu ba daga cikin kudaden na dai samu na sai wa kaina ledan daki da dutsen guga da wani tsohon tv na hannun don nagaji da shiga dakin yan hayan gidan mu kallo. Don Anty tasha min fada tana nuna min illar yin hakan da nakeyi na zuwa dakin yan gidan mu kallo wanda a lokacin ban daukan hakan a komai gare ni. Amma da take nuna min illar yin hakan sai naji abin ya fita mun a raina ko sunce an samo sabon kaset ban zuwa ko ina kallon ina dakina zaune. Shiyasa na matsa na sai wanan dan tv na hannu wanda ma bai kai nawa dana zo dashi gidan ba wanda baba kabiru suka saya min a lokacin aure na. Kowa taji zancen kudina sun kare sai yayi mamaki sosai don abin akwai mamaki gaskiya don ba a gani a dakina ba da jikina