Sashe 40
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read
rana zai tashi daga barcin jiya da muka kwanta yayi wanka ya shirya ba maganan yin sallah. Idan nayi mai magana sai ya hauni da fada yana fadin kin san ni bansan Allah ba sai kin koya min may zaki nuna min akan addini kin dai san na fiki sanin hakan. Ni da na tashi a gida cikin hausawa yan uwana kuma musulmai na san Al,Qurani nasan hadisi don haka bake zaki nuna min yin sallah ba inda yake shiga ba nan yake fita ba. Ni dai na samu gefen gado nayi tagumi ina kallon shi sai ruwan bala,i yake min kan kawai nace dashi ya tashi rana nayi yayi sallah. Har ta gaji ya mike ya dauki buta ya kurkure bakin sa ya dawo yana tambayana idan na gama abin karyawa in kawo mashi fita zaiyi. Na mike jiki ba karfi na fita na dauko mai kayar karyawan shi da na aje mai ya zauna sai da yayi kat ya fice daga gidan. Mikewa nayi na kwashe kaya raina ba dadi ina tunanen maganan umma a karo na farko a raina ashe abinda take hango min ke nan wanda na kaaa hangowa kaina shi. Tun ba,a je ko ina ba zaman ya fara ban tsoro da Jamil don babu wani dadin auren da zance naji wanda amare suke ji idan anyi aure a farkon aure. Ga tsoro shi da yake kokarin cusawa a zuciyana dan abu kadan zanyi yanzu ya hauni da fada na fitan arziki yana zagi iya son ranshi ni dai babu zancen wani amarci a gurina sam. Iyayyen shi kuma da muke zama dasu da akace wai zasu zauna ne don barin iya mu yara a gidan baiyi ba shine suka ga dacewan zaman mu tare dasu din. Ni dai banga wani amfanin su ba a gidan asalima kamar tsoron dan nasu suma suke ji don har su yakewa wanan tsare gidan nashi da yake min sai dan jefi jefi zakaji yana hira da mahaifin nasa. Ko idan yana min fada mahaifin nasa ya karbe ya goyi bayan dan nasa kirikiri yana fadin nice banda gaskiya banda mutunci. Sai dai idan sunga yana cikin dadin rai da nine nake samun sakewa dasu a gidan har zamu dan zauna muyi hira da matan amaryan baban nasa da muke zaune a tare. Duk wanan baya damu na nidai buri na inga munyi zaman lafiya a tsakanin mu dashi kamar na sauran ma,aurata don sam banda wani walwala balle har in dan fara cikan daki da akeyi idan anyi aure. Ranan da yan gidan mu suka zo gani na na rasa yadda zanyi akan rashin kayan dakin da babu dakina wanda akai min daga gida da Jamil ya sayar din. Suna shiga dakin maganan farko da sukai min shine anty hadiza ina kayan dakin ki nace ku zauna mana in fada maku komai a tsanake. Zama sukayi suna saurarona don jin abinda zance din bayan sun zauna ne muka gaisa nake fada masu sai da aka jera min kayan naga basu min kyau ba na bayar a hurhura min ne za a kawo min wani sati in Allah ya yarda. Badon sun yarda da magana ta ba don yarda naga suna min wani irin kallon na tuhuma a ransu sai da mukai hirane zasu tafi nake rokon su akan don Allah su rufa min asiri kada su fada a gida sai idan an kawo min kayan zanje in fada a gida. Sukai min alkawarin ba zasu fadi ba kuma hakan ne don naji shiru ya tabbatar min da basu fadi din ba a gida don banga kowa yazo min da maganan ba. Jin shirun yayi yawa ne kan kayan yasa ranan na tambaye shi labarin kayan fada ya fara yi abinda yasan ban so ke nan fada yana fadin idan ta ban ai zan kawo maki tunda kin nuna min banda iko a kan abinki yanzu. Da har zaki bude baki kina tambayana kayan ki kamar wanda baki yarda dashi ba ya fice yana fada kamar yadda ya saba yi idan zaiyi yaudaran nasa a gurina. Tun ranan da nai maganan kayan ya shiga fushi dani sai ya shigo fuska a murtuke yayi abinda zaiyi a dakin ya fice daga gidan idan ya gama. Da abin ya ishe gani ban iya gaba ba a rayuwana ranan dai na kudirta a raina zan mashi magana idan yashigo gidan don mu fahinci juna dashi. Dama ni tsoro na kada yan gidan mu su sanda wanan zancen a dauki mataki a kaina shine kawai damuwa na a lokacin. Can cikin dare ina barci ya shigo dakin ina jin motsin shi na bude idanuwa ina kallon shi filo ya dauka ba tare da yai min magana ba zai nufi falo dashi da sauran abinda yake bukata a dakin. Sannu da dawowa nayi mai bai amsa min ba sai kokarin fita yakeyi a dakin zuwa falo na mike na bishi falon yana kokarin kwanci a saman dogon kujera don kujera kawai ya bar min a dakin sai ledan kasa a lokacin. Zama nayi a dayan kujeran dake kusa dashi ina fadin haba my may ya faru da zafi haka kake fushi dani kan dan magana kankani. Ya juyo a fusace yana fadin oh baki ma san abinda kikai min ba ke nan har kina daukan maganan dan kankani a gurin ki ko ? Nace ni banga abindana fada mai zafi ba daga tambayan kaya sai ka hau fushi dani haka kawai yace eh tunda kin nuna min kayan ki kayan ki ne ni banda iko dasu ke nan. Na marairaice murya ina fadin ni ba haka nake nufi ba my ka sani wanan ba halina bane amma idan maganan ya bata maka rai kayi hakkuri don Allah. Sai hawaye ya zubo min wanda ban san ko na may ye ba a lokacin ya dago kai yana kallona tare da fadin mayye kuma na kuka yanzu daga magana. Nace naga maganan ya bata maka rai ne sosai don kawai na tambayi ba,asin kayan dakina daka kwashe da sunan hurhura min su. Yace baki yarda ba dani ke nan kika kasa hakkuri har kiga iya guduna a kan kayan na kara marairaicewa nace ni dama tsoro nake ji azo daga gida a samu babu kayan a dakin nan. Yace idan sun zo sunyi magana ki fada masu abinda na fada maki a baya, ina kin gane yanzu na gyada mai kai a hankali wanan ne yasa muka shirya ya bar fushin da yake yi din dani da farko.